THE PSALMS IN HAUSA


Zabura ta 1

Albarka ga wanda bai shiga * shawarar miyagu ba,

    bai tsaya a taron masu zunubi ba, * bai kuma zauna a gun masu yin baa ba.

Sai dai yana jin daɗin karanta shariar Yahweh, * yana ta nazarinta dare da rana.


    Yana kama da itacen * da ke a gefen ƙorama,

    yakan ba da yaya a kan kari, * ganyayensa ba sa yin yaushi, * yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

Miyagu ba haka suke ba, * su kamar yayi suke * wanda iska take kwashewa.

    Mai sama kuwa ba zai tallafa ba * miyagu a wurin hukunci * ko kuwa masu zunubi wurin adilai.

Sai dai Yahweh yana lura da taron adalai, * amma taron miyagu zai hallaka.

Zabura ta 2

Don me alummai suke tayarwa, * suna ƙirga mayaƙansu?

    Don me sarakunan duniya suke yin tawaye, * masu mulkinsu suna gama kai

         na gāba da Yahweh, * da shafaffen sarkinsa?

    Suna cewa Bari mu kwance igiyarsu, * mu fice daga ƙarƙashinsu.

         Shi wanda ke zaune a sama yana dariya, * yana mai da su abin dariya.

         Sannan yana korar manyansu da hushinsa, * da hasalarsa kuma yana razana su.

              Ni ma an naɗa ni sarkinsa * a bisa Sihiyona, dutsensa tsattarka.

                   Bari in yi shelar umurnin * Ubangiji Yahweh, * ya ce da ni:

              Kai ɗana ne, * a yau ne na haife ka.

         Ka roƙe ni, zan ba ka * alummai ka gada, * har bangon duniya za ka mallaka.

         Za ka yi kiwonsu da sandan ƙarfe, * ka farfashe su kamar tukunyar magini.

    Yanzu, ku sarakuna, ku yi hankali, * ku gargaɗu, ku mahukunta!

         Ku bauta wa Yahweh da tsoro, * ku yi rawar jiki, ku da aka ƙaddarawa zuwa kabari,

    don kada ya yi hushi, taronku kuwa ya hallaka, * gama yakan yi hushi da sauri.

Albarka ga duk * masu neman mafaka a wurinsa.

Zabura ta 3

Yahweh, magabtana sun ƙaru ƙwarai! * Da yawa ne masu tasam mani!

    Barkatai ne su ke hararrata, suna cewa: * Ai ba wani taimakon da Allah zai yi masa.

    Amma kai, Yahweh, maigidana ne iyakar raina, * Maɗaukakina ne kuma, mai tallafata.

         In na kai kukana gaban Yahweh, * yakan amsa mani daga tsattsarkan dutsensa.

              In na kwanta in yi barci, * nakan farka, domin Yahweh yana kiyaye ni.

         Ya Ƙaƙƙarfa, bana jin tsoron kiban magabtana, * da ke kewaye ta kowane gefe, ya Mai Sama.

    Ka yinƙuro mana, Yahweh, * ka kuɓutad da ni, ya Allahna!

    Kai da kanka * ka bugi bakin magabtana, * ka kakkarya haƙoran miyagu.

Ya Yahweh, kai mai nasara ne! * Albarkarka ga jamaarka.

Zabura ta 4

Da na yi kira, ka amsa mani, * ya Allah mai nasarata.

Daga matsatsi ka buɗe mani hanya, * ka ji tausayina, ka saurari adduata.

    Ya ku yan adan, yaushe ne * za ku dena zagin Maɗaukaki?

        kun bauta ma abubuwan banza, * kuna shawara da allolin ƙarya?

    Amma dai ku san cewa * Yahweh zai yi abubuwan mamaki don bawansa, * Yahweh zai saurara saad da na kira shi.

        Ku ji tsoro, kada ku ɗau zunubi, * ku binciki zukatanku, * ku kwanta, ku yi kuka.

        Ku yanka dabbobin da suka hallata hadaya, * ku kuma dogara ga Yahweh.

    Mutane da yawa suke cewa, * Wa zai kawo mana ruwan sama?

        Hasken fuskarka * ya guje mana, Yahweh!

    Sai dai ka sanya farinciki a cikin zuciyata, * yanzu sai hatsinsu da abinshan inabinsu su ƙaru.

Da kwanciyar rai a gaban fuskarsa * zan kwanta in yi barci,

domin kai kaɗai ne, Yahweh, * kake zaunad da ni a cikin aminci.

Zabura ta 5

Ka kasa kunne ga kalmomina, Yahweh, * ka ji maganata.

    Ka saurari sautin kukana, * ya Sarkina, Allahna, * domin gare ka nake addua.

    Da sassafe ka ji muryata, * da sassafe nake yin ƙara, * in kuma yi dakonka.

         Allolin banza ne ke jin daɗin mugunta, * mugun mutun ma ba zai zo gunka ba.

         Masu fariya * kada su tsaya a gaban idanunka.

              Na ƙi dukkan masu mummunan aiki, * sai ka hallaka maƙaryata.

              Mai gunki da mai tsafi, * duk Yahweh yana ƙinsu.

                   Amma ni, da yalwar ƙaunarka, * zan shiga gidanka.

                       Zan yi sujada zuwa ga tsattsarkan Haikalinka * tare da masu tsoronka.

                   Ka yi mani jagora zuwa aljanna, * nesa daga magabtana; * ka sa hanyarka ta yi mani saukin bi.

              Ba abin da za a gaskanta daga bakinsu, * cikinsu kududdufi ne da ba zai cika ba.

              Maƙogwaronsu na haɗiya kamar buɗaɗɗen kabari, * suna kisa da halshensu.

         Ka hallaka su, ya Allah, * bari shirye-shiryensu su tadiye su.

         Saboda ɗumbun laifuffukansu * ka jefad da su * domin sun yi maka tawaye.

    Duk waɗanda suka fake gare ka su yi farinciki, * kullun su yi ta raira waƙar murna.

    Kakan kiyaye masu ƙaunar sunanka,* domin su yi matuƙar murna da kai.

Gama kana yi wa mai gaskiya albarka, * Yahweh, * kamar garkuwa, soyayyarka ke kewaye shi.

Zabura ta 6

Yahweh, kada ka tsawata mani da hushinka, * kada kuma ka hore ni da zafin ranka.

    Ka ji tausayina, Yahweh, * domin na bushe.

    Ka warkad da ni, Yahweh, * domin ƙasusuwana sun rafke.

         Raina ya wahala ƙwarai, * amma kai, Yahweh, yaushe za ka dube ni?

         Ka dawo, Yahweh, ka kuɓutad da raina, * ka cece ni yadda ya dace da ƙaunarka.

              Gama ba mai tunawa da kai a Mulkin Mutuwa. * Can a Lahira ma wa zai yi yabonka?

              Na gaji da kuka, * kowane dare sai na jiƙa gadona, * ina cika tabarmana da hawaye.

         Idanuna sun dishe da baƙinciki, * zuciyata ta karaya saboda baƙinciki.

    Ku rabu da ni, masu mugun aiki, * domin Yahweh ya ji sautin kukana.

    Yahweh yā ji roƙona, * Yahweh ya karɓi adduata.

Su kunyata, su ɗauki rawar jiki * dukan magabtana * su juya, su ji kunya a Mahallaka.

Zabura ta 7

Yahweh, Allahna, gare ka nake dogara, * ka cece ni daga dukan masu korata.

Ka kuɓutad da ni, kada wannan ya kacancana ni * kamar zaki * yana ƙarya wuyana, ba kuma mai ceto.

    Yahweh, Allahna, in na yi cin mutunci, * in hannuna na da laifi,

    in na ci amanar abokina, * ko na dame shi da tsegumi,

         to, magabcina ya bi ni, ya kama ni, * ya tattake kayan cikina a ƙasa, * ya jefad da antata a caɓi.

         Ka tashi, Yahweh, da hushinka, * ka tsai da wulakancin magabtana.

         Ka falka, ya Allahna, * ka umurci

              Ka tattaro dukan kabilan kewaye da kai, * ka shugabance su, ya Maɗ aukaki, * Yahweh, ka yi wa dukan mutane sharia.

              Ka hukunta ni gwargwadon aikina na gaskiya * da kirkina, ya Maɗaukaki.

                   Ka rama taaddancin yan taadda, * ka kuma kāre mai gaskiya.

                   Mai binciken zukata da hankula, * shi ne Allah mai gaskiya.

              Maigidana Allah Maɗakukaki ne, * yakan ceci masu zuciya tagari.

              Allah alkali ne mai gaskiya, * yana tsai da zalunci a kullun.

         Bari Mai Nasara ya sake * wasa takobinsa, * ya ɗana bakansa cikin shiri.

         Bari ya shirya makamansa masu kisa,* ya kunna kibansa masu wuta.

    Mugu yakan ɗauki cuta, * yakan yi ciki da fitina, * yakan haifi ruɗu.

    Ramin da ya haƙa ya tadiye shi, * ya faɗa ramin da ya tona.

    Muguntarsa ta koma kansa, * rikicinsa ya sauka ƙoƙwan kansa.

Na gode wa Yahweh yadda ya kamata, * ina waƙar yabon Yahweh Maɗaukaki.

Zabura ta 8

Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ɗaukaka ne * a dukan duniya.

    Zan yi wa martabarka sujada, * wadda take bisa sama, * da bakin jarirai masu shan mama.

    Ka gina mafaka don gidanka, * bayan ka bebanta magabtanka * da maƙiyanka da masu ramuwa.

         Saad da na dubi sammai, * aikin yatsunka,

         da wata da taurari * waɗanda ka halitta:

             Menene mutun, har da za ka tuna da shi, * ko ɗan adan, har da za ka kula da shi?

         Duk da haka, ka yi shi ya gaza alloli kaɗan, * da daraja da girma ka naɗa shi.

         Ka mai da shi sarkin ayyukan hannuwanka, * ka sanya kome a ƙalƙashin sawayensa:

    tumaki tare da shanu, * har da namomin jeji,

    da tsuntsaye da kifayen teku, * masu yawo a hanyoyin ruwan tekuna.

Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ɗaukaka ne * a dukan duniya.

Zabura ta 9-10

Zan yabe ka, Yahweh, da dukan zuciyata, * zan bayyana dukan ayyukanka masu banmamaki.

Zan yi murna, in yi farinciki da kai, * zan raira waƙar da sunanka, Maɗaukaki.

    Saad da magabtana suke ja da baya, * suna tuntuɓe, su hallaka saboda hushinka.

    Ka yi naam da hakkina da shaanina, * ka zauna a kan gadon sarauta, ya Alkalin gaskiya.

         Ka tsawata wa alummai, ka hallaka miyagu, * ka shafe sunansu har abada abadin.

         Magabtana su isa ƙarshensu, * su zama kufai har abada.

         Ka tuge allolinsu masu tsare su, * a dena tunawa da su.

    Ga shi, tun filazal Yahweh ya yi mulki, * ya kafa kursiyinsa don yin sharia.

    Shi ne yake mulkin duniya da gaskiya, * yana yi wa mutane sharia da adalci.

         Yahweh mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, * matsera kuma a lokacin ƙunci.

         Bari waɗanda suke son sunanka su amince da kai, * domin ba ka ƙyale masu nemanka, Yahweh.

              Ku yi waƙoƙin yabon Yahweh, Sarkin Sihiyona, * ku gaya wa alummai aiyyukansa.

              Gama yakan lura da masu kuka, * yakan tuna da nishinsu, * baya mantawa da ƙarar masu shan wuya.

                  Ka ji tausayina, Yahweh, * ka ga wahalata.

                  Ka janye ni daga Maƙiyina, * da ƙofofin Mutuwa,

                  don in bayyana yabonka sosai * daga ƙofofin Ya Sihiyona,

                  in yi farinciki * da nasararka.

              Bari alummai su dulmuya cikin ramin da suka yi, * da tarkon da suka ɗana ya kama ƙafafunsu.

              Bari Yahweh ya sanu ta hukuncin da yake zartaswa, * amma bari a kama mugu ta aikin hannuwansa.

          Miyagu su koma Shawol, * su hallaka, su alumman da suka manta da Allah.

          Gama ba kullun ne za a manta da mabukata ba, * sazuciyar zaluntattu ma ba za ta dannu ba har abada.

          Ka tashi, Yahweh, kada mutane su yi kirari, * a yi wa alummai sharia a gabanka.

          Yahweh, ka danne bakinsu, * ka sa alummai su san su mutane ne kawai.

10           Yahweh, don me kake tsaye can nesa, * kana ɓoyewa a lokacin wahala?

              Cikin mugu yana dafa wulakanci, * da aniya yake aikata dabarun da ya ƙuƙƙulla.

              Mugu yana fahariya da marmarinsa, * mai ƙwacewa ma yana bauta wa kwaɗayinsa.

                   Mugu yakan rena Yahweh, cewa: * Mai Sama ba zai aikata hushinsa ba.

                   Allah ba zai jirkita dabarunsa ba, * wadatata za ta jure har abada.

                   Maɗaukaki, hukuntanka suna nesa da shi, * daga birnin zuciyarsa yana firjinsu da baa.

                   Yana cewa da kansa, Ba zan yi tuntuɓe ba, * ina da madauwamin farinciki ba wahala.

              Bakinsa cike yake da zagi, zamba da zalunci, * halshensa yana riƙon wulakanci da mugunta.

              Yakan yi kwanton ɓauna a ƙauyuka, * a maɓoya yakan kashe marasa aibu, * idanunsa na hararar kāsasse.

          Yakan yi sanɗa kamar zaki a kogonnsa, * yakan yi sanɗa don ya kama gajiyayye, * yakan kama shi, ya tafi da shi.

          A tarkonsa zaluntacce ke fāɗuwa, * marasa katari kuma na fāɗawa raminsa.

          Yana cewa da kansa, Allah ya mance, * ya rufe idonsa, * baya dubawa har abada.

    Ka tashi, Yahweh Allah, ka ɗaga hannunka, * kada ka manta da masu shan wahala.

    Har abada ne mugu zai rena Allah? * yana cewa da kansa, Ba zai yi hisabi ba.

         Ka dubi bakincikin da kanka, * ka dubi ɓacin ran, * gama hannunka ne ke bayas da su.

         A gare ka gajiyayyen maraya ke danƙa kansa, * ka zama mataimakinsa mana!

    Ka karya dantsen mugu, * ka biya shi da muguntarsa. * Ba ka ganin ƙetarsa?

    Yahweh madauwamin sarki ne, * bari alummai su hallaka daga ƙasarsa.

Yahweh, ka saurari kukan matalauta, * ka mai da hankali, ka kasa kunne.

In ka kāre maraya da zaluntacce, * masu girman kai ba za su riƙa razana mutane daga duniya ba.

Zabura ta 11

Na sami mafaka wurin Yahweh. * Don me kuke sanɗar raina? * kuna farautata kamar tsuntsu?

    Ga yadda miyagu suke jan baka, * suna ɗana kibansu,

    don su harbi * masu gaskiya a ɓuye.

         Lokacin da ake ture harsashen, * me Mai-Gaskiya yake yi?

              Yahweh yana da mazauni a Haikalin, * kursiyin Yahweh a sama yake.

                   Idanunsa suna kallo, * suna binciken * duk yan adan.

              Yahweh mai gaskiya * yana auna miyagu.

         Duk wanda yake son zalunci * yana ƙin ransa.

    Bari Yahweh ya zubo wa miyagu * garwashin wuta da kibiritu.

    Bari iska mai ƙuna * ta zama rabonsu.

Yahweh mai gaskiya ne * yana son ayyukan gaskiya. * Fuska da fuska zamu kalli Mai-Kirki.

Zabura ta 12

Ka yi taimako, Yahweh, * domin masu ibada sun ƙare.

Amintattun mutane sun kasa * a cikin yan adan.

    Kowa na zancen ƙarya, * da maƙwabcinsa.

    Da baki mai lahani * da zuciya biyu suke magana.

         Bari Yahweh ya yanka * duk baki mai lahani, * da duk halshe mai murɗa gaskiya,

         waɗanda suke fariya cewa, * Halshenmu shi ne ikonmu.

         Makamanmu leɓunanmu ne, * wa zai mallake mu?

         Saboda ajiyar zucin gajiyayyu * da nishin masu bukata,

         yanzu zan tashi, * in ji Yahweh.

         Zan ba da taimako * ga wanda ya ke bukatarsa.

    Alkawalan Yahweh * alkawalai ne masu gaskiya,

    azurfa ne da aka tace a matoya, * aka tsabtace ta daga laka sau bakwai.

Yahweh, kai kā tsare mu, * kā kiyaye mu tun filazal, ya Madauwami.

Koina miyagu suna rangadi, * suna tona ramuka don yan adan.

Zabura ta 13

Har zuwa yaushe za ka mance da ni, Yahweh? Har abada? * Har zuwa yaushe za ka kau da fuskarka daga wajena?

Har zuwa yaushe zan yi shakka a raina, * ina baƙinciki a raina? * Har zuwa yaushe maƙiyina zai yi mani dariya?

    Ka dube ni, ka amsa mani, * Yahweh Allahna.

         Ka buɗe mani idona, * ka kau da barcin mutuwa daga wajena.

    Kada magabcina ya ce, * Na rinjaye shi, * kada maƙiyina ya yi farinciki saboda faɗuwata.

Amma ina dogara ga rahamarka, * bari zuciyata ta yi murna don ka cece ni.

Zan raira waƙa ga Yahweh, * gama Maɗaukaki ya kyautata mani.

Zabura ta 14

A tunanin wawayesuna cewa, * Allah baya nan.

Su ɓatattu ne, suna aikata alamuran ƙyama, * ba wani mai yin abu mai kyau.

    Daga sama Yahweh yana dubo * yan adan duka,

    don ya ga ko akwai masu fahimi, * masu neman Allah.

         Amma dukansu masu taurin kai ne, * sun ƙazanta gaba ɗaya.

         Ba mai yin kyakkyawan aiki, * babu ko ɗaya.

         Masu aikin mugunta ba su sani ba * cewa masu washe jamaarsa

         suna satar hatsin Yahweh, * da ba su yi noma ba?

    Ga yadda suka yi ƙungiya, * amma Allah ne a cikin jamaar adilai.

    Majalisar gajiyayyu ta kunyata miyagu, * gama Yahweh shi ne mafakarsu.

Daga Sihiyona sai ceton Israila ya fito! * Saad da Yahweh ya sake arzuta jamaarsa,

bari yayan Yakubu su yi farinciki, * yayan Israila su yi murna.

Zabura ta 15

Yahweh, wa zai iya baƙunci a alfarwarka? * Wa zai iya zama a kan tsarttsarkan dutsenka?

    Sai wanda ke bin hanya mara aibu, * yana aikata gaskiya, * yana faɗar kaskiya daga zuciyarsa,

         Wanda baya kusƙure da halshensa, * baya cutar makwabcinsa, * baya baza jita-jita a kan abokansa.

              Yakan rena mai laifi, * amma yakan shirya liyafa don masu tsoron Yahweh.

         Ya rantse ba zai yi mugunta ba, * ba kuma zai canza ba.

    Baya bayas da rance da ruwa, * baya ma karɓar toshi daga mayunwata.

Wanda yake yin waɗannan abubuwa * ba zai gaza ba.

Zabura ta 16

Ka kiyaye ni, ya Allah, * gama a gunka nike neman mafaka.

Na ce: Yahweh, kai ne Ubangijina, * kai ne Nagartata, * ba wanda ya fi ka a sama.

    Game da tsarkakan iskokin gargajiya, * jarruman da na ji daɗinsu dā,

         baru nakuɗarsu ta ƙaru, * su daɗe cikin tsanani.

    Hannuwana ba zasu zuba masu hadaya ba, * bakina ma ba zai ambaci sunayensu ba.

         Yahweh, kā ba ni rabona na abin sha mai daɗi, * kā yi kuriar ƙasata.

         An auna mani kyakkyawar ƙasa, * Maɗaukaki ya zaɓi ganduna.

    Zan yabi Yahweh mai ba ni shawara, * da dare yana gargaɗina a zuci.

         Na zaɓi Yahweh shugabana har abada, * daga hannun damansa ba zan girgiza ba.

    Don haka zuciyata ke farinciki, antata ma ke murna, * jikina na zaune a cikin aminci.

Gama ba za ka sa ni a Mahallaka ba, * ba za ka bar mai bauta maka ya ga Ramin ba.

Za ka nuna mani hanyar rai, * kana cika ni da farinciki a gabanka, * da murna a hannun damanka har abada.

Zabura ta 17

Yahweh, ka ji roƙona don hakkina, * ka saurari kukana.

    Ka kasa kunne ga adduata, * ka hallakad da bakunan yauɗara.

    Bari adalcina ya yi haske a gabanka, * idanunka su dubi gaskiyata.

         Ka gwada zuciyata, * ka bincike ni da dare, * ka jarrabce ni da wuta:

         Ba za ka sami tsafi a wurina ba, * ban yi batanci game da aikin hannuwanka ba.

         Ga kalmomin bakinka * na riƙe amana.

         Ƙafafuna sun bi ta hanya mai wuya * ba su ratse daga hanyoyinka ba.

    Ina kiranka, * ka amsa mani, ya Allah.

    Ka kasa kunne gare ni, * ka ji maganata.

         Ka yi karo da masu saɓonka, ya Maceci, * rufe bakunan magabtanka.

              Ka adana ni kamar ƙwayar ido, * ka ɓoye ni a inuwar fukafukanka

         daga mugun da ke son yayyaga ni * daga magabtana da ke kewaye da ni.

    Sun naɗi gara, * suna magana da izgilanci sosai.

    Ƙafafuna suna kyarma, * da suka kewaye ni.

         Sun sa ido su fyaɗa ni * Ƙasar Hallaka,

         kamar zaki mai haɗamar kisan abincinsa, * kamar kuyakuyan zaki masu ɓuya a wurin fako.

         Ka tashi, Yahweh, ka tsai da hushinsu, * ka kā da su, * ka cece ni daga miyagun da ke yaƙinka.

         Ka kashe su da hannunka, Yahweh, * ka hallaka su daga duniya, * ka shafe su daga masu rai.

    Amma darajantattun mutanenka, * ka cika cikinsu da gara.

    Yayansu su sami duk abin da suke so, * su bar wadatarsu ga jikokinsu.

A ranar sharia zan ga fuskarka. * a ranar tashin kiyama zan gamsu da zatinka.

Zabura ta 18

Ina ƙaunarka, Yahweh, ƙarfina. * Yahweh dutsena ne da matserata. * Allahna mafakata ne,

    Tuduna ne kuma wurin da ni ke gudu, * da garkuwata da makamin ceto, * hasumiyata mai cancantar yabo.

Na yi kira ga Yahweh, * ya cece ni daga magabtana.

    Raƙuman ruwan Mutuwa sun kewaye ni, * rafukan Hallaka sun gangara ta kaina.

    Igiyoyin Mahallaka sun ɗaure ni, * tarkunan Mutuwa sun fuskance ni.

A shan wahalata na yi kuka ga Yahweh, * ga Allahna na yi kira don taimako.

Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata, * kukana ya kai har kunnuwansa.

    Ƙarƙashin Ƙasa ya yi tangaɗi, * gindin duwatsu ma ya motsa, * ya yi makyarkyata da Yahweh ya fusata.

    Hayaƙi ya fito daga hancinsa, * wutar gobara daga bakinsa, * har da garwashin wuta daga wajensa.

         Ya buɗe sama, ya sauko, * girgijen hadari alfarwarsa ya ke.

         Ya hau Kerub, ya tashi sama, * ya yi tafiya da fikafikai buɗe.

              Tantinsa ya duhunta, * alfarwarsa da gajimaren ruwa.

              Saboda haskensa gizagizai sun dāre a gabansa, * duk da kanƙara da harsunan wuta.

                   Yahweh ya yi tsawa daga sama, * Mafi ɗaukaka ya furta maganarsa.

                   Ya ƙera kibansa, ya warwatsa su, * ya yawaita walƙiyoyinsa, ya fatattake su.

              Ƙalƙashin teku ya bayyana, * harsasan duniya sun tonu,

              saboda tsautawarka, Yahweh, * saboda rurin hancinka.

         Ya miƙo hannu daga sama ya ɗauke ni, * ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.

         Ya kuɓutar da ni daga ƙaƙƙarfan Magabcina, * daga Maƙiyina da ya fi ni ƙarfi.

    Ya bi da ni ranar mutuwata, * Yahweh ya zama sandata.

    Ya fisshe ni daga Ƙasar Hallaka, * ya cece ni, domin ya ji daɗina.

         Yahweh ya biya ni saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba ya saka mani da alheri.

              Gama na kiyaye hanyoyin Yahweh, * ba ni da laifi, ya Allahna.

                   Gama dukan hukuncinsa na gabana, * ban kuwa yas da dokokinsa ba.

              Kullun ina da sahihanci a gare shi, * na yi laakari kada in yi masa laifi.

         Don haka ya saka mani saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba a gaban idanunsa.

              Ga mai aminci kai mai aminci ne, * ga mai sahihanci kai mai sahihanci ne.

              Ga mai gaskiya kai mai gaskiya ne, * amma ga mai wayo kai ne mafi wayo.

                   Ai, kai ne Mai iko duka, * kana ceton gajiyayyu, * amma kakan tanƙwaso masu alfarma.

                        Kana yi mani haske, * fitilata Yahweh ne, * Allahna yana haskaka dufuna.

                   Ta wurinka ina da gwanintar sere, * da ikon Allahna na iya tsallace duk wani shinge.

              Sarautar Allah kammalalliya ce, * ana tabbatad da umurninsa.

              Shi shugaba ne * na duk masu dogara gare shi.

         Gama wanene Allah in ba Yahweh ba? * Wanene kuma dutse in ban da Allahnmu?

              Shi Allah ne da ke yi mani ɗamara da ƙarƙo, * da kuma Mai Bayarwa wanda sarautarsa take cikakka.

              Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa, * ya sa in tsaya a kan tudunsa.

         Ya hori hannuwana don yaƙi, * ya saukar mani da baka mai banmamaki.

    Kā ba ni garkuwarka ta nasara, * da hannunka na dama kā riƙe ni, * da hoɓɓasanka na zama mai girma.

    Kā ba ni dogayen ƙafafuna masu sauri, * idanun ƙafata ma ba su goce ba.

         Na bi magabtana har na kama su, * ban juya baya ba sai da aka gama da su.

         Na kā da su, ba su iya tashi ba, * sun fāɗi a ƙafafuna.

         Kā yi mani ɗamara da ƙarfi don yaƙi, * kā kā da masu yaƙi da ni a ƙarƙashina.

         Kā ba ni wuyan magabtana, * na hallaka maƙiyana.

    Sun yi kuka, amma Macecin baya nan, * sun kira Yahweh Maɗaukaki, * amma bai amsa masu ba.

    Na marmashe su sun zama kamar ƙurar titi, * kamar taɓon kwararo na tattake su.

Kā kuɓutad da ni daga kiban mutane, * kā tsare ni daga dafin sauran alummai.

Baƙuwar alumma za ta zama baiwata, * da sun ji ni, nan da nan sai su yi mani biyayya, * baƙi sai sun sunkuya don tsoro.

Baƙi sukan yi rawar jiki, * zukatansu sukan karaya.

    Ran Yahweh ya daɗe! * Dutsena a yabe shi! * Ɗaukaka ga Allah mai ba ni nasara!

    Shi Allah ne wanda ya ba ni nasara, * ya sarayar da alummai gare ni.

    Ya kuɓutad da ni daga Magabcina, * ya ɗaukaka ni a kan masu yin yaƙi da ni, * ya cece ni daga masu cin mutuncina.

Ya Maɗaukakin Zati, zan yabe ka a cikin al-ummai, * Yahweh, in kuma yi waƙar yabon sunanka.

Ya mai da sarkinsa sananne don cin nasara da ya yi, * ya nuna ƙauna ga shafaffen sarkinsa, * ga Dauda da irinsa har abada.

Zabura ta 19

Sammai suna shaida ɗaukakar Allah, * aikin hannuwansa ma, sararin sama ke bayyana shi.

    Kowace rana tana furta magana ga rana ta biye, * kowane dare yana sanad da dare na biye.

    Ba wata magana, ba wasu kalmomi, * ba a jin muryarsu.

A duniya duka kiransu ke bazuwa, * maganarsu kuwa har zuwa bangon duniya.

    Ya kafa wa rana alfarwa, * kamar ango tana taƙama daga maɓoyarta.

        Tana murna kamar mayaƙi, * don ta ruga a kan hanyarta.

    Takan fara daga farkon sama, * ta koma gare shi, * ba ta kuskuren ɗakinta.

Shariar Yahweh kammalalliya ce, * tana sanyaya zuciyata.

Shariar Yahweh tabbatacciya ce, * tana sa hikima a tunanina.

    Kaidodin Yahweh madaidaita ne, * suna faranta zuciyata.

    Umurnin Yahweh mai haske ne, * yana haskaka idanuna.

        Dokar Yahweh mai tsabta ce, * tana jurewa har abada.

        Hukuntan Yahweh gaskiya ne, * dukansu daidai ne.

          Su aka fi so a kan zinariya, * komi yawanta.

          Sun fi zuma zaƙi, * i, fiye da saƙa cike da ruwan zuma.

     Suna haskaka ni bawanka, * wajen kiyaye su da lada mai girma.

     Wa zai iya gano kurakurai? * Ka hana ni bauɗewa.

Ka kuma kare ni daga allolin ƙarya, * kada su mallake ni.

A saan nan ne zan zama kamili, * in kuma kuɓuta daga babban zunubi.

     Sai bakina ya furta abin da ya gamshe ka, * zuciyata ma ta bi nufinka, * Yahweh, Dutsena da Mai Fansata!

Zabura ta 20

Yahweh ya ba ka nasara a ranar wahala! * Sunan Allah na Yakubu ya zama garunka.

    Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa, * ya kawo maka gudunmuwa daga Sihiyona.

         Ya tuna da dukan baye-bayenka, * ya yi naam da hadayunka na ƙonawa.

    Ya biya bukatar zuciyarka, * ya cika dukan shirye-shiryenka.

         Sannan za mu yi sowa ta farinciki saboda ka ci nasara, * da sunan Allahnmu kuma za mu kaɗa tutoci. * Bari Yahweh ya cika dukan roƙe-roƙenka!

              Yanzu dai na sani * Yahweh yakan ba shafaffen sarkinsa nasara.

         Yakan ba shi nasara daga tsattsarkar samaniyarsa, * a mafakarsa yakan ba da nasara da hannunsa na dama.

    Waɗansu suna da karusai, * waɗansu suna da dawaki,

         amma mu da sunan Yahweh * Allahnmu ne muke da ƙarfi.

    Suna sunkuyawa, suna faɗi, * amma mu, muna tashi tsaye kyam.

Yahweh yā ba sarkin nasara, * yā ba shi nasara da muka roƙa.

Zabura ta 21

Yahweh, da nasararka sarki yake murna, * da agajinka yake farinciki.

    Kā biya masa burin zuciyarsa, * ba ka ƙyale roƙon da ya yi ba.

    Kā zo gare shi da albarka mai kyau, * kā sanya kambin zinariya a kansa.

         Ya roƙe ka madauwamin rai, ka kuma ba shi, * kwanaki ba iyaka, har abada abadin.

         Martabarsa babba ce don nasarar da ka ba shi, * kā sa ya yi suna da kwarjini.

              Albarkarka tana a kansa har abada, * za ka faranta masa rai da ganin fuskarka.

              Sarkin yana dogara ga Yahweh, * ba kuma zai kawu daga ƙaunar Madaukaki ba.

              Hannunka na hagu ya kama dukan magabtanka, * hannunka na dama ya kama maƙiyanka.

              Yahweh, kā sa su a cikin tanderu mai wuta * a lokacin hushinka.

         Da hushinsa yā cinye su da wuta, * ya haɗiye su.

         Kā hallaka yayansu daga duniya, * da zuriyarsu daga cikin yan adan.

    Gama sun shirya tayarwa game da kai, * sun ƙulla mugunyar dabara, * amma ba su iya yinta ba.

    Kā sa su durkusa, * inda kake ɗana masu bakanka.

Yahweh, ka yi bikin nasararka! * Za mu raira waƙa ta yabon ikonka.

Zabura ta 22

Ya Allahna, ya Allahna, * don me ka yashe ni?

kana korar roƙona, * da sautin kururuwata.

    Ya Allahna, ina kira da rana, * amma ba ka amsa ba,

         da dare kuma, * ban sami taaziya ba.

    Amma kana zaune a kan tsattsarkan gado, * Ɗaukakar Israila.

Gare ka ne kakanninmu suka dogara, * sun dogara, kai ma ka kuɓutad da su.

Gare ka ne suka yi kira, sun kuwa kuɓuta, * gare ka ne suka yi kira, ba su kuwa kunyata ba.

    Amma ni tsutsa ne, ba mutun ba, * mafi renanne wurin mutane, * abin baa ga kowa.

         Duk waɗanda ke ganina suna maishe ni abin dariya, * suna tsaki, suna kaɗa kai, suna cewa:

              Ya bi Yahweh, bari ya kuɓutad da shi; * sai ya cece shi in ya so shi.

              Amma kai ne ka fito da ni daga mahaifa, * ka kwantad da raina a maman mahaifiyata.

         Kai ne ka ciyad da ni daga haifuwata, * tun ina cikin uwata kai Allahna ne.

    Kada ka yi nesa da ni, * gama masu tsananta sun yi kusa, * ba ma wani mataimaki.

         Bajimai masu yawa suna kewaye ni, * ƙarfafan bajimai daga Bashan suna sa ni tsaka.

         Suna buɗe mani bakinsu, * kamar zakoki masu kāwa masu hauka.

              An zub da ni kamar ruwa, * ƙasusuwana duka sun guggulle.

              Zuciyata ta narke kamar danko * tana ɗigowa daga ƙirjina.

                   Ƙarfina ya bushe kamar sakaina, * halshena ya liƙe wa muƙamuƙaina, *

                   an tura ni cikin caɓin Mutuwa.

                       Gama karnuka sun kewaye ni, * ƙungiyar miyagu ta sa ni a tsaka,

                       sun cinye naman hannuwana da ƙafafuna. * Na iya ƙirga dukan ƙasusuwana.

                   Ga yadda suke kallona, suke zura mani ido, *

                   suna rarraba tufafina a junansu, * rigata kuwa suna ƙuria a kanta.

              Amma kai, Yahweh, kada ka yi nisa, * ya Rundunata, ka gaggauta ka taimake ni!

              Ka ceci wūyana daga takobi, * da fuskata daga ruwan gatari.

         Ka kuɓutad da ni daga bakin zaki, * ka sa in rinjayi ƙahonin ɓakwane,

         don in yi shelar sunanka ga yanuwana, * in yabe ka a tsakiyar jamaa.

    Masu tsoron Yahweh, ku yaba masa, * ku jikokin Yakubu, ku girmama shi, * ku tsorace shi, dukan jikokin Israila.

         Gama bai rena ba, * ko ƙin waƙar gajiyayye.

              Bai kuma kau da fuskarsa daga gareshi ba, * amma da ya yi kuka, yā ji shi.

              Zan raira yabonka sau ɗari * wurin babbar jamaa * zan biya alkwaran da na rantse, ya Shugaba.

         Masu tsoronsa za su ci abinci, * matalauta za su ƙoshi.

    Masu neman Yahweh za su yaba masa, * zukatanku su daɗe har abada!

Dukan iyakokin duniya za su tuna, * su komo wa Yahweh.

Dukan kabilan alummai ma * za su yi maka sujada.

    Gama Yahweh sarki ne, * mai mulki kuma na alummai.

         Lalle, dukan masu yin barci a Lahira * za su yi masa sujada.

    Duk waɗanda suka sauka a Caɓin * za su durƙusa masa, * gama Mai nasara yakan mayar da rai.

Bari jikokina su bauta masa, * su ba da labarinsa har abada.

Su soma ba da shaidar nagartarsa * ga mutanen da za a haifa, cewa ya yi abin.

Zabura ta 23

Yahweh makiyayina ne, * ba zan yi rashi ba, * zai sa ni in kwanta wurin ɗanyar ciyawa.

Zai bi da ni wurin ruwan de ke kwance, * don ya farfaɗo mani da rai.

Zai bishe ni wuri mai yawan ciyawa, * kamar yadda ya dace da sunansa.

    Ko da yake ina tafiya * ta tsakar duhu baƙiƙ ƙirin,

    ba zan ji tsoron hatsari ba, * domin kana tare da ni.

         Sandarka da kerenka * ba shakka za su yi mani jagora.

    Kakan shirya mani abinci * a gaban magabtana.

    Kakan shafa mani mai a ka, * ƙoƙona ya cika har yana zuba.

Ashe, alheri da rahama za su raka ni * duk kwanakin raina.

Zan kuma zauna a gidan Yahweh * kwanaki marasa iyaka.

Zabura ta 24

Ƙasa da duk wadatarta na Yahweh ne, * da duniya da mazaunanta.

Gama ya gina ta a bisa tekunan da ke ƙarƙashin ƙasa, * ya kafa harsashinta bisa igiyar tekuna.

    Wa zai hau kan dutsen Yahweh? * Wa zai tsaya a tsattsarkan wurinsa?

    Sai wanda hannunsa da zuciyarsa ba su da aibu, * wanda bai juya nufinsa ga gunki ba, * ko kuma ya rantse a kan allahn ƙarya.

         Shi ne zai karɓi albarka daga wurin Yahweh, * da nagarta daga Allahnsa maceci.

         Ku nemi Sarkin zamanai, * ku bi Wanda ya zauna tare da Isiyaku.

    Ku ɗaga kanku, ya ku ƙofofi, * ku ɗagu, ku ƙofofin Madauwami, * Sarkin ɗaukaka na zuwa.

    Wanene Sarkin ɗaukaka? * Yahweh ne mai ƙarfi mai iko, * Yahweh mai iko a yaƙi.

Ku ɗaga kanku, ya ku ƙofofi, * ku ɗagu, ku ƙofofin Madauwami, * Sarkin ɗaukaka na zuwa.

Wanene Sarkin ɗaukaka? * Yahweh ne mai runduna, * shi ne Sarkin ɗaukaka.

Zabura ta 25

A gare ka, Yahweh, * ni ke sa raina.

    Ya Allahna, a gare ka ni ke dogara, * kada in kunyata, * kada magabtana su yi murna a kaina.

    Duk wanda ya kira ka ba zai kunyata ba, * sai matsegunta marasa aminci su kunyata.

         Ka nuna mani hanyoyinka, Yahweh, * ka koya mani tafarkunka.

         Ka sa in bi ka da aminci, ka ma koya mani, * domin kai ne Allah mai cetona, * gare ka ni ke kira duk yini.

              Ka tuna, Yahweh, da rahamarka da alherinka, * yadda tun filazal suke.

              Zunubaina da kurakuraina na ƙuruciyata, * kada ka tuna da su!

              Amma ka tuna da ni bisa ga alherinka, * bisa ga ƙaunarka, Yahweh.

                   Yahweh mai nagarta da gaskiya ne, * Maɗaukakin Zati, ya kan koya wa masu zunubi hanyarsa.

                   Yakan bi da matalauta ta adalcinsa, * yakan koya masu hanyarsa.

                   Dukan hanyoyin Yahweh alheri ne da aminci * ga waɗanda suke kiyaye kaidodin yarjejeniyarsa.

                       Albarkacin sunanka, Yahweh, * ka gafarta zunubina, * ko da yake babba ne.

                   Wane mutun ne ke tsoron Yahweh? * Shi ne wdanda zai koya wa hanyar da zai zaɓa.

                   Ransa zai zauna lafiya, * jikokinsa ma za su gaji ƙasar.

                   Zumuncin Yahweh ya ɗauru da masu tsoronsa, * yana sanar masu da yarjejeniyarsa.

              Idanunna kullun ga Yahweh ne, * domin zai kau da ƙafafuna daga tarko.

              Ka dube ni, ka ji tausayina, * domin ina kaɗaici a cikin matsatsi.

         Damuwa ta matsa wa zuciyata, * ka fid da ni daga ɓacin raina.

         Ka dubi wahalata da azabata, * ka kawas da dukan zunubaina.

    Ka dubi yawan magabtana, * masu hainci da su ke ƙina.

    Ka kiyaye raina, ka kuɓutad da ni, * kada in kunyata, domin na nemi kāriya a wurinka.

    Ka sa nagarta da aminci su kiyaye ni, * domin na kire ka.

Ya Allah, ka ceci yayan Israila * daga dukan wahalarsu.

Zabura ta 26

Ka hukunta ni, Yahweh, * gama na riƙa bin gaskiya.

Na dogara ga Yahweh, * ban girgiza ba.

    Ka bincike ni, Yahweh, ka auna ni, * ka gwada zuciyata da tunanina.

         Lalle, a kullun ƙaunarka tana cikin hankalina, * ina kuma bin ka da aminci.

              Ban zauna da masu bautar gumaki ba, * ban shiga gidan masu jahilci ba.

                   Na tsargi taron masu aikata mugunta, * ban taɓa zama da miyagu ba.

                       Na wanke hannuwana ba tare da aibu ba, * don in zagaya bagadinka, Yahweh,

                       don in ɗaga muryar yabonka, * in faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.

                   Yahweh, ina ƙaunar zama a gidanka, * inda ɗaukakarka take.

              Kada ka runtume ni da masu zunubi, * ko haɗa raina da matsafa.

         A hannunsu na hagu akwai gumaka, * hannunsu na dama cike ya ke da cin hanci.

    Ni kam, zan riƙa yin halin kirki, * ka fanshe ni, ka yi mani rahama.

Ƙafata ta tsaya daram da masu gaskiya, * a cikin taronsu ne nike durƙusa wa Yahweh.

Zabura ta 27

Yahweh ne haskena da cetona, * to, wa zan ji tsoro?

Yahweh ne mafakar raina, * to, wa zai sa in firgita?

    Saad da miyagu suke yaƙina * don su ci namana,

    maƙiyana da magabtana * suna tuntuɓe, suna fāɗuwa.

         Ko da rundunar soja ta kewaye ni, * zuciyata ba za ta razana ba.

         Ko da mayaƙa sun taso mani, * zan yi taho mu gama da su.

              Abu guda na roƙa sau ɗari, * shi ne, Yahweh, ni ke nema:

              In zauna a gidan Yahweh, * dukan kwanakin raina,

              in ga kyan Yahweh, * in tashi kowace safiya a cikin Haikalinsa.

                   Zai darajanta ni a Zaurensa, * bayan Mugunyar Rana.

                       Zai ɓoye ni a innuwar tantinsa, * a kan dutse mai tsayi.

                       Yanzu an ɗaga kaina * bisa magabtana da ke kewaye da ni.

                   Zan yanka hadayun murna a tantinsa, * zan yi kiɗa da waƙa ga Yahweh.

              Ka ji muryata, Yahweh, lokacin da na yi kira, * ka ji tausayina, ka amsa mani.

              Zo mana, in ji zuciyata, ka nemi fuskarsa! * Fuskarka zan nema, Yahweh.

              Kada ka juya mani baya, * kada ka watsar da bawanka cikin hushi, * ka zama mataimakina.

         Kada ka ƙi ni, * kada kuwa ka yashe ni, * ya Allah mai cetona.

         In ubana da uwata sun yashe ni, * Yahweh zai riƙe ni.

    Yahweh, ka nuna mani hanyarka, * ka yi mani jagora a hanyarka mara gargada * saboda magabtana.

    Kada ka bari magabtana su haɗiye ni, * don akwai shaidar zur a kaina, * suna magana da magudi.

Na amince da Mai Nasara, * don in ga kyan Yahweh * a ƙasar rai madauwami.

Ka jira Yahweh, ka ƙarfafa, * bari zuciyarka ta ɗaure * ka jira Yahweh.

Zabura ta 28

A gare ka, Yahweh, nike kira, * Dutsena, * kada ka ƙi amsa mani.

In ba ka amsa mani ba, * zan yi kama da waɗanda suka gangara Ramin.

    Ka ji roƙona don jinƙai, * da nike kira gare ka,

    da nike ɗaga hannuwana * wajen tsarkakken dandalinka.

         Kada ka haɗa ni da miyagu, * ko masu aikata mugunta.

         waɗanda ke maganar salama da maƙwabtansu, * amma zukatansu cike suke da hainci.

              Ka yi masu abin da suka yi, * da sakayya gwargwadon ayyukan da suka yi.

              Ka biya su bisa ga aikin hannuwansu, * ka ba su abin da ya cancance su.

         Gama ba su kula * da abin da Yahweh ya yi ba, * ko kuwa aikin hannuwansa.

         Shi ma zai rushe su, * ba kuwa zai sake gina su ba.

    Yabo ga Yahweh! * domin ya ji roƙona na jinƙai.

    Yahweh ne garkuwata mai ƙarfi, * zuciyata ta amince da shi.

Na koma ƙuruciyata, * zuciyata tana murna, * da waƙata zan yabe shi.

Yahweh makara da mafakarmu, * shi Macecin shafaffen sarkinsa ne.

Ka ba jamaarka nasara, * ka yi wa gādonka albarka, * ka kiwace su, ka tallafa masu har abada.


Zabura ta 29

Ku biya wa Yahweh, ku alloli, * ku biya shi ɗaukaka da yabo, * ku biya Yahweh abin da ya dace da sunansa.

Ku rusuna a gaban Yahweh. * Mai-Tsarkin ya bayyana.

    Ana jin muryar Yahweh a bisa tekuna, * Allah Maɗaukaki yana tsawa, * Yahweh yana ƙara bisa teku.

    Muryar Yahweh ƙarfi ce, * muryar Yahweh ɗaukaka ce.

         Muryar Yahweh na tsaga itatuwan al-ul, * Yahweh na tsaga itatuwan alul na Labanon.

              Muryar Yahweh tana tatsatsi * da harsunan wuta.

              Yana sa Labanan tsalle kamar ɗan maraƙi, * da Sirion kamar ɗan sa.

         Muryar Yahweh tana girgiza ƙasar jeji, * tana girgiza ƙasar jejin Kadesh.

    Muryar Yahweh tana sa bareyi haifuwa, * tana zabge ganyen daji duka,

    a cikin Haikalinsa kuma * Maɗaukakin yana bayyana.

Tun ruwan tsufana Yahweh ya zauna gadon mulkinsa, * tun filazal Yahweh sarki ne.

Yahweh yakan ba jamaarsa nasara. * Yahweh yana sa masu albarka da salama.

Zabura ta 30

Ina girmama ka, Yahweh, * gama ka ta da ni, * ba ka kuma bar magabtana su yi mani dariya ba.

    Yahweh Allahna, * na yi kuka gare ka, * ka ma warkad da ni.

    Yahweh ya tsamo ni daga Shawol, * bayan gangarawata a Rami ka mayar mani da rai.

         Ku yi waƙa ga Yahweh, ku masu bautarsa, * ku yabi sunansa mai tsarki.

         Gama mutuwa tana cikin hushinsa, * amma rai madauwami yana wurin alherinsa.

         Da duhu ya yi ana kwanciya da kuka, * amma da Asuba ana tashi da sowa ta murna.

              A wautance sai na ce, * Har abada ba zan yi tuntuɓe ba.

                   Yahweh, alherinka ya ƙarfafa ni * fiye da manyan tsaunuka.

              Amma da ka kau da fuskarka, * sai na jijjiga ƙwarai.

         Ina kira gare ka, Yahweh, * Ubangijina, ina neman jinƙai.

         Wane amfani za a samu daga hawayena? * ko gargarawata Ramin?

         Caɓi zai taɓa yabonka? * ko zai yi shelar amincinka?

    Yahweh, kasa kunne, ka ji tausayina, * Yahweh, ka zama mai taimakona.

    Ka mai da makokina rawa, * ka kwance tsummokina, ka yi mani ɗamara da murna.

    Bari zuciyata ta yi waƙar yabonka, * kada in sake yin bakinciki.

Yahweh Allahna, * zan gode maka har abada.

Zabura ta 31

A gare ka, Yahweh, na zo neman tsari, * kada in kunyata, ya Madauwami, * a cikin amincinka ka fanshe ni.

    Ka kasa kunne gare ni, * ka cecei ni da hanzari.

    Ya Dutsen mafaka, ka zama nawa, * ya Barikin Tsira, ka cece ni.

         Gama kai ne dutsena wurin tsira, * albarkacin sunanka za ka yi mani jagora, ka nuna mani hanya.

         Za ka yanta ni daga tarkon * da suka ɗana mani, * domin kai ne mafakata.

              A cikin hannunka nike danƙa ruhuna, * ka fanshe ni, Yahweh Allah.

         A gaskiya na ƙi * jinin masu bautar gumakan banza.

         Na dogara ga Yahweh, * zan yi farinciki da murna saboda alherinka.

    Lokacin da ka ga wahalata, * kā lura da ni gāba da Magabci.

    Ba ka ƙulle ni a hannun Magabci ba, * ba ka ma sa ƙafafuna cikin Mugun Daji ba.

         Yahweh, ka ji tausayina, * gama ina cikin shan wahala.

         Idona ya lalace da baƙinciki, * har da maƙogwarona da cikina.

              I, rayuwata ta gaji saboda makoki, * shekaruna kuma saboda nishi.

              Ƙarfina ya gaza cikin wahala, * ƙasusuwana sun tabke, * ana kuma cin kayan cikina.

                   Na zama abin baa har ma ga maƙwabtana, * na zama balai mai ban tsoro ga abokaina; * waɗanda suka gan ni a hanya suna guduna.

                   Na yanƙwane, ba hankali kamar matacce, * na zama kamar fasasshen tulu.

                       Gama ina jin raɗe-raɗe masu yawa, * ta koina razana ta kewaye ni,

                       lokacin da suka taru suna shawara a kaina, * suna ƙulla maƙircin kashe ni.

                   Amma a gare ka na dogara, * Yahweh, * ina cewa, kai ne Allahna.

                   Matakan rayuwata suna a hannunka, * ka cece ni daga hannun magabtana * da na masu matsa mani lamba.

              Ka sa fuskarka ta haskaka bawanka, * ka cece ni ta alherinka.

              Yahweh, kada in kunyata, * lokacin da nike kiranka.

         Bari miyagu su kunyata, * a jefad da su Shawol.

         Ka yi wa leɓunan maƙaryata takunkumi, * waɗanda ke maganar fariya da gaba gaɗi * ga Mai Gaskiya Mai Zamanu.

    Abubuwan alherai barkatai ne * ka shirya wa waɗanda suke jin tsoronka,

    abubuwan da ka tanada wa masu dogara gare ka, * a gaban mutane.

         Kā ɓoye su a maɓoyar zatinka * daga ƙarairayin mutane.

         Kā kare su a zaurenka * daga tankiyar harsuna.

              Alhamdu ga Yahweh! * Gama ya nuna mani ƙauna mai bammamaki * daga ƙaƙƙarfan birninsa.

         Dā fargabata tana sa in zaci: * An raba ni a gabanka.

         Amma kā ji roƙona na jinƙai * lokacin da na yi kira gare ka.

    Ku ƙaunaci Yahweh, dukanku masu bauta masa, * gama Yahweh yana kiyaye amintattunsa.

    Amma yana sakayya mai zafi * ga masu aikata izgili.

Ku ƙarfafa zukatanku, * dukanku masu sa zuciya ga Yahweh.

Zabura ta 32

Albarka ga wanda aka yafe wa laifinsa, * wanda aka gafarta zunubinsa.

Albarka ga wanda Yahweh bai sa wa laifi ba, * wanda ba zamba a ransa.

    Amma ni kamar fasassar tukunya nine, * ƙasusuwana sun rafke * saboda nishina wuni zubut.

    Ya Maɗaukaki, dare da rana * hannunka yana yi mani nauyi.

    Na kaɗu, ya Shaddai, * kamar farin bazara.

         Na sanad da zunubina gare ka, * ban kuma ɓoye laifina ba.

         Na ce, Maɗaukaki, zan faɗi * laifofina, Yahweh. * Kā gafarta kurena da zunubina.

              Don haka ya kamata kowane mai bauta maka * ya yi addua zuwa gunka.

         Lokacin da runduna ta kusato, * ko babbar ambaliyar ruwa ta malalo, * ba za su kai gare shi ba.

         Kai ne mafakata, * ka kiyaye ni daga masu afka mani, * ya Matsarata, ka cece ni, ka kewaye ni.

    Zan karantad da kai in koya maka * hanyar da za ka bi. * A kullun idona baya rufu gare ka.

    Kada ka zama kamar doki * ko alfadari mara hankali.

    Da ragama da linzami ne * za a iya sarrafa shi, * sannan ka kusance shi.

Azabun miyagu da yawa suke, * amma duk wanda ya dogara ga Yahweh, * da ƙauna zai rungume shi.

Ku yi farinciki da murna ga Yahweh, ku adilai, * ku yi sowar farinciki, dukanku masu zucya ta kirki.

Zabura ta 33

Ku yi farinciki ga Yahweh, ku masu gaskiya, * ku yabi Maɗaukaki, ku adalai.

    Ku yabi Yahweh da molo, ku kaɗa masa garaya mai tsarkiya goma.

    Ku raira masa sabuwar waƙa, * ku yi kiɗi da gwaninta da muryoyi masu daɗi.

         Gama maganar Yahweh daidai ta ke, * dukan ayyukansa kuma abin dogara ne.

         Yana ƙaunar abin da ke na adalci da adalci, * da alheri Yahweh ya cika duniya.

              Da umurnin Yahweh aka yi sammai. * Ta kalmar da ya faɗi * aka yi rundunar taurari.

              Yana tara tekuna a cikin tulu, * yana sa zurfafan tekuna a cikin rumbu.

              Ku ji tsoron Yahweh, ku dukan duniya, * girmama shi ku dukan mazaunan duniya.

                   Ya yi magana, ta zauna, * ya yi umurni, abubuwan sun kasance.

                   Yahweh yana sukulkuce shirin alummai, * yana mai da tsare-tsaren jamaa banza.

                   Amma shirin Yahweh ya tabbata tun filazal, * manufofinsa ma na dukan zamanai ne.

                       Mai murna ce alummar * da Yahweh Allahnta ya albarkace ta,

                       jamaar da ya zaɓa * ta zama abin gadonsa.

                   Yahweh yana kallo daga sama, * yana ganin dukan yanadan.

                   Daga inda ya zauna a kan kursiyinsa yana kallon * dukan mazaunan duniya.

                   Mahallicin yana binciken zukatansu, * Mai-Gani yana kallon dukan ayyukansu.

              Sarki baya nasara * da ƙarfin mayaƙa.

              Haka ma jarumi baya kuɓuta * saboda ƙarfinsa.

              Dokinsa baya da amfani don cin nasara, * haka ma ƙarfin rundunar yaƙinsa don kwana lafiya.

         Yahweh yana kare masu tsoronsa, * waɗanda ke dogara ga alherinsa.

         Yana cetonsu daga mutuwa, * daga yunwarta yake kare rayukansu.

    Ga Yahweh muke sa zuciya, * Shi ne mai tsare mu da garkuwarmu.

    Muna murna saboda shi, * mun amince da sunansa mai tsarki.

Yahweh, ka sa tausayinka ya kasance tare da mu, * tun da a gare ka muke sa zuciya.

Zabura ta 34

Zan albarkaci Yahweh kulluni, * a kowane lokaci yabonsa yana bakina.

A wurin Yahweh ruhuna zai sami ɗaukaka, * bari gajiyayyu su ji, su yi murna.

    Ku taya ni girmama Yahweh, * mu ɗaukaka sunansa tare.

    Na yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa mani, * daga dukan fargabana ya kuɓutad da ni.

         Sun dube shi, fuskokinsu sun yi haske, * ba za su kunyata ba har abada.

         Gajiyayyen nan ya yi kira, * Yahweh ya ji shi, * daga dukan ɓacin ransa ya cece shi.

    Malaikan Yahweh yana sintiri * kewaye da masu tsoronsa, * domin ya cece su.

    Ku ɗanɗana, ku tsotsa sosai, * gama Yahweh yana da zaƙi, * mai albarka ne mutumin da ya amince da shi.

         Ku ji tsoron Yahweh, ku tsarkakansa, * gama masu jin tsoronsa ba za su rasa kome ba.

         Mawadata za su yi talauci, su yi yunwa, * amma masu neman Yahweh, ba za su rasa albarka ba.

              Ku zo, yayana, ku saurare ni, * zan koya maku tsoron Yahweh.

              Akwai wani mutun da ke son tsawon rai? * da lokaci don ya daɗe yana cin albarka?

         To, ka tsare halshenka daga mugunta, * leɓenka kuma maganganun ƙarya.

         Ƙi mugunta, ka aikata alheri, * nemi salama, ka bi ta.

    Idanun Yahweh suna kallon masu gaskiya, * kunnuwansa kuma suna sauraren kukansu.

    Hushin Yahweh kan masu aikata mugunta ya ke, * domin ya shafe tunawa da su a duniya.

         Lokacin da masu gaskiya suke yin kuka, Yahweh yana jinsu, * don ya cece su daga dukan ƙacin ransu.

         Yahweh na kusa da waɗanda suka karai, * waɗanda suka fid da zuciya ma yana cetonsu.

    Gwaje-gwajen masu gaskiya yawa gare su, * amma daga dukansu Yahweh yana cetonsu.

    Yana lura da dukan ƙasusuwansa, * ko ɗayansu ba zai karye ba.

Ƙeta zata kashe mugu, * maƙiyan masu gaskiya ma za su hallaka.

Yahweh yana fansar rayukan bayinsa, * masu amince wa shi ma ba za su hallaka ba.

Zabura ta 35

Yahweh, ka yi faɗa da masu faɗa da ni, * ka yi yaƙi da masu yaƙi da ni.

    Ka ɗauki garkuwarka da warwaji, * ka wo mani gudummuwar yaƙi.

    Ka zaro mashinka da gatari, * don ka yi arangama da masu jan-daga da ni.

    Ka gaya wa ruhuna cewa, * ni ne nasararka.

         Masu neman raina, * bari su kunyata da ƙasƙanci.

         Masu yi mani maƙarkashiya * su juya da kunya.

              Su zama kamar ƙaiƙayi a gaban iska, * malaikan Yahweh yana tasa ƙeyarsu.

              Bari ƙaddararsu ta zama Duhu da Hallaka, * malaikan Yahweh yana tangaza ƙeyarsu.

         Gama a ɓoye sun gina mani rami, * sun ɗana tarko suna haƙon raina.

         Bari Ramin ya ba su mamaki, * tarkonsu ya kama su, * su kuma fāɗa cikin ramin da suka gina.

    Amma ruhuna zai yi murna da Yahweh, * ya ji daɗi cikin nasararsa.

    Dukan ƙasusuwana za su ce, * Yahweh, wa ke kama da kai?

    Kā kuɓutad da gajiyye daga hannun wanda ya fi shi ƙarfi, * shi da mabukaci daga hannun mai zaluntarsu.

         Mashaidan ƙarya sun tayar mani, * waɗanda ban sani ba sun yi mani tambayoyi.

         Sun saka mani alheri da mugunta, * suna baƙanta ruhuna.

             Amma ni, lokacin da suka busa sarewa, * na sa tsumma.

                 Na hori kaina ta wurin azumi, * adduata ta liƙe a ƙirjina, * sai ka ce abokina ko kuma ɗanuwa.

                     Ina tafiya kamar mai makokin mahaifiyarsa, * na dukufa da ɓakinciki.

                     Da na yi tuntuɓe, sai su fashe da dariya, * yan dambe sun kewaye ni.

                 Waɗanda ban sani ba suna ta yayyage ni, * ba su kuma dena yi mani ƙaraiyayi ba.

             Masu baa kewaye da ni * suna ta murguɗa mani baki.

        Ya Ubangiji, don me ka tsaya kana kallo kawai? * Ka ceci raina daga ramukansu * fuskata kuma daga kuyakuyan zakoki.

        Zan gode maka a cikin babban taro, * a cikin babban biki ma zan yabe ka.


    Kada magabtana masu hainci su yi murna a kaina, * ko ma magabtana masu limshe idanu.

    Gama ba sa yin maganar salama, * amma suna afka wa marasa galibu na ƙasar.

        Sun shirya makirci, * duk sun wage bakunansu a kaina.

        Suna cewa, Aha, Aha! * mun gan shi.

              Duba, Yahweh, kada ka yi shuru, * ya Ubangiji, kada ka yi nesa da ni.

                    Hanzarta ka zaburo don kāre ni, * ya Ubangijina da Allahna, ka taya ni fama.

                    Yahweh, ka kāre ni a cikin adalcinka, * ya Allah, kada ka bari su yi mani dariya,

              ko su yi fahariya a cikin zukatansu, * su ce, Haba, bakinmu ya kama shi, * ko su ce, Mun gama da shi.

         Duk masu murna da rashin katarina, * bari su kunyata, su sha ƙasƙanci.

         Duk masu shuka ƙarya a kaina, * bari a lulluɓe su da kunya da ƙasƙanci.

    Amma duk masu son yin nasarata, * ka sa su yi sowa ta murna.

    Su dinga cewa: * Yahweh akbar! * mai son zaman lafiyar bawansa.

Sannan ne halshena zai yi shelar adalcinka * in kuma yi yabonka dukan yini.

Zabura ta 36

Zunubi yana hura birnin zuciyar mugu, * baya ma fahimtar maanar tsoron Allah.

    Amma Allahnsa zai hallaka shi da harara, * tun da yake ya ga saɓonsa.

    Maganarsa cike take da miyagun ƙarairayi, * ƙetarsa tana hana shi tunani ko yin abin kirki.

Yana ƙaga mugunta a kan gadonsa, * kamin ya fita aikatata, * baya ma jin kunyar aikata kowane mugun abu.

    Yahweh, ƙaunarka daga sama take, * amincinka ya kai har cikin gajimarai.

    Nagartarka ta milla sama kamar manyan duwatsu, * ƙaddararka tana da zurfi kamar teku.

         Yahweh, kakan adana mutane da dabbobi, * alherinka akwai girma!

    Alloli da mutane suna samun mafaka * a innuwar fukafukanka.

    Suna biki da abinci mai kyau na gidanka, * kana shayar da su kuma daga kogin alherinka.

Kai ne tushen rai, * a cikin aljannarka za mu ga haske.

    Ci gaba da ƙaunatar waɗanda suka san ka, * yi alheri ga masu zukatai nagari.

    Kada ƙafar mai girman kai ta cim mani, * kada dantsen mugu ya yā da ni ƙasa.

Dubi yadda masu aikata mugunta ke faɗi, * sun fāɗi ƙasa warwas, ba su iya tashi.

Zabura ta 37

Kada ranka ya ɓaci saboda miyagu, * kada kuma ka ji haushin masu aikata sharri.

Domin sauran kaɗan za su bushe kamar ciyawa, * kamar ɗanyen ganye za su shuɗe.

    Ka dogara ga Yahweh, ka aikata nagarta, * ka zauna a ƙasar, ka ci wadatarta.

    Ka gamsu da Yahweh * zai kuwa biya maka bukatar zuciyarka.

         Ka danƙa dabararka ga Yahweh, * ka dogara gare shi, zai kuwa cika ta.

         Zai sa adalcinka ya haskaka kamar rana, * hakkinka kuma kamar tsakar rana.

         Ka jira Yahweh, * ka sa zuciya gare shi.

         Kada ranka ya ɓaci kan mutumin da ya arzuta, * yana nasara kan miyagun shirye-shiryensa.

    Dena hushi, ka ya da harzuƙa, * kada ka cika damuwa, lahani kawai take jawowa.

    Domin za a sassare miyagu, * amma tabbaci hakika masu kira da sunanYahweh za su gaji ƙasar.

Sauran kaɗan miyagu za su shuɗe, * in ka duba gidajensu, ba sa nan.

Amma gajiyayyu za su gaji ƙasar, * za su kuma ji daɗin albarka mai yawa.

    Mugu yakan yi wa mai kirki maƙarƙashiya, * har yana cizon haƙora a kansa.

    Ubangiji yana yi masa dariya, * domin ya ga ajalinsa yana gabatowa.

         Miyagu suna zaro takobinsu, * suna ɗana baka

         su ka da gajiyayyu da matalauta, * don su karkashe masu aikata gaskiya.

         Takobinsu zai sassoki zukatansu, * bakanninsu kuma za su kakkarye.

              Gara talaucin mai adalci * da wadatar mugu.

              Domin wadatar miyagu zata rushe, * amma Yahweh zai tallafi masu gaskiya.

         Yahweh yana lura da wadatar masu gaskiya, * gadonsu zai wanzu har abada.

         Ba za su bushe a lokacin fari ba, * amma za su ƙoshi a kwanakin yunwa.

    Amma miyagu za su yanƙwane, * magabtan Yahweh za su hallaka

    kamar daji mai ƙonewa, * fiye da hayaƙi za su shuɗe.

    Mugu yakan ci bashi, ya ƙi biya, * amma mai adalci yana bayaswa hannu sake.

    Waɗanda ya sa wa albarka za su gaji ƙasar, * amma waɗanda ya laanta sassare su za a yi.

         Yahweh ne yake kare matakan mutun, * yana kuma tabbatad da tafiyarsa.

         In ya kai hari ba za a yi takara da shi ba, * domin Yahweh yana ɗaga hannunsa.

              Dā ni yaro ne, amma na tsufa, * tun da nike ban taɓa ganin inda aka ya da mai gaskiya ba, * ko kuma a ga yayansa na barar abinci.

              A kullun yakan ba da rance hannu sake, * yayansu kuma albarka ce ke biye da su.

         Rabu da mugunta, ka aikata alheri, * don ka wanzu har abada.

         Domin Yahweh yana ƙaunar masu gaskiya, * baya kuma ya da masu bauta masa.

    Za a hallaka miyagu, * yayansu ma za a sassare su.

    Amma masu gaskiya za su gaji ƙasar, * su zauna cikinta har abada.

Bakin mai gaskiya yana maganar hikima, * halshensa ma na faɗar abin da ke daidai.

Shariar Allah na cikin zuciyarsa, * ƙafafunsa kuma ba za su yi tuntuɓe ba.

    Da mugu ya makirci mai gaskiya, * yana neman kashe shi,

    Yahweh ba zai sa shi a hannunsa ba, * ba ma zai bari a same shi da laifi ba in an tuhunce shi.

         Ka jira Yahweh, * ka kiyaye hanyarsa,

         domin zai ɗaga ka don ka mallaki ƙasar. * Za ka ga ran da za a sassare miyagu.

         Na taɓa ganin mugu da wadata, * ya yi tsawo kamar ƙaƙƙarfan itacen alul.

         Amma ya shuɗe, ba a ƙara ganinsa ba, * na nem shi, amma ba a iya samunsa.

    Ka bi malaikan Kirki, ka dubi malaikan Gaskiya, * gama akwai albarka ga mutumin kirki.

    Amma za a hallaka mutanen banza kwatakwata, * ba ma wata albarka da miyagu za su samu.

Daga wurin Yaweh ceton adalai yake, * shi ne mafakarsu a lokacin hari.

Yahweh ne zai kuɓutad da su, ya cece su, * zai fanso su daga hannun miyagu,

ya ba su kariya, * domin sun nemi mafaka a gunsa.

Zabura ta 38

Yahweh, kada ka tsananta mani loton hushinka, * kada ma ka hore ni da zafin hushinka.

    Gama kibanka sun shisshige ni, * dantsenka kuma ya afko mani.

         Ba lafiya a naman jikina, * saboda haushinka.

         Ba ƙarfi a ƙasusuwana, * saboda zunubina.

    Domin sharrin ƙetata ya dawo kaina, * kamar kaya mai nauyi ya danƙare ni.

         Miyakuna suna zama gyambuna, suna ɗoyi, * don wawancina.

              Duk na yanƙwane, ina kwance, * ina baƙinciki wuni zubut.

              Domin jijiyoyina suna fama da zazzaɓi, * ba lafiya a naman jikina.

         Na gaji, na tafke, * ina kururuwa da nishi a zuciyata.

              Ya Ubangiji, duka ajiyar zuciyata tana gabanka, * kururuwata ba ta barin gabanka.

                   Zuciyata tana harbawa, * ba ni da ƙarfi.

                       Har ma ganin idanuna, * ya dushe.

                       Aminaina da abokan tafiya * sun kauce daga damuwata, * dangina sun yi nesa da ni.

                   Masu neman raina sun kafa mani tarko, * masu son ganin faɗuwata suna bina.

              Balai da lalacewa * suke yi mani fata dukan yini.

         Amma na yi kama da bebe da baya ji, * kamar kurma da baya magana.

              Na zama kamar beben da baya ji, * wanda babu wata tsawatawa daga bakinsa.

              Amma gare ka, Yahweh, kai ne nike jira, * Ubangijina da Allahna, ka amsa mani da nike cewa:

         Kada su yi murna a kaina, * kada su zage ni in na yi sassarfa.

    Gama muguntata ta tsaya a kaina, * bakincikina yana gabana kullun.

         I, ina rungume laifina a gabana, * ina firgita saboda zunubina.

         Maƙiyana masu ƙarfi ne, * magabtana masu hainci suna da yawan gaske.

    Masu rama mugunta da alheri * suna zagina, lokacin da nike nema masu alheri.

Yahweh, kada ka yashe ni, * ya Allahna, kada ka yi nesa da ni.

Ka gaggauta taimakona, * ya Ubangiji, ka cece ni!

Zabura ta 39

Na ce, Zan yi hankali da abin da nike yi, * kada in kuskure da halshena.

Zan yi wa bakina linzami, * saad da mugu ke yin surutu a gabana.

Na yi shuru tsit, * na ƙi yin magana, * damuwata ta taso.

    Zuciyata tana yi mani ƙuna, * in na yi tunani a kai, sai ka ce an cinna mani wuta.

Sai na yi magana, na ce, * Yahweh, ka sanar da ni ƙarshena,

in san ko kwana nawa suka rage mani, * bari in san ajizancina.

Ga shi, ka mai da rayuwata yar guntuwa, * shekaruna a gabanka kamar babu ne.

    Kash! Kowa kamar hayaƙi ne, * kowane mutun siffa ne kawai.

         Kash! Mutun kamar iska yake zagayawa. * Kash! Yana fusata a banza.

         Yana jibge dukiya, * bai kuwa san mai cinta ba.

              Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan roƙa, * Begena yana gare ka.

              Daga dukan taurin kaina ka cece ni, * kada ka mai da ni gurbin wawa.

         Na zama bebe, ban buɗe bakina ba, * ya Ubangiji, yi wani abu!

         Ka kawar mani da bugunka, * domin kulkin hannunka zai hallaka ni.

    Da tsawatawar laifin mutun kake horonsa, * kakan ci jikinsa kamar asu. * Kash! Kowane mutun kamar iska ne.

Yahweh, ka ji adduata. * Ya Allah, ka saurari roƙona.

Kada ka zama bebe ga kwallana, * domin ni baƙo ne a gidanka, * mai ziyara kamar dukan kakannina.

Ka kau da fuskarka daga wajena don raina ya ji daɗi, * kafin in ƙaura, in dena wanzuwa.

Zabura ta 40

Na yi ta kiran Yahweh, * ya kuwa karkato gare ni, ya amsa kukana.

    Ya tsamo ni daga Ramin Hallaka, * daga Lema Mai Caɓi.

         Ya ɗora ƙafafuna a kan dutse, * na taka tudun-na-tsira.

    Ya sanya sabuwar waƙa a bakina, * waƙar yabon Allahnmu.

Da yawa za su gani, su ji tsoro, * su ma dogara ga Yahweh.

    Albarka ta tabbata ga mutumin * da ya dogara ga Yahweh,

    bai juya ga gumaka ba, * ko ga siffofin ƙarya.

         Yahweh, kā yi manyan ayyuka, * ya Allahna, kā aikata alajibai masu bammamaki.

              Kana tunaninmu kullun, * ba wani kamarka.

         Da na so in faɗe su duka, * sun fi gaban ƙidaya.

              Ba ruwanka da hadaya ko baiko, * shi ya sa ka shirya kunnena ya ji.

              Ƙonannen baiko da na gafarar zunubi * ba ka bukata.

                   Sannan na yi alkawali na ce, * Ga shi, ina zuwa.

                   A cikin shafofin Littafi ne * aka rubuta wajibaina.

                   Ina jin daɗin aikata nufinka * ya Allahna, shariarka tana cikin birnin zuciyata.

              Na bayyana albishir mai daɗi na cetonka * ga babban taron jamaa.

              I, ban kulle leɓunana ba, * kai ma ka sani, Yahweh.

         Ban rufe alherinka * a birnin zuciyata kaɗai ba.

              Na bayyana amincinka * da aikinka mai ceto.

         Ban ɓoye ƙaunarka * da amincinka ga babban taron ba.

    Yahweh, kai ba ka hana ƙaunarka * zuwa gare ni ba.

    Alherinka da amincinka * suna kiyaye ni a kullun.

Amma wahaloli sun kewaye ni, * har ba su ƙidayuwa.

Ƙaiƙan zunubaina ya komo mani, * har bana iya tsira.

    Sun fi gashin kaina yawa, * zuciyata kuma ta karai.

    Gaggauta, Yahweh, ka cece ni, * Yahweh ka yi hanzari ka taimake ni.

         Bari dukan masu neman raina * su kunyata, su sha ƙasƙanci.

         Duk masu neman kisa * su koma da kunya da ƙasƙanci.

         Duk masu ce da ni, Yauwa, yauwa! * bari su karai don tseguminsu.

    Bari dukan masu nemanka * su yi murna da farinciki a wurinka.

    Bari dukan masu son cetonka * su yi ta cewa: Yahweh akbar!

Ko da nike gajiyayye da mabukaci, * Ubangiji zai tuna da ni.

Kai ne mataimakina, macecina, * ya Allahna, kada ka yi jinkiri.

Zabura ta 41

Albarka ga mai magana da azanci, * a lokacin hatsari Yahweh ya cece shi.

    Yahweh ya kiyaye shi, ya tsawanta rayuwarsa, * ya yi masa albarka a duniya, * kada ya ba da shi ga magabtansa.

    Yahweh ya tallabe shi a kan gadon jiyyarsa, * ka yi masa rangwame, * ka kau da ciwonsa.

         Na ce, Yahweh, ka ji tausayina, * ka warkad da ni, * ko da yake na yi maka laifi.

              Magabtana suna zagina, suna cewa, * Yaushe ne zai mutu, a manta da sunansa?

              In waninsu ya zo ya gaishe ni, * yana ƙaga ƙarya a zuciyarsa.

              Yana tattara wa kansa ƙeta, * ya fita waje, yana tsegumguma.

                   Duk maƙiyana, ya Maɗaukaki, * suna raɗa da junansu a kaina, * suna shirya mani maƙarƙashiya, cewa:

                   Zuba masa wani abu mai dafi, * domin wanda yake kwance kada ya sake tashi.

              Har ma abokina * wanda na amince da shi,

              wanda muke ci a kushi ɗaya, * yana ƙulla ƙarairayi a kaina.

         Amma kai, Yahweh, ka ji tausayina, * ka tashe ni, * domin in saka masu.

    Sannan ne zan san kana sona, * in dai Magabcina bai yi rinjaye a kaina ba.

    Saboda cikar kirkina ka sure ni, * ka aje ni a gabanka har abada.

Albarka ga Yahweh, Allah na Israila, * tun filazal har abada abadin.

Amin. Amin.

Zabura ta 42

Kamar yadda kishimi ke kururuwa don ruwan rafi, * haka raina ke kururuwa gare ka, Allah.

Raina yana jin ƙishi, * Allah, ya rayayyen Allah.

Yaushe ne zan soma sha * a gaban fuskar Allah?

    Hawayena sun zama abincina * dare da rana,

    a kullun kuma ana tambayata, * Ina Allahnka?

Waɗannan abubuwa nike tunawa, * zan zubar da ruhuna gare shi

in na ƙetare dokin ƙofa, * in na kwanta rub da ciki * kusa da gidan Allah,

inda ake yin sowar ta yabon Allah, * tare da taron alhazan Ƙudus.

    Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

    Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna

         Zuciyata ta karaya, * Maɗaukakin Zati, ina tunawa da kai

              daga Magangaran Lahira duk da tarunanta, * daga gindin dutsenta.

              A can ruwa mai zurfi ke kiran ruwa mai zurfi, * yana amsa wa tsawarka.

         Dukan raƙuman ruwanka masu husata * suna taɗiye ni.

              Dā Yahweh yakan aiko mani da alherinsa da rana, * da ruyarsa kuma da dare.

         Ina yin addua ga Allahna rayayye, * ina cewa, ya Allah, Dutsena,

              me ya sa ka mance da ni? * Me ya sa nike sha takaici

              saboda matsawar Magabci, * saboda Makashin cikin ƙasusuwana?

         Maƙiyana suna bakanta mani, * a kullun suna cewa da ni, * Ina Allahnka?

    Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

    Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna

(Zabura ta 43)

Ka kāre ni, ya Allah, * ka tsaya wa hakkina.

Ka fanshe ni daga hannun marasa bin Allah, * daga hannun mayaudara, marasa gaskiya.

    Tun da kai ne Allah Mafakata, * me ya sa ka yā da ni?

    Dom me nike shan takaici * saboda matsawar Magabci?

         Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, * i, bari su yi mani jagora.

         Bari su kai ni zuwa dutsenka mai tsarki * wurin zamanka.

    Bari in tafi wurin bagaden Allah, * gun Allah, mai faranta mani rai.

    Bari in yabe ka da garaya, * ya Allah, Allahna.

Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna.

Zabura ta 44

                   Ya Allah, mun ji da kunnuwanmu,* kakanninmu sun gaya mana

                   ayyukan da ka yi a zamaninsu, * a zamanin dā hannunka ya aikata alajibai.

                   Kā kori sauran alummai, * amma kā dasa taka.

                   Kā warwatsa sauran kabilu, * amma kā sa taka ta yi toho.

Ba da kaifin takobinsa suka ci ƙasar ba, * ba da ƙarfin dantsensu suka yi nasara ba,

amma ta hannun damanka da dantsenka ne * da hasken fuskarka, * tun da yake ka ƙaunace su.

    Kai ne Sarkina, Allahna, * Shugabana, Macecin Yakubu.

    Ta wurinka mun fatattaki abokan gabanmu, * ta sunanka muka tattaka masu nemanmu da yaƙi.

Domin ban dogara ga bakana ba, * takobina kuma bai sa in ci nasara ba.

Amma ka sa mun yi nasara kan abokan gabanmu, * ka kuma kunyata maƙiyanmu.

    Da Allah ne muke yin taƙama kullun, * sunanka ne kuma za mu yaba har abada.

         Amma ka yi watsi da mu, ka ƙasƙantad da mu, * ba ka kuma ƙara taya sojojimu ba.

         Ka sa abokan gabanmu su ga ƙeyarmu, * maƙiyanmu kuma sun ƙwace kayanmu.

              Ka bashe mu kamar bisashen da za a yanyanka, * ka warwatsa mu a cikin alummai.

              Ka sayar da mutanenka arha, * ba su yi tsada ba.

         Ka mai da mu abin zagi ga maƙwabtanmu, * abin reni da baa ga waɗanda ke kewaye da mu.

         Ka mai da mu abin zunɗe ga alummai, * abin kaɗa kai ga mutane.

              Wulakancina yana gabana kullun, * kullun ina sane da kunyata,

              saboda muryar mai zagin nan da mai saɓon nan, * saboda magabci da mai neman ramuwa.

         Kowane wulakanci ya zo mana, * amma ba mu mance da kai ba, * ko yin rashin biyayya da yarjejeniyarka.

         Zuciyarmu ba ta juya baya ba, * ƙafafunmu kuma ba su goce daga hanyarka ba,

              ko da yake ka wahalshe mu da ciwon gindi, * ka ma rufe mu da duhu baƙiƙ ƙirin.

         In da mun mance da sunan Allahnmu, * ko mun miƙa hannu ga wani allah,

         ashe Allah ba zai tona wannan ba? * tun da yake ya san lungu-lungu na zuciya.

    Duk da haka, saboda kai ne ake kashe mu yini zubut, * ana ƙirga mu kamar tumakin da za a yanka.

Ka farka! Dom me kake barci, ya Ubangiji, * ka tashi, kada ka yi hushi, ya Jarumi.

    Me ya sa ka kau da fuskarka, * ka mance da ƙuncinmu da danniyar da ake yi mana?

    Domin wūyanmu ya bunkuya cikin turɓaya, * cikinmu ya nane ƙasa.

Ka tashi, ka agaje mu, * ka fanshe mu saboda ƙaunarka.

Zabura ta 45

                       Zuciyata ta wallafa waƙa mai daɗi, * zan raira aikina, ya Sarki,

                       halshena alkalamin ƙwararren marubici ne.

Kai ne mafi kyau a cikin dukan yanadan, * daɗɗaɗar magana na fitowa daga leɓunanka.

Allah, Maɗaukakin Zati, * ya albarkace ka tun filazal.

     Ka ɗora takobinka a kan cinyarka, * ka rinjaya da darajarka, * ka ci nasara da sarautarka.

     Ka rinjaya a harinka saboda gaskiya, * ka ma kāre matalauta.

Alajiban hannunka na dama da kibanka masu tsini * su za su sa ka yi suna.

Alummai za su fāɗi a gabanka, * magabtan Sarki su kwanta sumammu.

               Allah Madauwami ya tabbatar da sarautarka, * sandar sarautarka sanda ce ta gaskiya.

                   Ƙaunaci gaskiya, ka ƙi mugunta, * Madauwamin Zati ya shafe ka, * Allah, Allahnka.

               Mayafanka ne man farinciki, * duk tufafinka su ne mur da aloyes da tafasa.

Ai, akwai gidajen hauren giwa barkatai, * don faranta maka zuciya.

Yayan sarakuna mata na cikin matan fādarka, * sarauniya na tsaye a hannun damanka da kayan zinarya ta Ofir.

     Saurara, ke ɗiya, ki gani, * ki kasa kunne: * Manta da mutanenki * da gidan mahaifinki.

     Domin Sarki yana marmarin kyanki, * i, shi ne ubangijinki, * ki yi masa sujada.

     Riga daga garin Taya tana a cikin kyautayinki, * manyan baƙi ma suna biɗar alherinki.

Dukan tufafinta iri na sarauta ne, * a ciki an yi masu dajiya da zinariya, * gwanayen maɗinka ne suka yi kayanta.

Bari a kai Gimbiya wurin Sarki, * daga baya kawayenta su bi.

Ku zo, bari a raka ta da murna da farinciki, * a shigar da ita fādar Sarki.

               Gurbin kakanninka yayanka za su maye, * za ka maishe su sarakunan dukan duniya.

               Zan yi shelar sunanka a dukan zamanai, * dukan jamaa za su yabe ka, ya Maɗaukaki Madauwamin Zati.

Zabura ta 46

Allah ne maɓoyarmu da mafakarmu, * Mai Duka, mun same shi Macecinmu daga yaƙi.

    Maɗaukakin Zati, ba za mu ji tsoron * muƙamuƙan Ƙalƙashin Ƙasa ba.

    Ko faɗawar duwatsu * a tsakiyar teku,

    ko da ruwayen teku na kumfa, * duwatsu na fāɗuwa cikinsu, * igiyoyin ruwa suna gilme-gilme.

         Allah yana kawo wa birninsa farinciki, * Maɗaukaki yana tsarkake mazauninsa.

         Da yake Allah na cikinsa, * ba zai girgiza ba.

          Zai taimake shi * tun da asuba.

     Alummai sun raunana, * sarautu sun jijjigu.

     Ya yi furci, * duniya ta narke.

Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.

    Ku zo, ku ga ayyukan Yahweh, * wanda ya sa wa duniya albarka.

         Yakan tsaid da yaƙi * har bangon duniya.

         Ya kan karya baka, yana lalata mashi, * yana ƙone karusai da walƙiya.

    Ku kwantar da hankalinku, ku sansance ni ne Allah, * ina bisa alummai, * na ma mallaki duniya.

Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.

Zabura ta 47

Dukanku ƙafarfan ruhuna, ku yi tafi, * ku alloki, ku yi sowa ta murna.

    Yahweh Maɗaukaki mai ban tsoro ne, * babban sarki ne bisa dukan duniya.

    Ya bi mana da mutane, * ya sa alummai a ƙalƙashen ƙafafunmu.

    Ya zaɓi mulkinmu don kansa, * ƙasar Yakubu abar taƙama da yake ƙauna.

         Allah ya hau da sowa, * Yahweh da muryar kakaki.

         Ku raira yabbai, ku alloki, ku raira yabbai, * ku raira yabbai ga Sarkinmu, ku raira yabbai.

    Gama shi ne Sarkin dukan duniya, * ku alloli, ku raira yabo da gwaninta.

    Allah ne ke mulkin alummai, * yana zaune kan tsattsarkan kursiyinsa, * ku sarakunan jamaa, ku tattaru.

Allahn Ibrahim Mai Iko ne, * Allah shi ne Mai duniya, * shi ne kuma mafi dacewa da ɗaukaka.

Zabura ta 48

Yahweh mai girma ne, * ya cancanci matuƙar yabo.

A birnin Allahnmu * akwai tsattsarkan dutsensa.

    Ƙololuwa mai kyan gani, * da ke faranta wa dukan duniya rai,

    Dutsen Sihiyona ne babban birnin duniya, * birnin Sarki mai girma.

    Karagarsa Allah ne * da gwadajjiyar mafaka.

         Gama sarakunan sun taru, * sun kai hari tare.

         Da suka ga garin sun yi mamaki, * suka firgita, suka ranta a noman kare.

              Tsoro ya kama su * i, azaba kamar ta mace mai naƙuda,

              kamar yadda iskar gabas * kan kakkarya jiragen ruwan Tarshishi.

                   Kamar yadd muka ji, * haka muka gani

                       a birnin Yahweh mai runduna, * a birnin Allahnmu.

                   Allah zai tabbatad da shi * har abada abadin.

              Mun tuna da ƙaunarka, ya Allah, *a tsakkiyar Haikalinka.

              Kamar sammanka, ya Allah, * haka yabonka ke kaiwa har bangon duniya.

         Hannun damanka cike yake da alheri, * bari dutsen Sihiyona ya yi murna,

         ƙauyukan Yahuda kuma su yi farinciki, * saboda ayyukanka na tsare su.

    Ku zaga Sihiyona, ku kewaye ta, * ku ƙirga hasumiyoyinta.

    Ku dubi ganuwarta, * ku binciki ginin tsaronta,

donin ku gaya wa tsara mai zuwa, * cewa Birnin nan na Allah ne.

Madauwamin Allahnmu * shi zai bishe mu har abada.

Zabura ta 49

                Ku ji wannan, ku dukan jamaa. * Ku saurara, ku dukan mazauna duniya,

                ƙasƙantattu da ɗaukakakku, * mawadata da matalauta duka.

                Bakina zai yi zancen hikima, * zuciyata za ta furta fahinta.

                Zan kasa kunnena ga misali, * zan raɗa kacinci-kacincina da kiɗin molo.

Don me zan ji tsoron miyagun kwanaki, * ko ƙetar maƙaryata kewaye da ni,

waɗanda ke dogara ga dukiyarsu, * suke fahariya da ɗumbin wadatarsu?

     Kai! Mutun baya iya ceton kansa, * ko ya biya wa Allah fansarsa.

     Gidan Can Ƙasa zai zama fansar ransa, * zai tafi har abada,

          ko da yake dā ya iya rayuwa da murna har abada, * da ma bai ga Ramin ba.

     In Allah ya fuskanci masu hikima, za su mutu. * In ya harari wawaye,

         nan da nan za su hallaka, * su bar wa wasu dukiyarsu.

Loton da suke a madauwamin gidansu, * mazauninsu na har abada,

magadansu a duniya * suna ambaton sunayensu.

A Gidan Ƙasa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka shuɗe.

    Wannan ce ƙadarar mawadata, * da ƙarshen masu mugun kwaɗayi.

    Tamkar bisashe za a jefa su a Shawol, * Mutuwa ce za ta zama mai kiwonsu.

         Za su gangara cikin maƙogwaronta kamar ɗan maraƙi, * Shawol za ta haɗiye gaɓoɓinsu, * Mai Cinyewa zai gama da su.

         Amma Allah zai fanshe ni, * ba shakka zai kwato ni daga hannun Shawol.

    Kada ka yi ƙyashin mai arziki, * lokacin da wadatar gidansa ke haɓɓaka.

    Domin lokacin da ya mutu ba zai tafi da kome ba, * dukiyarsa ba za ta bi shi ba, * ko da ya bauta wa shaawarsa lokacin da yake da rai.

    Duk da ana yabonka in ka arzuta, * za ka shiga taron kakanninka, * waɗanda ba za su ƙara ganin haske ba.

A Gidan Ƙasa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka shuɗe.

Zabura ta 50

Allahn alloli shi ne Yahweh, * ya yi magana, ya kirayi duniya, * daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.

Daga Sihiyona, cikamakin kyau, * Allah ya hasko.

    Allahnmu yana zuwa, * ba zai yi shuru ba.

    Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, * kewaye da shi kuma da hadari mai tsawa.

    Ya kirayi sama da ƙasa * wajen shariar jamaarsa.

Ku tattaro masa masu yi masa bauta, * masu jarjejeniya da shi a gaban hadaya.

Bari sammai su yi shelar hakkinsa, * domin shi ne Allah mai gaskiya.

    Ku saurara, jamaata, zan yi magana, * Israila kam, zan yi magana mai gāba da ke. * Ni ne Allah, Allahnki.

    Ban tsauta maki saboda hadayunki ba, * ko hadayun ƙonawarki da ke gabana kullun.

    Ban biɗi bajimin sa daga gidajenku ba, * ko awaki daga garkunanku,

         tun da yake dukan namomin daji nawa ne, * da dabbobin da ke bisa duwatsu.

         Na ma san dukan tsuntsayen da ke kan duwatsu, * duk mai yawon karkara ma a gabana yake.

         Da na ji yunwa, da ba zan gaya maku ba, * domin duniya tawa ce da dukan abin da ke cikinta.

         Ina cin naman bajimai, * ko in sha jinin awaki?

    Miƙa wa Allah hadayarka ta godiya, * ka cika waadodinku ga Maɗaukaki.

    Sannan ka kira ni a lokacin wahala, * zan cece ka, in kira ka biki.

    Amma game da mugu Allah ya ce: * Ta yaya za ka furta dokokina, * ka ambaci yarjejeniyata da bakinka?

    Tun da yake ba ka son a koya maka, * kana kuma yin watsi da kalmomina.

         Lokacin da ka ga ɓarawo, kana yin gasa da shi, * kana kuma cudanya da mazinata.

         Da bakinka kake furta mugunta, * da halshenka kake saƙa yaudara.

         Ka zauna kana yin gulma da ƙanenka, * kana yaɗa aibu ga ɗan mahaifiyarka.

    Duk ka yi waɗannan abubuwa, * to, ni zan yi shuru ne?

    Kā shirya makirce-makirce, * ni ma kamarka ne?

    Zan tuhume ku, in gabatad da ƙara * a gaban idanunka.

Ku yi tunani kan wannan, ku da ke mance wa Allah, * kada in cafke ku, ba mai ƙwacewa.

Duk wanda ya miƙa hadayar yabo, * zan gayyace shi biki.

Wanda ya tsaya a kan hanyata, * zan shanyad da shi sosai da ceton Allah.

Zabura ta 51

Ka ji tausayina, ya Allah, * saboda ƙaunarka.

Saboda yawan rahamarka, * ka shafe tawayena.

Zubo ruwa, ka wanke ni daga muguntata, * ka tsarkake ni daga zunubaina.

    Sharrin ƙeta da ke tuhumata na san shi, * zunubina gabana yake kullun.

    Kai kaɗai ne na yi wa laifi, * na yi zunubin nan a idanunka.

         To, ka yi daidai a shariar da ka yanke, * hukuncin da kakan yi ba shi da aibu.

    I, da laifi aka ɗauki cikina, * ni mai zunubi ne tun haifuwata.

    I, ka fi son gaskiya * fiye da sanin boka da wayon wulli, * ka koya mani hikima.

         Ka raba ni da zunubi, * zan kuma tsarkaka fiye da ruwan ƙalƙashin dutse, * ka wanke ni, zan fi auduga fari.

         Bari in ji farinciki da murna, * bari ƙasusuwan da aka rumurmutse su farfaɗo.

              Ka kau da fuskarka daga zunubaina, * ka shafe dukan ƙetata.

                   Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, * ka sa mani sabon ruhu na biyayya.

              Kada ka kore ni daga gabanka, * ko ka ƙwace mani Ruhunka Mai Tsarki.

         Ka mayar mani da farinciki na cetonka, * ka ƙarfafa ni da ruhun biyayya,

         domin in koya wa masu tawaye hanyoyinka, * masu zunubi kuma za su juyo gare ka.

    Ka cece ni daga ƙwallan mutuwa, * ya Allah, Allahna.

    Sannan ne, Macecina, * halshena zai raira yabon alherinka da ƙarfi.

         Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, * halshena kuma zai furta yabonka.

    Da ka so hadaya, * da na miƙa, * da ka yi marmarin hadaya ta ƙonawa, da na bayas.

    Hadaya mafi kyau, ita ce ruhu na ƙasƙanci, * ƙasƙantaciyyar zuciya, ya Allah, ba za ka yas ba.

Ka sabunta kyan Sihiyona da alherinka, * ka sake ginin ganuwar Urushalima.

Sannan ne za ka karɓi hadayun da ke daidai, * ƙonannun hadayu, * har yan marƙa za su hau bagadinka.

Zabura ta 52

Don me kake alfari da ƙeta, kai gawurtaccen mutun? * Mai bautar Allah, me ya sa ka ke tunanin fitina kullun?

    Halshenka kamar kakkaifar aska yake, * ya kai gwanin yaudara.

    Ka fi son mugunta da nagarta, * da ƙarya maimakon faɗin gaskiya.

    Kana ƙaunar dukan batutuwa * da halshenka mai yaudara ke yi.

         Allah ya hana ka haifuwa har abada, * ya rushe ka da tsawa!

         Ya koro ka daga alfarwarka, * ya janye rayukan yayanka daga duniya.

              Masu gaskiya za su duba da tsoro, * amma daga baya za su yi masa dariya, su ce:

         Ga mutumin nan * da bai mai da Allah mafakarsa ba,

         amma ya dogara ga yawan wadatarsa, * ya dogara ga mugun abunsa.

    Ni dai, kamar itacen zaitun ne, * da ke girma a cikin gidan Allah,

    na dogara ga ƙauna * ta Madauwamin Allah.

Ina yabonka, ya Madauwami, * domin ka aikata.

Zan yabi sunanka * mai daɗi gun masu bauta maka.

Zabura ta 53

Wawa yana tunani a zuciyarsa, * cewa, Allah baya nan.

Masu hainci ne, suna yin miyagun abubuwa, * babu wani mai aikata alheri.

    Daga sama Allah yana dubo * dukan yanadan,

    ya gani ko akwai masu hikima, * da ke neman Allah.

         Amma dukansu sun bauɗe, * duk miyagu ne.

         Babu mai yin kirki a cikinsu, * ko mutun ɗaya.

         Masu aikata aibu ba su sani ba, * in sun washe jamaarsa,

         suna cin hatsin Allah, * wanda ba su yi girbi ba?

    Ga yadda suka yi ƙungiya ta sojinsu, * amma hari bai daɗe ba,

    domin Allah ya yi kaca-kaca * da ƙasusuwan masu kai maku hari.

    Kun karai * sai da Allah ya tara gawarwakinsu.

Daga Sihiyona wa zai kawo wa Israila ceto? * Lokacin da Allah ya sake arzuta jamaarsa,

bari yayan Yakubu su yi farinciki, * yayan Israila su yi murna.

Zabura ta 54

Ya Allah, ka cece ni da sunanka, * ta ikonka kuma ka kāre ni.

    Ya Allah, ka ji adduata, * ka kasa kunne ga kalmomin bakina,

         domin baƙi sun tasam mani, * yan iska suna neman raina, * ba su san Allah shugabana ba ne.

              Dubi yadda Allah ya zama mataimakina, * Ubangiji Matallafin raina.

         Ya saka wa masu ɓata mani suna da muguntarsu, * da amincinsa ya hallaka su.

    Saboda darajarka zan yi maka hadaya, * Yahweh, zan yabi sunanka mafificin kyau.

Gama ya tserad da ni daga dukan maƙiyana, * idanuna sun ga yadda ya yi nasara da magabtana.

Zabura ta 55

Ya Allah, ka ji adduata, * kada ka zama kurma ga roƙona.

Ka karkato gare ni, ka amsa mani, * ka sauko inda ni ke ƙara.

    Na gigice da muryar abokin gaba, * da hararar miyagu,

    domin suna tila mani zage, * suna ci mani fuska.

         Zuciyata tana raɗaɗi a cikina, * razanar mutuwa tana girgiza ni.

         Tsoro da fargaba sun afka mani, * sai makyarkyata nike yi.

              Sai na ce, Wa zai ba ni fukafukai kamar na kuruciya, * don in tashi fir in huta.

              Da sai in tafi nesa, * in sauka a kungarmin daji.

              Zan hanzarta zuwa mafakata, * daga iska mai ƙarfi da hadari.

                   Ya Ubangiji, ka hallaka halshensu mai rinto, * domin na ga tashin hankali da hargitsi a cikin birnin.

                   Dare da rana suna kewaye da shi. * A kan garunsa akwai ƙeta da fitina.

                   Daga tsakkiyarsa ayyukan mugunta suna fitowa, * daga tsakkiyarsa ba su dena zuwa ba, * daga dandalinsa zalunci da zamɓa suna watsuwa.

                       Ba magabci ba ne * wanda ya yi mani cin fuskar da nike jurewa.

                       Ba maƙiyi ba ne ya ɓata mani suna, * balle in ɓuya daga gare shi.

                            Amma kai ne, aminina, * abokina da na amince da shi.

                            Mun saba yin shirin zaune tare * a cikin Gidan Allah, * inda muke cudanya da taron jamaa.

                       Bari mutuwa ta afko masu, * bari su gangara Shawol da ransu,

                       domin magana mai dafi na fitowa * daga maƙogwaronsu da ƙirjinsu.

                   Amma na yi kira ga Allah, * Yahweh kuwa ya cece ni.

                   Da yamma, da safe, da rana tsaka * ina kai ƙara da nishi.

              Mafanshi kuwa ya ji muryata, * yana biyan kuɗin raina.

              Ya matso kusa da ni * lokacin da masu yawa suke gāba da ni.

              Allah ya ji ni, * Mai Zamanu ya ba ni amsa, * domin ba canzawa a gare shi.

         Duk da haka, basu da tsoron Allah. * Wancan mutun ya sa hannu kan amininsa, * ya saɓa yarjejeniyarsa.

         Maganarsa ta fi kitse taushi, * amma zuciyarsa tana cike da ƙiyayya.

         Kalmominsa sun fi mai sulɓi, * amma a gaskiya sun fi takobi kaifi.

    Yahweh Maɗaukaki ne Mai Arzutaka, * Mai Ba ka wanda ke tallafa maka.

    Har abada ba zai bar * mai gaskiya ya yi tuntuɓe ba.

Amma kai, ya Allah, za ka kai su, * Rami mai Caɓi.

Kada masu gumaki da tsafi * su rayu rabin kwanakinsu. * Amma ni, na dogara gare ka.

Zabura ta 56

Ka ji tausayina, ya Allah, * gama mutane suna musguna mani!

Wuni zubut * suna tozarta ni da muƙamuƙansu.

Masu yankena suna wahalda ni wuni zubut, * mutane barkatai ne ke yaƙi da ni.

    Ya Maɗaukaki, in na firgita, * ina dogara gare ka.

Da Allah nike taƙamai, kai mai yanke! * Na dogara ga Allah.

Bana jin tsoro. * Me mutun zai iya yi mani?

    Wuni zubut masu yankena suna harzuka ni, * suna mugun shiri a kaina kullun.

    Suna shawara da juna da mugun nufi a asirce, * dubi yadda masu kushena ke kallo, * kamar tarkon ƙafa suke neman raina.

        Ka cece mu daga ƙetarsu, * cikin hushinka ka tsawata wa alummai, ya Allah!

        Ka rubuta makokina kai da kanka, * ka lissafta hawayena a kan takardarka, * da gajiyata a ckikin kundinka.

    Da magabtana sun juya, * sun yi dabur-dabur da na yi kira,

    sannan nike sani, * lalle Allah yana goyon bayana.

Da Allah ne nike taƙama, kai mai yanke! * Da Yahweh nike taƙama, kai mai yanke!

Na dogara ga Allah. * Bana jin tsoro. * Menene mutun zai iya yi mani?

    Hakika, ya Allah Maɗaukaki, * zan biya waadodina * tare da yabbanka.

Sai ka cece ni daga Mutuwa, * ka hana ƙafafuna zuwa cikin Kora,

domin in yi tafiya a gaban Allah * a cikin aljannar rayuwa.

Zabura ta 57

Ka tausaya mani, ya Allah, ka tausaya mani, * domin a gare ka nike fakewa.

A innuwar fukafukanka nike fakewa, * har balain nan ya wuce.

    Ina kira ga Allah Maɗaukaki, * ga Allah, Sarkin Sakayya.

    Zai aiko daga sama a cece ni, * daga cin mutuncin masu tozarta ni.

    Allah zai aiko * da alherinsa da amincinsa.

        Ina kwance a tsakkiyar zakoki, * ga shi, suna marmarin naman yanadan.

        Haƙoransu masu ne da kibau, * harsunansu takubba ne masu shegen kaifi.

            Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ɗaukakarka ta rufe dukan duniya.

        Sun haƙa wa ƙafafuna tarko, * da igiya don su zarge wuyana.

        Sun gina rami don in fāda ciki da kā, * da ma su yi kundumbala a ciki.

    Na shirya zuciyata, ya Allah, * na shirya zuciyata, * zan yi waƙa in yabe ka.

    Ki farka, zuciyata! * Ku farka, molona da garayata! * Sai in farkad da asuba!

Zan gode maka a cikin jamaa, ya Ubangiji, * zan yabe ka a cikin alummai, ya Mai Duka.

Domin alherinka ya kere sammai, * amincinka kuma ya zarce sararin sama.

Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ɗaukakarka ta rufe dukan duniya.

Zabura ta 58

Ya ku mashawarta, ku alkalai, ku zartad da hukuncin adalci, * ku yi mulkin yanadan da gaskiya.

Amma ba haka ba, kuna aikata ƙeta a zukatanku, * da zalunci kuke yanke sharia ta son ranku.

    Miyagu abin ƙyama ne tun daga ɗaukar cikinsu, * tun daga haifuwa maƙaryata ke bauɗewa.

    Dafinsu kamar na maciji ne, * suna yin kama da kububuwa mai tosasshen kunne,

    wadda ba ta jin muryar gardawa, * ko ta gwanayen tsibbu.

        Ya Allah, ka zub da haƙoransu daga bakunansu, * Yahweh, ka kakkarya fiƙoƙin kuyakuyan zakoki.

        Bari su zube, kamar ruwa mai gudu, * su ɗana kibansu ba tare da ƙarfin harbi ba.

    Kamar wanda ciwon ƙanjamau ya takure, bari ya ƙaura * kamar ɓarin mace, kada su ga hasken rana.

    Kafin su yi laakari da hadarinka, * bari zafin haushinka ya watsad da su.

Mai adalci zai yi murna in ya ga nasararsa, * zai wanke ƙafafunsa daga jinin miyagu.

Mutane za su ce, Zama mai adalci abin kirki ne. * Hakika akwai Allah mai sharaanta duniya!

Zabura ta 59

Ka cece ni daga abokan gabata, ya Allah, * a game da masu tasar mani ka zama ganuwata!

Ka cece ni daga masu aikata mugunta, * daga masu gumaka ka fanshe ni.

    Dubi yadda suke fakon raina, * masu iko suna yi mani maƙarƙashiya.

    Ba don laifina ba, * ba don zunubina ba, Yahweh,

    ba don kurena ba, * sun sha mani da-ga.

Tashi, ka bi ni, * ka gani da kanka,

Yahweh, Allah mai runduna, * Allah na Israila.

Farka domin ka hori dukan alummai, * kada ka ji tausayin miyagun masu hainci.

    Sukan dakata sai maraice, * kāna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.

    Duba daga bakunansu da leɓunansu suna aman takubba. * Suna cewa, Wanene zai saurare mu?

        Amma, Yahweh, za ka yi masu dariya, * kana mai da dukan alummai abin wasa.

            Allahna mafakata ne, * hakika ina samun kariya.

            Allah, shi ne ganuwata, * hakika Allah ne katangata.

            Allah zai riga ni zuwa, * zai sa in yi wa magabtana dariya.

                 Ya Allah, ka kashe su, * kada mutanena su razana.

                 Ka runtume su daga mafakarka, * ka yā da su ƙasa, * ya Ubangiji Shugabanmu.

            Bari a kama su ta zunubin bakinsu * da gulmar leɓunansu.

            Saboda izgilancinsu, zage-zage da ƙarairayinsu, * bari a shafe su.

            Ka hallaka su da hushinka, * ka hallaka, ka shafe su,

        domin su sani Allah ne * yake mulki daga ƙasar Yakubu * har zuwa bangon duniya.

    Sukan dakata sai maraice, * kāna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.

    Da haushi sukan nemi rabonsu, * in ba su ƙoshi ba, sai su ci gaba.

Zan yi waƙar ikonka, * kowace safiya zan yabi ƙarfinka,

    domin kā zama ganuwata, * da katangata lokacin hari.

    Allah mafakata ne, * hakika yana tsare ni.

Allah shi ne ganuwata, * Allah ne katangata.

Zabura ta 60

Ya Allah, ka ji hushi da mu, ka guje mu. * Kā yi haushi, ka juya mana baya.

    Kā girgiza ƙasar, ta kuwa rugurguje.* Raunanniya daga targaɗenta, * ta gigice sosai.

        Kā sa jamaarka su shanye ƙoƙon, * kā sa mun sha abinshan inabi da ya bugar da mu.

            Ka ba masu tsoronka tuta, * inda za su iya gāba da masu baka.

            Domin ka kuɓutad da ƙaunatattunka, * da hannun damanka sa mu yi rinjaye, mu ci nasara.

                 Allah ya yi magana daga tsattsarkan gidansa, ya ce: * Ku ji, zan raba Shekem, * in auna kwarin Sukkot.

                 Gileyad nawa ne, har da Manassa, * Ifraimu hulata ne, * Yahuda kuma sandata ce ta sarauta.

                 Mowab bangajin wankina ne, * a kan Edom zan taka da takalmina, * a kan Filistiya zan yi ihun nasara.

            Wa zai kai ni Birnin Dutse? * Wa zai ba ni gadon Edom?

        Amma kai, ya Allah, za ka yi hushi da mu? * ba za ka ƙara fita da sojojinmu ba?

    Ka ba mu yanci daga abokan gaba, * tun da yake taimakon mutane banza ne.

Da ikon Allah za mu yi nasara, * shi kansa ne zai tattake magabtanmu.

Zabura ta 61

Ya Allah, ka ji kukana, * ka saurari adduata.

    Daga bakin Ƙalƙashin Ƙasa * na yi kiranka, * lokacin da zuciyata ta karaya.

    Ka jawo ni daga bakin Ramin * zuwa Dogon Dutse.

    I, zama mafakata, * hasumiyar tsaro daga Magabcina.

        Bari in zauna a madauwamiyar alfarwarka, * in sami tsira a innuwar fukafukanka.

    Ya Allah, ka ji waadonina, * ka biya begen mai tsoron sunanka.

    Ka ƙara shekaru ga shekarun sarki, * shekarunsa su zama tsararraki barkatai.

    Bari ya zauna kan kursiyinsa a gaban Allah har abada, * ka sa alheri da aminci su kiyaye shi.

Sannan zan yi waƙar sunanka har abada, * ina cika waadodina kowace rana.

Zabura ta 62

Allah mai alloli, * shi kaɗai ne mafakata. * Ya raina, daga gare shi ne cetona zai zo.

Shi kaɗai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan fāda a Tarun ba.

    Don me za ku dinga maganar banza, * kuna ta yin tsegumi a kan mutun?

    Dukanku kama da bango mai son fāɗi, * ko dangar da ta kishingiɗa.

    Yauɗara ce kawai suka runguma, * suna jin daɗin ƙarairayi.

    I, da baka suna sa albarka, * amma a zuci suna yi maka laana.

Allah kaɗai ne mafakata,* ya raina, daga gareshi ne nike samun bege.

Shi kaɗai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan yi tuntuɓe ba.

            Allah Maɗaukaki ne nasarata, * Mai Ɗaukaka shi ne mafakata, * Allah shi ne masterata.

            Ku dogara gare shi, Mai Iko ne kullun, * ku buɗe zukatanku gare shi, * domin Allah ne matseranmu.

Talakawa kamkar hayaƙi suke, * manyan mutane kuma kamar tururi.

A kan sikelai ba su yi nauyin ganyaye ba, * dukansu biyu kuma ba su kai nauyin iska ba.

    Kada ku cika rungumar zulunci, * kada ku mai da dukiya gunkinku.

    In Allah ya yi magana, * ku saurara.

    Abu ɗaya ne Allah ya faɗi, * biyu kaɗai ne na ji:

Iko na Allah ne, * a gare ka kuma, ya Ubangiji, ƙauna take.

Domin kana saka wa kowane mutun * gwargwadon aikinsa.

Zabura ta 63

Ya Allah, Allahna, * kai ne nike marmari.

    Raina yana jin ƙishinka, * jikina na begenka,

        fiye da yadda busasshiyar ƙasa * ke marmarin ruwa.

            A tsattsarkan mabautarka bari in zuba ido gare ka, * ina kallon ikonka da ɗaukakarka.

        Domin ƙaunarka tana da daɗi * fiye da rayuwata da leɓunana da ke yabonka.

    A madauwamiyar rayuwata ka sa in yabe ka, * a samaniyarka kuma in ɗaga hannuwana zuwa gare ka.

        A can zan yi biki, in ƙoshi * da madara da man shanu.

        Leɓunana za su yi sowa ta murna, * bakina kuma zai raira yabonka.

    A kan gadona ina tunawa da kai, * dukan dare ina tunaninka.

        Ka zama Mataimakina! * Bari in ɓuya a cikin innuwar fukafukanka.

            Bari in manne maka, * hannunka na dama kuwa ya ɗaga ni.

        Amma masu neman kisana, * bari su tafi can ƙurewar Ƙalƙashin Ƙasa.

    Bari su gamu da kaifin takobinsa, * duk su zama kalacin kyarketai.

Sarki zai yi murna da Allah. * Duk wanda ya rantse da shi zai gama lafiya, * amma za a toshe bakin maƙaryata.

Zabura ta 64

Ka ji muryata, ya Allah, da nike roƙo.

Ka kiyaye raina daga taron maƙiya, * ka ɓoye ni daga miyagun mashawarta, * daga rukunin yan iska,

    masu wasa halshensu kamar takobi, * suna bārā da maganarsu mai dafi kamar kibiya,

    don su yi wa mara laifi kwanton ɓauna, * su hallaka shi kwatsam, ba tsoron Allah.

        Suna shirya masa magani mai dafi, * suna kakkafa masa tarkuna,

            suna cewa: Wanene ke ganinmu? * Wa zai binciki daidaitaccen sharrinmu?

            Amma Mai Bincike zai binciki * can cikin cikin mutun * har cikin birnin zuciya.

        Ɗaukaka ga Allah Mai Kibau! * Ka ninka raunukansu!

    Maɗaukaki zai sa matsegunta su yi tuntuɓe, * dukan masu girman kai za su ƙasƙanta.

    Kowane mutun zai ji tsoro, * ya bayyana aikin Allah, * ya riƙa tunanin aikinsa.

Bari mai adalci ya yi murna da Yahweh, * ya nemi tsira a gunsa! * Bari dukan masu zuciyar kirki su more!

Zabura ta 65

Yabo gare ka a mafakarka ta samaniya, * da can Sihiyona, ya Allah.

    A gun ka za a cika waadodi, * domin ka kan ji adduoi.

        A gare ka duk biladama * zai kai miyagun ayyukansa.

            Ayyukanmu na tawaye sun yi yawa, * ka gafarta mana!

            Mai albarka ne wanda ka zaɓa zuwa kusa da kai, * don ya zauna a majalisarka.

        Bari mu gamsu da kyan gidanka, * da tsarkin Haikalinka.

    Lokacin sharia ka nuna mana alajibanka, * ya Allahnmu mai nasara!

        Kā shimfiɗa dukan kusurwoyin duniya, * da na nesan teku.

            Kā kakkafa duwatsu da ikonka, * sun yi ɗamara da ƙarfinka.

            Kā kwantada da haukan teku, * da haukan raƙuman ruwansa, * da kuma tarzomar mutane.

        Mazaunan bangon duniya sun ji tsoro * saboda alajibanka.

    Ka sa gamzaki da tauraron dare * su yi sowar murna.

        Ka ziyarci ƙasa, * ka sa ta tsalle don murna, * ka sa ta yi albarku da ruwan samanka.

            Ka cika magudadar sama da ruwa, * ka wadaci ƙasa da hatsi, * gama kā kafa ta don wannan.

                Ka malalo ruwa a kwarin gona, * ka jiƙa kunyoyinta.

                Ka tausasa ta da ruwa mai yawa, * ka albarkaci hatsinta!

            Ka albarkaci tuddai da ruwan samanka, * makiyayunka sun ba da mai.

        Dajin Allah ya tsatso da mai, * ka lulluɓi tuddai da murna.

    Ka sa kwaruruwa su cika da dabbobi * ƙasar kwari kuwa alkama.

Bari su ta da murya, * su yi sowar farinciki.

Zabura ta 66

Yi sowar farinciki ga Allah, ke duniya duka, * yi waƙar ɗaukaka sunansa, * yi shelar ɗaukaka yabonsa.

A ce, Ya Allah, * mai ban tsoro ne kai ta ayyukanka!

    Saboda girman ikonka, * magabtanka suna sunkuyawa don tsoro a gabanka.

    Dukan duniya tana bauta maka, * tana yi maka waƙa, waƙar sunanka.

        Ku zo, ku ga ayyukan Allah, * mai firgita yanadan ta ayyukansa.

            Ya mai da teku busasshiyar ƙasa, * suka taka ƙasar kogin suka haye. * Ku zo, mu yi farinciki a cikinsa!

        Yana sarauta daga madauwamiyar mafakarsa, * idanunsa na kallon alummai, * don kada yan tawaye su tayar masa.

    Ku yabi Allahnmu, ya ku mutane, * da murya mai ƙarfi ku yabe shi!

    Wanda ya lissafa mu a cikin rayayyu, * bai ma sa ƙafafuna cikin Lema ba.

        Amma kā gwada mu, ya Allah, * kā jarraba mu kamar yadda ake tace azurfa.

        Kā kai mu cikin hamada, * kā sa marurai a gindinmu.

        Kā sa ciwo ya hau kanmu, * mun ratsa wuta da ruwa, * bayan ka fishe mu daga wurin wadata.

    Zan shiga gidanka da ƙonannun hadayuna, * in cika waadodina,

    waɗanda na faɗa da leɓunana, * bakina ya furta a lokacin wahala.

    Zan miƙa maka dabbobi masu kiɓa don a ƙona, * da ƙamshin raguna da aka ƙona. * Zan shirya bajimai duk da awaki.

        Ku zo, ku ji, dukanku masu tsoron Allah, * zan gaya maku abin da ya yi mani.

        Da bakina na yi kuka gare shi, * muryaoyin waƙa kuma suna kan halshena.

    Da na tabbata mugunta a zuciyata, * da Ubangiji bai ji ni ba.

    Amma Allah ya ji ni, * ya saurari muryar adduata.

Albarka ga Allah! * domin bai ƙi adduata ba, * zan sake faɗin alherinsa har sau ɗari.

Zabura ta 67

Allah ya ji tausayinmu, ya yi mana albarka, * ya zo mana da hasken fuskarsa.

In an san sarautarka a duniya, * da nasararka a cikin dukan alummai,

    mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.

        Alummai za su yi farinciki da sowar murna, * domin kai ne sarki.

        Za ka kai alummai Sararin, * jamaa kuma cikin Ƙasar.

    Mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.

Bari ƙasa ta ba da amfaninta, * Allah, Allahnmu, ya yi mana albarka.

Allah ya yi mana albarka, * dukan ƙasashe su ji tsoronsa * har bangon duniya.

Zabura ta 68

In Allah ya tashi, * magabtansa sukan watsu, * maƙiyansa sukan guje shi.

Kamar yadda hayaƙi ke bin iska, su ɓace, * kamar yadda danƙo ke narkewa a gaban wuta.

A gaban Allah * miyagu sukan san inda dare ya yi masu.

    Amma masu gaskiya za su yi murna, * su sami tagomashi a gaban Allah, * za su yi waƙa mai farinciki.

        Ku yi waƙa, ku alloli, * ku raira yabo, ku sammansa, * ku share hanya ga Mai Hawan Giza-gizai.

    Ku ji yi murna da Yahweh, * ku yi murna a gabansa!

Allah daga tsattsarkan mazauninsa * shi ne uban marayu da mai kare gwauraye.

Allah wanda ya ba mai kaɗaici gida, * shi ya yanto yan sarƙa tare da waƙa

Amma masu taurin kai, * an binne su a Hamada.

    Ya Allah, saad da ka fita * gaban mutanenka, * da ka ƙetare hamada,

    sai ƙasa ta raunana, * sammai kuma suka saukad da ruwa

        da ganin Allah, * Mai Sinina,

        da ganin Allah, * Allah na Israila.

            Ya Allah, ka aiko da ruwan samanka mai yawa, * ƙasarka da sarautarka, ka tabbatad da su.

            Ka wadaci jamaarka da ke zaune a kai, * da ruwan samanka ka arzuta mazaunanta, ya Allah.

                 Allah ya aike da magana, * mai faranta rundunar taurari.

                 Sarakunan rundunarsu su sauko da ruwa, * wurin kiwon kasar ya sami rabonsa na albarka.

                 Bari su zube * a tsakar garken tumaki

            An dalaye fukafukan kuruciya da azurfa, * da gashinta kuma da zinariya.

            Saad da Shaddai ya inuwantad da sarakuna, * dusar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmona.

        Ya babban dutse, Dutsen Bashan, * ya dutse mai yawan tulluwa, Dutsen Bashan,

        don me kake kallo da hassada, * ya dutse mai yawan tulluwa,

        dutsen da Allah ya zaɓa don mazauninsa, * inda Yahweh zai zauna har abada.

    Karusan Allah dubu ishirin ne, * maharban Ubangiji dubbai ne, * wanda ya kafa Sinina mabautarsa.

    Kā hau sama, * kā jawo kamammu.

    Kā karɓi kyautai daga hannuwansu, * amma Yahweh Allah ya binne masu taurin kai.

    Albarka ga Ubangiji yau da kullun, * Allah kansa, Macecinmu, ya cire mana nauyin kayanmu.

    Allah kansa shi ne Allah na cetona, * tun da Ubangiji Yahweh ya sa mu tsira daga mutuwa.

    I, Allah ya buge kan magabtansa, * ya farfashe kwakwalunsu, * saad da ya fito daga sammansa.

        Allah ya ce, Na taushe Macijin, * na kwantad da Teku Mai zurfi.

        Haka, ƙafarka ta ragargaji gaɓoɓinsu, * harsunan karnukanka kuma sun sami rabo gun magabtanka.

            Ku ga faratin Allah, * faratin Allahna, * Sarkina daga mabautarsa.

            Mawaƙa suna kan gaba, * mabusa a baya, * a tsakiya yan mata suna kiɗa.

                 A taruwar jamaa ku yabi Allah, * Yahweh kuwa a taron Israila.

            Ga Biliyaminu ƙarami, yana yi masu jagora, * sarakunan Yahuda kuma a jeri biyu,

            sarakunan Zabaluna, * da sarakunan Naftali.

        Ya Allah, ka aiko mana da ƙarfinka, * ƙarfi, ya Allah, abin da ka gina domin mu.

        Haikalinka, ya Maɗaukaki, a Ƙudus yake, * sarakuna za su kawo maka kyautai.

    Ka tsawata wa dabbar lema, * taron bajimai da maruƙansu.

    waɗanda ke tattaka mutane saboda shaawar azurfa, * suna warwatsa mutane don marmarin yaƙi,

Bari attajiran Masar su kawo shuɗin zane, * Habasha ta rugo ta kawo kayanta ga Allah.

Ku sarakunan duniya, ku yi waƙa, * ku alloli, ku raira yabbai ga Ubangiji.

    Ku dubi Mai Hawa sammansa, * sammai na tun filazal.

    Ku saurara, yana aiko muryarsa, * murya mai girma!

Ku girmama Allah, * Maɗaukakin Israila.

Ɗaukakarsa da ikonsa * sun fi ƙarfin sama. * Allah mai bantsoro ne a tsattsarkan mabautarsa.

Hakika shi Allah ne na Israila, * wanda ke ba da nasara da iko. * Ku mutane, ku yabi Allah!

Zabura ta 69

Ka cece ni, Allah, * domin ruwa ya kai wuyana.

    Na nutse cikin Taɓo mai zurfi, * inda ba damar tsayawa.

        Na shiga zuzzurfan ruwa, * inda igiyoyin ruwa suke cina.

    Na gaji da kuka, * maƙogwarona ya bushe.

Idanuna sun fara dushewa, * saad da nike dako, ya Allah.

    Magabtana masu makirci sun yi yawa, * fiye da gashin kaina.

    Fiye da gashin kaina * mayaudarana suka zarce da yawa.

    Abin da ban sata ba, * dole ne in mayas da shi?

        Ya Allah, ka san barancina, * laifofina ma ba a ɓoye suke gare ka ba.

            Kada masu sa zuciya gare ka su sha kunya * saboda ni, ya Ubangiji Yahweh Mai Runduna.

                 Kada masu nemanka su kunyata * saboda ni, ya Allah na Israila.

                 Saboda kai ne na sha zagi, * cin mutunci ya rufe fuskata.

            Na zama baƙo ga yanuwana, * bare kuma ga yayan da muke uwa ɗaya.

        Gama kishi domin gidanka ya cinye ni, * zage-zagen masu zaginka sun taru a kaina.

    Ina tunanin dukan ɓacin raina a cikin azumina, * wulakanci kuma ya zama rabona.

    Na mai da tsummoki tufafina, * na zame masu abin dariya.

    Har yan bikin da mashaya * suna wallafa waƙoƙin shegantaka a kaina.

        Amma ni kam, adduata gare ka take, Yahweh, * ya Allah, ka nuna mani alherinka yanzu.

        Da ƙaunarka mai girma * ka amsa mani * da amintaccen taimakonka.

            Ka cece ni daga Caɓin, * kada in nutse.

            Bari a kuɓutad da ni daga Maƙiyi, * daga zurfafan ruwaye ma.

            Kada juyewar ruwan teku ta rufe ni, * ko zurfinsa ya haɗiye ni, * ko Ramin ya rufe bakinsa a kaina.

                 Ka amsa mani, Yahweh, * domin ƙaunarka mai girma ce.

                      Bisa ga yawan rahamarka, * ka juyo fuskarka gare ni.

                           Kada ka juya * wa bawanka baya.

                      Ka amsa mani da sauri, * don wahalar da ke damuna,

                 Ka kusato ni, ya Allah, ka cece ni, * ka fanshe ni daga Mazaunin Magabcina.

            Ka san wulakancin da ake yi mani, * kunyata da ƙasƙancina a gabanka suke.

            Wulakanci ya lalata kayan cikina, * ciwo ya dagargaji zuciyata.

        Na nemi mai jin tausayi, amma babu, * da mai sanyaya zuciya, amma ban sami wani ba.

        Sun sa dafi a abincina, * don ƙishinruwana sun miƙa mani ruwan tsami.

    Bari teburin abincin da ke gabansu ya zama tarko gare su, * abokan tarayyarsu kuma su zaman masu taru.

    Idanunsu su dushe don kada su gani, * cinyansu kuma su yi ta rawa kullun.

    Ka jibga masu haushinka, * bari tsananin hushinka ya cim masu.

        A sansaninsu kada wani ya ragu, * a tantunansu kada wani ya zauna.

            Domin wanda ka buge sun tsananta masa, * azabar wanda ka raunata kuwa suna ta tsegumi a kai.

            Ka hukunta su da sharri bisa sharri, * kada su shiga aljannarka.

        Bari a share sunayensu daga littafin rai, * kada a sa a cikin adalai.

    Amma ni gajiyayye ne, cikin azaba, * taimakon Allah ya tallafe ni,

    don in yabi sunan Allah da waƙa, * in ɗaukaka shi da godiya.

    Wannan zai daɗaɗa ran Yahweh fiye da takarkari, * ko fiye da bajimin sa mai ƙahoni da kofatai.

Ku duba, ku gajiyayyu, * bari masu neman Allah su yi farinciki, * zukatansu su tofu!

    Domin Allah yana sauraren mabukata, * Yahweh baya ya da waɗanda ke nasa.

        Bari sama da ƙasa su yabe shi, * tekuna da dukan abin da ke motsi a cikinsu.

    Hakika, Allah zai ceci Sihiyona, * zai sake ginin garuruwan Yahuda, * waɗanda aka kora za su koma su zauna ciki.

Jikokin bayinsa za su gaji birnin, * za su zauna ciki, su mallake shi.

Zabura ta 70

Ya Allah, ka cece ni, * Yahweh, ka yi hanzari ka taimake ni!

    Bari masu neman raina * su kunyata, su ruɗe.

        Bari masu shaawar lalacewata * ƙasƙanci ya zama nasu.

            Ƙaiƙai ya koma wa masu tseguman banza, * waɗanda ke ce mani, Ga shegen nan, ga shegen nan!

            Bari dukan masu nemanka * su yi farinciki, su yi murna da kai!

        Bari dukan masu son cetonka * su riƙa cewa: Allahu akbar!

    Amma ni, da ke gajiyayye da mabukaci, * ya Allah, ka hanzarto zuwa gare ni.

Kai ne mataimakina da macecina, * Yahweh, kada ka yi jinkiri.

Zabura ta 71

Yahweh, a gare ka nike dogara, * kada in kunyata, ya Madauwami!

    Da amincinka ka kuɓutad da ni, ka fanshe ni, * ka kasa kunne gare ni, ka cece ni.

        Dutsen Taimako, ka zama nawa! * Kā alkawalta zuwa guna a kowane lokaci.

        Ka cece ni yanzu! * gama kai ne dutsena da mafakata.

    Ya Allah, ka yanta ni daga hannun mugu, * daga kagen azzalumi da ɗan fashi.

        Gama kai ne begena, ya Ubangiji, * Yahweh, madogarata ne tun a cikin kuruciyata.

        Kai ne ka tallafa mani tun daga mahaifa, * daga cikin uwata kai ka lura da ni, * zan dinga yabonka.

            Na zama zakaran gwajin dafi ga maharɓa, * amma kai ne ƙaƙƙarfar mafakata.

        Bakina ya cika da yabonka, * da na alajibanka yini zubut.

        Kada ka watsad da ni da tsufana, * in ƙarfina ya gaza, kada ka yashe ni.

            Magabtana suna hararata, * masu neman raina suna ƙulla shawara da juna,

            suna cewa: Allah ya yashe shi, * mu fafare shi, mu kama shi, * domin babu mai ceto.

                 Ya Allahna, kada ka yi nesa da ni, * ya Allahna, ka hanzarta taimakona.

            Bari matseguntana * su sha kunya tuli.

            Masu neman lalacewata * su kwashi muzanci da kunya.

                 Amma ni a kullun zan sa zuciya gare ka, * in dinga yabonka ba fashi.

                 Bakina zai lissafta ayyukanka masu aminci, * wuni zubut kuma dukan aikinka na ceto, * duk da ba zan iya lissafa su ba.

            Zan shiga babban gidanka, ya Ubangiji, * Yahweh, amincinka kaɗai zan yi shela.

                 Ya Allah, kā hore ni tun daga ƙuruciyata, * har yanzu ma ina ba da labarin alajibanka.

                 Har cikin tsufana da furfura, * kada ka yashe ni, ya Allah,

            sai na ba jamaa labarin ikonka, * ga duk wanda zai shiga ƙaton gidanka.

            Ya Allah, amincinka ya kai har sama, * domin ka aikata manyan abubuwa. * ya Allah, wa ke kama da kai?

            Ko da yake ka nuna mani * wahalu masu yawa da husumai da cuta,

            za ka sake raya ni, * daga zurfafan Ƙalƙashin Ƙasa kuma * za ka sake ta da ni.

        Ka ji daɗin babban baikona na shanu, * ka ma lulluɓe ni da tausayinka.

    Da babbar murya zan yabe ka da garaya, * in yabi amincinka, ya Allah.

        Zan yabe ka da molo, * ya Mai Tsarkin nan na Israila.

        Leɓunana za su yi waƙa, * i, zan yabe ka, * duk da ruhuna da ka fanso.

    Da babbar murya halshena zai lissafta * ayyukanka masu aminci yini zubut.

Ka sa su sha kunya, * duk masu marmarin lalacewata, * ka sa su ruɗe.

Zabura ta 72

Ya Allah, ka ba sarki hikimar yanke hukuncinka, * ɗan sarki kuma ya san gaskiya,

    don ya hukunta mutanenka da gaskiya, * zaluntattu kuma da adalci.

        Bari duwasu su kawo wa mutanenka salama, * tuddai kuma adalci.

    Bari ya kare waɗanda aka zalunta * ya ceci yayan mabukata, * ya dami azzalumi.

Ka sa ya girmama ka muddin daɗewar rana, * har wanzuwar wata, * zuwa zamanin zamanu.

    Bari ya sauko kamar ruwan sama a kan ciyawa, * tamkar yayyafi a kan busasshiyar ƙasa.

    Bari adali ya bunƙasa a zamaninsa, * salama kuma ta kasance muddun wata na wanzuwa.

        Bari ya yi mulki daga teku zuwa teku, * daga Kogin Yufiretis har zuwa ƙarshen duniya.

        Bari kabilun hamada su durƙusa masa, * har sai magabtansa sun ci turɓaya.

            Sarakunan Tarshishi da na tsibirai * su kakkawo masa haraji.

                 Sarakunan Shiba da na Saba * su ba shi kyautayi.

                      Dukan sarakuna su durƙusa a gabansa, * dukan alummai su bauta masa!

                      In ya ceci mabukacin da ke kuka, * da zaluntaccen da ba shi da mataimaki,

                 in ya ji tausayin matalauci mabukaci, * har ya ceci rayukan yasassu,

            in ya ceci rayukansu daga zalunci, * jininsu kuwa yana da daraja a gare shi,

        daga nan ransa ya daɗe! * ya sami kyautar zinariya daga Shiba,

        a dinga yi masa addua ba fāshi, * ana roƙa masa albarku kullun.

    Bari mayafin alkama ya rufe ƙasar, * da haki mai yawa a kan tuddai.

    Yayansa su yi fure kamar icen Labanan, * suna yin toho kamar ciyawa.

Bari jikokinsa su ɗade har abada, * suna haifuwar yaya har ran da rana ta ƙare.

    Bari jikokinsa su sami albarka saboda shi, * dukan alummai su yi murna ta wurinsa.

    Albarka ga Allah Yahweh! * Allah na Israila, * mai aikata alajibai shi kaɗai.

Albarka ga sunansa mai ɗaukaka har abada! * Bari duniya duka ta cika da ɗaukakarsa.

Amin, Amin.


Zabura ta 73

Ya Israila, lalle Allah yana kyautata * wa masu tsattsarkar zuciya.

    Amma sawayena sun kusa yin tuntuɓe, * ƙafafuna sun kusa gocewa,

    saad da na ji ƙyashin masu fankama, * har na ga ƙwanjin dukiyar miyagu.

        Ba su da faɗi-tashi, * jikinsu yana da ƙarfi da sulɓi.

        Ba su yin aikin bayi, * ba a tsananta masu kamar sauran yanadan.

            Don haka alfarma ta zamam masu sarƙar wuya, * tufafin zalunci ya rufe su.

            Idanunsu na yin sheƙi fiye da madara, * miyagun dabarun zukatansu ba su da iyaka.

                 Suna zagi da magana Mai Kawo Mugunta, * Azzalumi ne suke kira Maɗaukaki.

                 Bakinsu yana laanta sama, * halshensu bai ƙyale abubuwan Ƙalƙashin Ƙasa ba.

            Don haka sun ƙagara su ƙosad da kansu, * har suna shanye ruwayen teku.

            Suna cewa, Ta yaya Allah zai sani? * ko Maɗaukaki yana da ilimi ne?

        Haka miyagu suke, * ba su damu da Madauwami ba, * sai dukiyarsu kawai suke ƙarawa.

    Ashe, a banza nike kiyaye zuciyata da tsabta, * ina kuwa wanke hannuwana daga laifi,

    domin ana tsananta mani wuni zubut, * ana horona kowace safiya.

        Da na ce, Haka zan yi magana, * da na yi wa jamaar yayanka hainci.

        Da na yi ƙoƙarin gane wannan, * zaluncinsa kawai nike tunani,

        sai da na shiga tsattsarkan mabautar Allah, * kāna na gane ƙarshensu.

    Hakika za ka sa su ƙaura zuwa Gidan Hallaka, * kana sa su fāɗa Kufai.

    Nan da nan za su fāɗa Hallaka, * za a share su da Falgaba!

    Tamkar mafarkin an farka, ya Ubangiji, * za ka mance da su can Garin Aljanu.

        Amma in zuciyata ta ɓaci, * hankalina ya gigice,

            sai in zama wawa mara fahinta, * dabba kurum a wurinka.

            Amma ni kullun ina wurinka, * ka riƙe hannuna na dama.

        Ka bi da ni zuwa mashawartarka, * ka ɗauke ni da ɗaukaka zuwa gunka.

    Me zan rasa a sama * tare da kai? * bana bukatar komi a duniya.

    Jikina da zuciyata sun gaza, ya Dutse, * amma zuciyata da jikina, ya Allah, za su dauwama har abada.

    Sai dai duk wanda ya nisance ka zai hallaka, * ka hallaka dukan masu yin zina ta guje maka.

Ni kam, kusantar Allah na sa ni murna, * na dogara ga Ubangiji Yahweh, * ina shelar dukan ayyukanka.

Zabura ta 74

Don me, ya Allah, kake riƙa yin hushi? * Don me hancinka kuma ke fid da hayaƙi a kan tumakin makiyayarka?

Ka tuna da garken da ka tanada tun dā, * ka fanshi gādonka da kulkinka, * Dutsen Sihiyona inda kake zaune.

Ka ɗaga jamaarka daga daɓen kufai, * magabci ya lalata komi daga tsattsarkan mabautarka.

    Magabtanka sun yi ruri a tsakar taron jamaarka, * sun kafa ɗaruruwan alamu.

        Sun ƙone ƙofar bisa, * suka sassare adon ƙofofi da gatura.

            Sun sassaka dukan ƙyamare, * sun bubbuge su da digogi da gudumu.

        Sun sa wa tsattsarkan mabautarka wuta, * sun wulakanta mazaunin sunanka.

    A zukatansu sun ce, * A ƙone dukan yayansu, * da dukan ɗakunan taron Allah a ƙasar.

        Ba wasu alamu daga wajenka dominmu, * ba sauran wani annabi yanzu, * ba mai bayyana wahayinka da muka samu.

            Ya Allah, har yaushe magabci zai saɓe ka? * maƙiyi kuma zai wulakanci sunanka, ya Jarumi?

            Me ya sa ka janye hannun hagunka? * kana dafe ƙirjinka da hannun dama?

        Ya Allah, ka hallaka sarakunan Gabas, * ka yi nasara a babban birnin duniya.

        Tuntuni ka farfashe Teku da ikonka, * ka kakkarya kawunan Tannin, dodon ruwa, * mai tasowa daga teku.

            Kai ne ka gwararraɓe kawunan Lawiyatan, * ka mai da su abinci, * domin kabilun hamada su ci.

                 Kai ne ka saki maɓuɓɓugu da yan rafuka, * ka ba da busasshiyar ƙasa daga tsaffin koguna.

            Kai ne mai rana da dare, * kai ne ma ka halicci rana da wata.

        Kai ne ka shata kusurwoyin duniya, * kai ne mai gumi mai ɗari.

    Ka tuna cin mutuncin magabci, * wanda ya saɓe ka, Yahweh, * da wawayen mutanen da suka saɓe ka.

        Kada ka ba mahaukatan dabbobi * mutanen da ka koyar wa.

            Ya Jarumi, kada ka ƙyale * rayukan gajiyayyunka.

        Ka dubi Haikalinka, * birnin ya cika da duhu, * karkara kuma da fitina.

    Kada dannannu su sha kunya, * amma bari matalauta da mabukata su yabi sunanka.

Ka tashi, ya Allah, ka tsare hakkinka! * Ka tuna yadda wawaye ke saɓonka wuni zubut.

Kada ka mance da rurin magabtanka, * da hargowar abokan gabarka da ke tasowa kullun.


Zabura ta 75

Mun gode maka, ya Allah, * mun gode maka, ya Makusaci! * sammanka suna bayyana alajibanka.

    I, zan kira taron jamaarka, * in kuma yi shariar adalci.

    Da duniya ke girgiza, * da dukan mazaunanta, * ni ne ke kafa ginshiƙanta.

        Na ce, Ku masu fankama, kada ku yi taƙama, * ku miyagu, kada ku ɗaga muryar ƙahonku!

            Kada ku yi karo da Maɗaukaki, * kada ku yi magana gāba da Dutsen Filazal.

            Domin shi Mai Nasara ne daga Gabas da Yamma, * Shi Mai Nasara ne daga hamadar kudu har duwatsun arewa.

        Domin shi Allah sarki ne, * yana saukad da mutun, * ya tashe shi kuma.

    Domin akwai ƙoƙo a hannun Yahweh, * da bangaji cike da abinshan inabi, * yakan ɗebo, yana zubawa.

    I, za su shanye tsakin, * dukan miyagun duniya za su sha mana!>Amma ni zan ɗaukaka Madauwamin, * in yi waƙa ga Allah na Yakubu.

Zan kakkarya dukan ƙahonin miyagu, * amma ƙahonin Mai Adalcin za su ɗaukaka.

Zabura ta 76

Allah ya bayyana a Yahuda, * a Israila ma sunansa babba ne.

    Kogonsa a Salem yake, * maɓoyarsa a Sihiyona.

    Da walƙiyoyinsu ya kakkarya bakan, * da garkuwar da takobin da makaman yaƙi.

        Ya Haske, kana da kwarjini, * sun yi aniyar kai hari a duwatsun Zaki,

        Amma mayaƙan sun yi barcinsu na ƙarshe, * ba a ƙara samunsu ba, * sojojin sun hallaka duk da ƙarfinsu.

        Da rurinka, ya Allah na Yakubu, * karusar da dokin sun fāɗi sumammu.

            Kai kaɗai ne mai razanarwa, * wa zai iya tsayawa a haushinka, * ga hushinka na tuntuni?

        Daga samaniya zaka yanke hukunci, * ƙasa za ta gigice, ta yi tsit.

        Saad da ka tashi yin sharia, ya Allah, * don ka ceci gajiyayyun duniya,

        za su yabe ka domin tunzurarka da biladama, * waɗanda suka rage bayan haushinka za su kewaye ka.

    Ku yi waadodinku, ku cika * ga Yahweh Allahnku.

    Bari dukan na kewaye da shi * su kai baye-baye ga Mai Gani.

Ya san tunanin hakimai, * mai bantsoro ne ga sarakunan duniya.

Zabura ta 77

Ina kuka, ya Allahn alloli, * ina kuka sosai.

Ina kuka, ya Allahn alloli, * ka ji ni!

    Da nike roƙon Allahna, * ina neman Ubangijina,

    hannunsa yana fāda ni da dare, * baya denawa, * ransa ya ƙi juyaji.

        Nikan tuna da Allah da nishi, * ina magana, amma ruhuna ya karai.

        Idanuna sun saba da tsaro, * yawo nike yi, ba kwanciya ba.

            Ina tunanin zamanin dā, * ina tuna shekarun da suka shuɗe.

            Dukan dare ina kaɗa molo, * ina magana a zuciyata, * ta yadda ruhuna zai warke.

                 Ubangiji zai yi hushi har abada? * Ba zai ƙara jin tausayi ba?

                 Ya dena yin alheri har abada? * ba za a sake samun wahayi daga gunsa ba?

                      Ko kayan cikin Allah sun bushe? * Ko kuwa cikinsa ya ɗame don zafin hushi?

                      Ina jin, Ciwonsa ke nan, * hannun dama na Maɗaukaki ya shanye.

                 Zan ba da labarin ayyukanka masu banmamaki, * i, zan faɗi alajibanka na tuntuni.

                 Zan lissafta dukan ayyukanka, * in yi maganar manyan ayyukanka.

            Ya Allah, kana mulkin dukan tsarkakan malaiku. * Wane allah ne ya fi ka girma, ya Allah?

            Ka zo, ya Allah mai aikata alajibai, * ka nuna ikonka gun mutane.

            Da dantsenka mai ƙarfi * ka fanshi yayan Yakubu da na Yusufu.

        Da ruwaye suka gan ka, ya Allah, * da ruwaye suka gan ka, sun gigice, * har zurfafan teku sun razana.

        Gajimarai sun saki ruwa, * sararin sama ya amsa muryarka, * kibanka sun tafi koina.

    Aradunka ta yi kururuwa a tulluwar sararin sama, * walƙiyoyinka sun haskaka duniya, * Ƙalƙashin Ƙasa kuwa ya razana, ya girgiza.

    Hanyarka bisa teku take, * kana jan zanenka bisa ruwayen da ke sama, * don haka ba a ganin digadiganka.

Ka yi jagoran mutanenka kamar tumaki, * ta hannuwan Musa da Haruna.

Zabura ta 78

    Mutanena, ku kasa kunne ga koyaswata, * ku karkata kunnuwanku ga maganad da zan faɗi.

    Zan buɗe bakina, in yi magana da misali, * zan bayyana kacinci-kacinci na zamanin dā.

        Abin da muka ji muka sani, * da kakanninmu suka gaya mana,

        ba za mu ɓoye wa yayanmu ba, * amma za mu sanar da tsara mai zuwa,

        nasarar Yahweh mai ɗaukaka * da alajiban da ya aikata.

            Ya kafa kaida don Yakubu, * da doka don Israila,

            da cewa abin da ya umurci kakanninmu * su sanad da yayansu,

        don tsara ta gaba ta sani, * da yayan da za a haifa su tashi, * su ba yayansu labarin,

        don su kafa begensu ga Allah, * kada kuma su manta da ayyukan Allah,

    su dinga kiyaye dokokinsa, * kada kuma su zama kamar kakanninsu,

    sangartacciyar tsara mai tawaye, * wadda ba ta yin abu da zuciya ɗaya, * da ruhunsu bai amince da Allah ba.

Yayan Ifraimawa ne mayaƙa masu baka, * maharbansa masu hainci, * masu juya baya a ranar yaƙi.

Sun kasa kiyaye yarjejeniyarsu da Allah, * sun kuma ƙi bin shariarsa.

Sun mance da ayyukansa, * da kuma alajiban da ya nuna masu.

    A idanun kakanninmu ya aikata alajibai, * a filin Zowan,a ƙasar Masar.

    Ya raba teku, ya ratsa ta ciki da su, * ya sa ruwayen sun tsaya kamar bango.

    Da rana ya bi da su da gajimare, * da duhu kuma da hasken wuta.

Ya faskara duwatsu a daji, * ya kuma niimantad da babbar hamada.

Ya fid da ƙoramu daga cikin dutse, * ya sa ruwa yana gudada kamar koguna.

    Duk da haka sun ci gaba da saɓonsa, * suna yi wa Maɗaukaki tawaye a hamada.

    Sun gwada Allah a zukatansu, * suna roƙon abinci don maƙogwaronsu.

        Suka yi maganar saɓon Allah, suka ce: * Ko Allah na iya shirya abinci a jeji?

        Ko da yake ya bugi dutsen, * ruwa kuma ya yi ambaliya, * ƙoramu sun malalo,

        anya zai iya ba da abinci, * ko nama ga mutanensa?

            Lokacin da Yahweh ya ji su, * sai ya fusata,

            ya harzuƙa da Yakubu, * hushinsa ya yi ƙuna kan Israila,

            don ba su gaskata da Allah ba, * balle dogara ga ceton da zai yi.

            Duk da haka, ya umurci sararin sama, * ya buɗe ƙofofin sammai.

            Ya zubo masu manna don su ci, * ya ba su tsaba ta sama.

            Ɗanadan tukururu ya ci abincin malaiku, * ya aiko masu da abinci a wadace.

        Ya sa iskar gabas ta buso daga sama, * ya ma saki iskar kudu daga mafakarsa.

        Ya zubo masu nama daga sama kamar ƙurā, * tsuntsaye kuwa kamar yashin teku.

    Ya sa sun zuba a tsakkiyar sansaninsu, * da kewayen zangonsu.

    Ta haka suka ci, suka ƙoshi, * ya kawo masu iyakar abin da suka lashe.

        Ba su dena tsegunguma ba, * duk da yake ga abinci a bakinsu.

        Hushin Allah ya yi ƙuna a kansu, * ya kashe ƙarfafansu, * ya yayyanke zaɓaɓɓun matasan Israila.

            Duk da haka sai suka ci gaba da yin zunubi, * ba su gaskanta da alajibansa ba.

            Ya sa kwanakinsu saurin wucewa fiye da tururi, * shekarunsu kuma sun fi iska gudu.

                 Da ya riƙa kisansu, sai suka neme shi, * suka tuba, suka bi shi da aniya.

                 Sai suka tuna Allah ne Dutsensu, * Allah Maɗaukaki kuma Mai Cetonsu.

                 Amma sun yi masa daɗin baki, * sun kuma yi masa ƙarya da halshensu.

                 Zuciyarsu ba ɗaya ba ce game da shi, * domin ba su gaskanta da yarjejeniyarsa ba.

            Amma Mai Jinƙan ya gafarta masu zunubansu, * bai hallaka su ba.

            Sau tari ya huce hushinsa, * bai ta da hasalarsa ba.

            Ya tuna su nama da jini ne kawai, * iska mai wucewa ba komowa.

        Sau nawa suka tayar masa a jeji, * suna baƙanta masa ciki a hamada.

    A kai a kai suka gwada Allah, * suna tsokanar Tsattsarkan Nan na Israila.

    Ba su tuna da ikonsa ba, * loton da ya fanshe su daga abokin gaba,

        da ya aikata alajibai a Masar, * da abubuwan banmamaki a filin Zowan,

        inda ya mai da ruwan kogunansu jini, * ba su kuma iya shan ruwan koramunsu ba.

            Ya aika ƙudaje don su cinye su, * da kwaɗi don su hallaka su.

            Ya ba farinɗango hatsinsu, * amfanin gonakinsu kuma ga ƙwari.

                  Ya kashe inabinsu da ƙanƙara, * da ɗoroyinsu da sanyi mai sandararwa.

                 Ƙanƙara ta hallaka shanunsu, * garkunansu gatarin aradu ya tarwatsa.

                      Ya aiko masu da zafin hushinsa, * haushi da hasala da ruɗewa,

                      da ke raka malaiku masu hallakarwa, * waɗanda ke share masa hanya.

                           Bai keɓe su daga mutuwa ba, * amma ya ba da ransu ga annoba.

                           Ya kashe duk ɗan fari a Masar, * amfanin farko na komi nasu a tantunan Hamu.

                           Sannan ya ja gaban mutanensa kamar tumaki, * yana bi da su ta cikin jeji.

                           Ya kare su ba falgabobi, * amma ruwan teku ya dulmuye magabtansu.

                      Ya kai su tudunsa mai tsarki, * dutsen nan da hannun damansa ya kafa.

                      Ya kori alummai a gabansu, * ya kā da su a ƙasarsu mai tsaunuka, * ya sa kabilun Israila sun gaje tantunansu.

                 Amma suka ci gaba da gwada Allah ta tawayensu, * ba su kiyaye dokokin Maɗaukaki ba.

                 Suka yi tawaye da rashin aminci kamar kakanninsu, * sun gaza aiki kamar lalataccen baka.

                 Suka tsokane shi da mabautansu kan tsaunukansu, * da gumakinsu kuma suka sa ya ji kishi.

            Allah ya ji su, ya husata, * Mai Iko ya ƙi Israila.

            Ya bar mazauninsa da ke Shilo, * tantin da ya kafa a tsakkiyar mutane.

        Ya bar mafakarsa ga masu kwashe ganima, * akwatin yarjejeniyarsa kuma a hannun magabci.

        Ya ba da mutanensa ga kaifin takobi, * ya yi hushi da gadonsa.

    Wuta ta ƙone samarinsu, * yan matansu kuma ba a yi masu waƙar amarci ba.

    Firistocinsu sun hallaka da kaifin takobi, * gwaurayensu kuma ba su yi waƙar makoki ba.

Sannan Ubangiji ya farka kamar wanda ke barci, * sai ka ce jarumin da ke hutu bayan shan barasa.

Ya runtumi magabtansa daga bayansu, * ya rufe su da kunya ta har abada.

    Ya yi watsi da alfarwoyin Yusufu, * bai ma zaɓi kabilar Ifraimu ba.

    Amma ya zaɓi kabilar Yahuda, * da Dutsen Sihiyona da yake ƙauna.

    Ya gina tsattsarkan mabautarsa da tsawo kamar sammai, * ya tabbatad da ita kamar ƙasa da ya kafa tun filazal.

Ya zaɓi baransa Dauda, * wanda ya ɗauko daga garken tumaki.

Daga kiwon tumaki ya kirawo shi, * don ya yi kiwon jamaar Yakubu da ke tasa, * da Israila abin gadonsa.

Ya lura da su da kyakkyawar zuciya, * da jagoranci mai kyau ya bi da su.

Zabura ta 79

Ya Allah, baƙi sun afka wa gādonka, * sun ƙazanta Haikalinka, * sun mai da Urushalima kufai.

    Sun bar wa tsuntsaye * gawarwakin bayinka su ci,

        da naman masu bautarka * ga namomin daji.

    Sun zub da jininsu kamar ruwa * ba wani daga kewayen Urushalima * da zai binne su.

Mun zama abin zargi ga maƙwabtanmu, * abin baa da ƙyama ga waɗanda ke kewaye da mu.

    Yahweh, sai yaushe? * Za ka yi hushi har abada? * Har yaushe kishinka zai dinga ƙuna kamar wuta?

    Ya Allah, ka kwararo hushinka, * a kan alumman da ba su san ka ba, * da kan masarautun da ba su kiran sunanka.

    Domin sun cinye Yakubu, * sun kuma mai da ƙasarsa kufai.

        Ya Magatakarda, kada ka rubuto laifinmu,* ko muguntar da kakanninmu suka aikata.

        Bari jiye-jiyen kanka su tarbe mu, * domin mun ƙasƙanta ƙwarai.

    Ka taimake mu, ya Allahnmu mai nasara! * Don sunanka mai ɗaukaka ka cece mu, * ka gafarta mana zunubanmu saboda sunanka,

    don kada alummai su ce, * Ina Allahnsu?

    Don mu ga sunanka ya sanu ga alummai, * ka rama jinin bayinka da aka zubas!

Bari ajiyar zucin ɗaurarru * ta zo wurinka.

    Miƙo hannunka mai tsawo, * ka kare waɗanda aka tanaji kisansu.

        Ya Ubangiji, ka biya wa maƙwabtanmu riɓi bakwai * na zagin da suka yi maka.

    Mu mutanenka ne, tumakin makiyarka, * za mu gode maka har abada.

Daga tsara zuwa tsara kuma * za mu yi shelar yabonka.

Zabura ta 80

            Ya Makiyayin Israila, ka kasa kunne, * ka shugabanci Yusufu kamar garke.

            Ya Mai Zama a kan Kerubobi, ka haskaka * a gaban Ifraimu da Biliyaminu da Manassa!

            Ka ta da ƙarfinka, * ka zo ka cece mu!

Ya Allah, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Yahweh Allah Mai Runduna, * yaya za ka yi hushi, * lokacin da jamaarka ke yin addua?

    Ka ƙosad da mu da kwalla, * ka shayad da mu da bangaji-bangajin hawaye.

    Ka mai da mu madari ga maƙwabtanmu, * maƙiyanmu ma suna yi mana dariya.

Ya Allah Mai Runduna, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Kā fito da kuringar inabi daga Masar, * kā kori sauran alummai, kā dasa ta.

    Kā tuge waɗanda suka gaje ta, * kā sa ta kafa sauya, * ta kuma mamaye ƙasar.

        An lulluɓe duwatsu da inuwarta, * ganyayenta sun rufe rimin Allah.

        Ka sa rassanta su bazu har Bahar Maliya, * yaɗunanta kuma har Kogin Yufiretis.

    Me ya sa ka rushe shingenta, * don duk mai wucewa ya tsigi inabinta?

    Alhanzir-alhanzir na daji sun yi kiwo a cikinta, * zomaye da bareyi sun yi ta cinye ta.

Ya Allah Mai Runduna,, ka juyo wurinmu yanzu-yanzu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Ka lura da abin da hannun damanka ya dasa, * da kuma Ɗan da ka ƙarfafa don kanka.

        Waɗanda suka banka mata wuta, * bari su hallaka ta tsautawar hushinka.

        Ɗora hannunka kan mutumin da ke hannunka na dama, * da kan Ɗanadan da ka ƙarfafa don kanka.

    Ba mu taɓa juya maka baya ba, * ka raya mu don mu kira sunanka.

Yahweh Allah Mai Runduna, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

Zabura ta 81

        Ku yi sowa ta farinciki ga Allahmu na Akwatin Yarjejeniya, * ku yi hayaniyar murna ga Allahn Yakubu.

        Ku raira waƙa, ku buga kuge da tambari, * da kiɗin molo mai daɗi da garaya.

            Ku busa ƙaho a amaryar wata, * da tsakkiyarsa, ran aikin hajinmu.

        Domin kaida ce, ya Israila, * umurni ne kuma daga Allahn Yakubu.

        Ya sanya shi ga Yusufu kamar doka, * saad da ya fito daga Masar.

Na ji maganar wanda ban san shi ba, * na sauke kaya daga kafaɗarsa, * an hutad da hannuwansa daga ɗaukar kwando.

    A cikin wahala ka yi kira, * na kuwa kuɓutad da kai.

Na amsa maka daga maɓoyar aradu, * ko da yake kun fusata ni wurin ruwan Mariba.

    Ku ji, ku mutanena, zan maku bakar shaida, * Israila, sai ku kasa kunne gare ni.

    Kada wani baƙon allah ya kasance a tsakaninku, * ba kuma za ku bauta wa shigaggen allah ba.

        Ni ne Yahweh, Allahnku, * da ya fito da ku daga ƙasar Masar, * na kuwa hangamemen bakinku.

    Amma mutanena ba su ji muryata ba, * Israila kuma bai yarda da ni ba.

    Don haka na yi watsi da su kan taurin zuciyarsu, * sun bi nasu shawarwari.

Dā ma mutanena sun saurare ni, * Israila sun ya bi turbata!

    Da nan take zan kau da magabtansu, * in juya hannuna kan maƙiyansu.

    Duk maƙiyan Yahweh za su duƙa a gabansa, * za su ɗanɗana kudarsu har abada.

Sannan zai ƙosad da Israila da alkamar tuddai, * zan kuwa ƙosad da ku da zuma na kan duwatsu.


Zabura ta 82

Allah yana yin jagorancin taron alloli, * yana zartas da hukuncinsu a tsakkiyarsu:

    Me ya sa kuke kāre marasa gaskiya, * da son zuciya kan miyagu?

    Kāre gajiyayyu da marayu, * ba da gaskiya ga wanda aka cuta da matalauci.

    Ceci gajiyayyu da mabukata, * ka cece su daga hannun miyagu.

    Ba sani ko fahinta, * suna ta yawo cikin duhu. * Ana girgiza dukan harsashun duniya.

    Na yi zaton, Ku alloli ne, * dukanku yayan Maɗaukaki ne.

    Amma kamar mutane za ku mutu, * ku bauɗe kamar kowane sarki.

Tashi, ya Allah, ka hukunta duniya, * ka sarauci dukan alummai da kanka.

Zabura ta 83

Ya Allahna, wane allah ne ya yi kama da kai? * kada ka yi shiru, kada ma ka yi zugum, ya Allah.

    Dubi yadda magabtanka ke surutu, * maƙiyanka kuma suna ɗaga kansu.

        Suna shirya wa mutanenka shawarwarin makirci, * a kan hajarka suke yin maƙarƙashiya.

    Suna cewa: Ku zo, mu shafe alummarsu, * kada a ƙara jin sunan Israila.

        I, suna yin shawara da zuciya ɗaya, * masu tasar maka suna ƙulla yarjejeniya:

        Idumawa da Ismailawa, * Mowabawa da Hagarawa,

            Bibilosawa tare da Amalakawa, * Filistiyawa da mutanen Taya,

            jamaar Assuriya ma ta gama kai da su, * inda ta zama garkuwar yaƙin yayan Lutu.

            Ka yi da su kamar yadda ka yi da Midiyan * da Sisera, da Yabin a Kogin Kishon.

            Ka shafe su daga fuskar duniya, * sai sun zama taki.

        Ka mai da dattawansu kamar Oreb da Ziyib, * da dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,

        waɗanda suka ce, Bari mu ƙwato * wurare mafi kyau na ƙasarsu.

    Ya Allahna, ka mai da su kamar bunu, * kamar ƙaiƙai a gaban iska.

        Kamar wutar gobarar kurmi, * da harsunan wuta masu lashe gefen dutse,

            ka runtume su da hadarinka, * ka raka su da iskarka mai ƙarfi.

        Ka cika fuskarsu da kunya, * Yahweh, ka ɗau fansar sunanka.

    Bari su kunyata, su muzanta * har abada * su hallaka da ƙasƙanci.

Bari su san kai ne ke da suna Yahweh, * kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.

Zabura ta 84

Lalle, mazauninka mai daɗi ne, * Yahweh Mai Runduna!

Yahweh, raina yana ɗoki da marmarinka sosai, * ga begen farfajiyarka! * zuciyata da jikina suna sowa.

    Ya Allah, ya Allah Mai Rai, * har gwara ta sami gida.

        Tsattsewa kuma ta sami sheƙa, * inda za ta sa yayanta.

            Yahweh Mai Runduna, * Sarkina da Allahna!

        Albarka ga mazaunan gidanka, * kusa da bagadanka suna riƙa yabonka.

    Albarka ga wanda mafakarsa a wurinka ne, * zuciyarsa kuma tana yabonka.

        Allah ya ƙaddara ƙoramu su malalo a kwarin, * ya mai da kwarin maɓuɓɓuga.

        Da tsautawa Mai Ba da Ruwa * ya yawaita shi da tabkuna!

            Suna tafiya daga ƙauye zuwa ƙauye, * don su ga Allah mai alloli a Sihiyona.

        Yahweh, Allah Mai Runduna, * ka ji adduata, * ka kasa kunne, ya Allah na Yakubu!

        Ka duba shugabanmu da alheri, ya Allah, * ka zuba ido a kan fuskar shafaffen sarkinka.

    Kwana ɗaya a farfajiyarka * ya fi kwana dubu a Kabari kyau.

        Gara a jira a ƙofar gidanka, ya Allahna, * da zama a Alfarwar Mugu.

        Lalle, Ranarmu da Shugabanmu, * Yahweh Allahnmu * ya kan ba da alheri da ɗaukaka.

    Yahweh ba zai hana ruwansa ba * daga masu bin hanyar gaskiya.

Yahweh Mai Runduna, * albarka ga wanda ya dogara gare ka!

Zabura ta 85

Yahweh, ka kyautata wa ƙasarka, * ka mai da lafiyar Yakubu!

Ka kau da laifin mutanenka, * ka yafe dukan zunubansu!

Ka kau da duk haushinka, * ka huce zafin hushinka!

    Yahweh mai arzuta mu, ka komo mana, * ka sauke fusatar da ka yi da mu!

    Za ka yi hushi da mu ne har abada? * kana tsawaita hushinka har ga tsararraki masu zuwa?

        Kai ne Mai Nasara, * ka sake raya mu, * don mutanenka su yi murna da kai.

        Yahweh, ka nuna mana tausayinka, * ka haɗa mu da arzikin da ka kan bayas.

            Bari in faɗi abin da Allah ya ce: * Hakika, Yahweh ya alkawalta zaman lafiya

        ga mutanen da ke bautar masa, * da masu sake sa zuciya a gunsa.

        Albarkarsa tana dab da masu tsoronsa, * i, ɗaukakarsa tana zaune a ƙasarmu.

    Tausai da aminci za su gamu, * gaskiya da lafiya za su sumbaci juna.

    Aminci zai tsiro daga ƙasa, * gaskiya za ta karkato daga samaniya.

Da tsautawa Yahweh zai ba da ruwan sama, * ƙasarmu kuma za ta ba da amfaninta.

Gaskiya za ta yi tafiya gabansa, * kyan gani kuma zai bi sawayensa.

Zabura ta 86

Ka karkato kunnenka, Yahweh, ka amsa mani, * domin ni gajiyayye ne da mabukaci.

Ka kiyaye raina, * domin ni mai bautarka ne.

    Ka ceci bawanka * da ke dogara gare ka, ya Allah.

Ka ji tausayina, ya Ubangijina, * a gare ka nike yin kuka wuni zubut.

Ka faranta ran baranka, ya Ubangijina, * domin a gare ka nike ɗaga raina.

    Tun da kai, Ubangijina, mai alheri da yafewa ne, * mai yalwar rahama ga duk masu roƙonka,

        ka kasa kunne, Yahweh ga adduata, * ka ji roƙona na neman afuwa.

        Ran da ake tsananta mani na kira ka, * sai ka amsa mani!

    Babu kamarka a cikin alloli, * ya Ubangijina, * ba kuma ayyuka irin naka.

        Ya Ubangijina, in ka yi wani abu, * dukan alummai za su zo,

        su yi sujada a gabanka, * su ɗaukaka sunanka.

    Hakika, kai mai girma ne, * Mai Yin Alajibai, * kai kaɗai, ya Allah.

        Ka nuna mani hanyarka, Yahweh, * don in bi ka kai kaɗai da aminci. * Koya wa zuciyata don in ji tsoron sunanka.

        Zan yi maka godiya, ya Ubangijina da Allahna * da dukan zuciyata * zan ɗaukaka sunanka, ya Madauwami.

    Tun da ƙaunarka mai girma ce, ya Maɗaukaki, * za ka jawo ni daga ƙarshen Shawol.

Ya Allah, masu alfarma sun tasam mani, * kungiyar mafaɗata tana neman raina, * ba su kula kai ne Shugabana ba.

Amma kai, ya Ubangijina, Allah ne mai rahama mai jinƙai, * mara jinkirin hushi, mai yalwar jinƙai da gaskiya. * Ka juyo gare ni, ka ji tausayina.

    Ka ba bawanka nasararka, * ka sa ɗanka mai aminci ya rinjaya.

Ka aikata mani alama, ya Managarci, * don maƙiyana su gani su kunyata.

Yahweh, kai kanka ka taimake ni, * ka sanyaya mani zuciya.

Zabura ta 87

        Ya birnin da ya kahu a kan tsarkakan duwatsu, * ya ƙofofin Sihiyona, Yahweh yana son ku.

        Shi ne Gwanin ginin gidajen Yakubu masu ɗaukaka * da ke magana a cikinka, ya birnin Allah:

Zan rubuta Masar da Babila * a cikin waɗanda suka san ni,

    har da Filistiya da Taya da Habasha: * Waɗansunsu a can aka haife su.

        Amma game da Sihiyona za a ce: * Kowanensu an haife shi a can, * Maɗaukaki kuma zai tabbatad da ita.

    Yahweh zai rubuta a cikin kundin mutane, cewa: * An haifi wannan a can.

Dukan waɗanda suka sha wuya a cikinki * za su yi waƙa da rawa.

Zabura ta 88

Yahweh, Allahna Macicina, * da dare da rana ina kuka gare ka.

Bari adduata ta zo gabanka, * ka kasa kunne ga kukana.


Gama ruhuna cike ya ke da wahala, * raina kuma ya kai gab da Shawol.

An lissafta ni tare da masu zuwa Rami, * na zama mutun mara ƙarfī.

    A fadar Mutuwa tabarmana yake, * kamar yankakku, * gadona yana Kabari,

    inda ba ka tunawa da su, * tun da an yanke ƙaunarka daga gare su.

    Kā jefa ni ƙuryar Rami, * a wurare masu duhu da zurfi.

    Hushinka ya yi ƙuna a game da ni, * ka ma tsananta haushinka a kaina.

Ka sa abokaina yin nesa da ni, * don na zama abin ƙyama a gare su.

Ina kurkuku, bana iya gudu, * idanuna sun rage gani saboda wahala.

    Ina kiran gare ka kullun, Yahweh, * ina ɗaga hannuwana gare ka.

        Kana aikata alajibai ga matattu? * Ko kuwa kurwoyinsu na tashi su yabe ka?

            Ana sanar da alherinka a Kabari? * ko kuwa amincinka a Ƙasar Mutuwa?

        Ana sanar da muujjizanka a Duhu? * ko kuma alherinka a Ƙasar Mantuwa?

    Amma ina yin kira gare ka, Yahweh, * da asuba bari adduata ta zo gabanka.

Yahweh, don me kake ya da ni? * kana juya fuskarka daga gare ni?

    Da ƙunci da nishi ina mutuwa, * ina shan wahala daga tsananinka.

        Harzuƙarka ta bangaje ni, * bankarka ta yi kaca-kaca da ni.

    Suna kewaye ni wuni zubut kamar tsufana, * suna kai mani hari a kaɗaicina.

Kā kai maƙwabcina mai ƙaunata nesa da ni, * duhu kaɗai ne abokina.

Zabura ta 89

        Yahweh, zan raira waƙar ƙaunarka har abada, * zan yi shelar amincinka a kowane zamani.

        Da bakina ina furtawa: * Ya Madauwami, ƙaunarka ce ta halicci sammai, * amma ka sa amincinka ya zarce su nesa.

        Na yi yarjejeniya da zaɓaɓɓena, * na rantse wa barana Dauda:

        Zan kafa zuriyarka har abada, * in inganta kursiyinka ga dukan zamanai.

A can sama ana yabon alkawalinka, Yahweh, * amincinka kuma a taron tsarkaka.

Domin wanene a sama ya iya kwatanci Yahweh? * Wa ya iya kwatancin Yahweh a cikin alloli?

    Allah ne mai bantsoro a mashawartar tsarkaka, * mai girma, mai banrazana ga dukan waɗanda ke kewaye da shi.

    Yahweh, Allah Mai Runduna, wa yake kamarka? * Yahweh mai iko, amintattunka suna kewaye da kai.

        Kai ne mai mulkin gadon bayan teku, * in raƙuman ruwansa na tashi, kai ne mai kwantad da su.

        Kā rushe Rahab kamar gawa, * da hannunka mai ƙarfi ne kā yi ɗaiɗai da magabtanka.

            Kai ne mai sammai da ƙassai, * duniya da dukan abin da ke cikinta kai ne ka kafa su.

            Duwatsun Zafon da Amanus kai ne ka hallice su, * Dutsen Tabor da Dutsen Harmon suna waƙa a gabanka.

        Kana da hannu ƙaƙƙarfa, ya Mayaƙi, * hannun hagunka ya jarunta, * hannun damanka ya ci nasara.

        Gaskiya da adalci su ne harsashin kursiyinka, * ƙauna da aminci suna tsaye a gabanka.

    Masu albarka ne da ke sanin haskenka, * waɗanda ke tafiya da ƙyalƙyalin fuskarka, Yahweh.

    Suna farinciki a gabanka wuni zubut, * suna murna da alherinka.

I, kai ne nasararmu mai ɗaukaka, * agajinka yana sa mu ci nasara.

Hakika Yahweh ne Shugabanmu, * Tsattsarkan Nan na Israila shi ne Sarkinmu.

    A zamanin dā ka yi magana ta wahayi, * i, ka ce da mai bautarka:

    Na mai da matashi sarki a maimakon mayaƙi, * na ɗaukaka saurayi fiye da mai ƙarfi.

        Na sami barana Dauda, * da maina mai tsarki na shafe shi.

        Hannuna ne zai tabbatad da ikonsa, * kafadata za ta ƙarfafa shi.

            Ba magabcin da zai tsokane shi, * ɗan mugunta ba zai rinjaye shi ba.

            Amma zan gwabji magabtansa a gabansa, * in kā da maƙiyansa.

                 Amincina da ƙaunata suna tare da shi, * ta wurin sunana zai yi nasara.

                 Zan sa hannun hagunsa bisa teku, * hannun damansa kuma kan Yufiretis.

                      Shi zai kira ni, * Kai ubana ne, Allahna, * kuma Dutsen cetona.

                      Zan mai da shi ɗan farina, * mafi ɗaukaka a cikin sarakunan duniya.

                 Zan ƙaunace shi har abada, * yarjejeniyata da shi za ta tabbata.

                 Zan sa zuriyarsa a kan kursiyinsa, * gadon mulkinsa ma zai daɗe kamar kwanakin sammai.

            In yayansa sun ƙeta shariata, * sun ƙi bin umurnaina,

            in sun saɓi kaidodina, * ba su kuma kiyaye dokokina ba,

            zan hori tawayensu da sanda, * taurin kansu kuma da bulala.

        Amma ba zan taɓa janye ƙaunata daga gunsa ba, * ba ma zan ƙaryata amincina ba.

        Ba zan karya jarjejeniyata ba, * ko kuwa in canza maganata.

    Daga yanzu na rantse da tsarkina, * bana iya yi wa Dauda ƙarya.

    Layin mulkinsa zai jure har abada, * kursiyinsa ma kamar rana a gabana.

    Kamar wata jikokinsa za su rayu, * gadon sarautarsa ma zai tabbata fiye da sararin sama.

Duk da haka cikin zafin hushi kā jefad da shafaffen sarkinka, * ka harzuƙa da shi.

Kā jefad da jarjejeniyarka da baranka, * ka wulakanta kambinsa.

    Kā huhhuda garunsa, * ka mai da wuraren tsaronsa kago.

    Duk masu wucewa suna cin ganimarsa, * ya zama abin ƙyama ga maƙwabtansa.

        Kā ɗaukaka hannun daman abokan gabarsa, * kā ɗaga hannuwan maƙiyansa.

        Da hushinka kā juye bakin askarsa, * ba ka tabbatad da takobinsa ba.

            Ka sa ya dena tashe a cikin mayaƙansa, * kā kuma jefad da kursiyinsa ƙasa.

            Kā gajarta kwanakin samartakarsa, * kā hana mashi haifuwa cikin ƙuruciyarsa.

        Yahweh, har yaushe za ka juya baya? * ka bar hushinka, ya Mai Nasara, ya yi ta ci kamar wuta?

        Ka tuna da ɓacin raina, * da yan kwanakin raina. * Saboda me kā halicci dukan yanadan?

    Wane rayayyen mutun ne ba zai ga mutuwa ba? * Wa zai ƙwaci ransa daga hannun Shawol?

    Ina ayyukan tausayinka na dā, * ya Ubangiji, * waɗanda ka alkawalta kan amincinka ga Dauda?

Ka tuna, ya Ubangiji, da cin mutuncin da aka yi wa bawanka, * yadda a ƙirjina nike ɗaukar kiban alummai,

yadda magabtanka, Yahweh, ke wulakanta ni, * da zage-zage suke wulakanta shafaffen sarkinka.

Yabo ga Yahweh har abada! * Amin, summa Amin.

Zabura ta 90

Ya Ubangiji, agajinmu, ka zo! * ka zama namu daga zamani zuwa zamani.

Kafin halittar duwatsu, * ko ƙasa da duniya, * tun filazal har abada kana nan.

    Kada ka mai da mutun ga Caɓi, * kada ka ce, Kai, ku yanadan, ku dawo!.

    Domin shekaru dubu a ganinka * suna wucewa kamar jiya, * kamar saar tsaro ta dare.

        In ka tsige su da dare, * da sassafe suna kama da ciyawa da aka yanke.

        Ta tsira da safe, * an yanke ta da yamma, * takan yi yaushi ya bushe.

    Muna hallaka a cikin hushinka, * muna gajiya cikin haushinka.

    Kana riƙe da laifofinmu a gabanka, * zunubanmu tun na ƙuruciya suna a hasken fuskarka.

        Duk kwanakinmu sun shuɗe * a cikin hushinka.

            Aiki ya zo ƙarshe, * shekarunmu kamar ajiyar zuciya suke.

            Tsawon ranmu shekaru sabain ne, * in muna da ƙarƙo, shekaru tamanin.

        To, alfarma wauta ce mara kyau, * jin daɗi na wucewa, mu ma za mu shuɗe.

    Wa zai gane taadin hushinka, * ko masu tsoronka ma za su gamu da haushinka?

    Don haka ka koya mana mu ƙirga kwanakinmu, * don mu sami zuciyar hikima.

        Yahweh, ka dawo, * don me kake jinkiri? * ka ji juyayin bayinka.

        Da safe ka wadata mu da ƙaunarka, * don mu yi sowar farinciki a dukan kwanakinmu.

    Ka sa kwanakin farincikinmu su zarce na bakincikinmu, * da shekarun da muka ga balai.

    Ka bayyana aikinka ga bayinka, * da sarautarka kuma ga yayansu.

Bari alherin Ubangiji * Allahnmu ya sauko mana!

Ya taimaki aikin hannuwammu * don amfanimmu!

Ya taimaki aikin hannuwammu * don amfaninsa!

Zabura ta 91

Mai kursiyin ƙalƙashin kāriyar Maɗaukaki, * wanda ke kwana a inuwar Mafi Iko Shaddai,

ya ce: Yahweh matserata da mafakata, * ya Allahna, na dogara gare ka.

    Shi kaɗai ne zai tsirad da kai daga tarko, * ya kāre ka daga makamai masu guba.

    Da gashinsa zai rufe ka, * ƙalƙashin fukafukansa za ka fake, * kafadarsa za ta zama garkuwarka da wargajinka.

        Kada ka ji tsoron taron karnuka da dare, * ko kibiyar da ke walankeluwa da rana,

        ko balain da ke shawaji da dufu, * ko allobar da ke kai da kawo da tsakar rana.

            Ko da dubu sun faɗi a hagunka, * dubu goma kuma a damanka, * ba za su kusance ka ba.

            Idanunka za su ga ruɓarsu, * za ka ga ribar miyagu.

        In ka mai da Yahweh matserarka, * Maɗaukaki mafakarka,

        ba wani mugun abin da zai same ka, * ba wani balain da zai tunkari alfarwarka.

    Gama zai aiko maka da malaikunsa, * don su kiyaye ka a dukan hare-haren yaƙinka.

    Za su tallabe ka da hannuwansu, * don kada ka yi tuntuɓe da dutse.

    Za ka taka zaki da kububuwa, * za ka bi ta kan marakin zaki da maciji.

In ya manne mani, zan cece shi, * in ɗaukaka shi in yana shaidar sunana.

In ya kira ni, zan amsa masa, * in kasance da shi a lokacin wahala, * zan cece shi, in shirya masa liyafa.

Zan wadata shi da tsawon rai, * in sa ya sha ruwan cetona.

Zabura ta 92

Yahweh, ya kyautu a yi yabo * da waƙar sunanka, ya Maɗaukaki,

a yi shelar ƙaunarka da safe, * da amincinka dukan dare,

da kiɗin molo da kuntigi, * da muryar garaya.

    Domin ka sa ni murna, Yahweh, ta aikinka, * saboda abubuwan da ka yi ina waƙa ta murna.

    Ayyukanka manya ne, * Yahweh Mai Duka, * tunaninka suna da zurfi ƙwarai.

        Daƙiƙi baya sanin haka, * wawa baya ganewa:

            lokacin da miyagu ke toho kamar ciyawa, * dukan masu ƙeta ma suna ci gaba,

                 yana hallaka su har abada. * amma kai, Yahweh, Mai Sama ne har abada.

                 Domin ga magabtanka, Yahweh, * ga magabtanka sun hallaka, * an fatattaki masu aikata mugunta.

            Amma kā ɗaga ƙahona kamar ƙahon ɓauna, * an shafe ni da sabon mai.

        Idanuna sun harari matseguntana * da miyagu masu neman tasam mani.

    Kunnuwana sun ji: * Masu gaskiya za su yi albarka kamar icen dabino, * su yi girma kamar icen al-ul na Labanan.

    An dasa su a gidan Yahweh, * za su yi yabanya a farfajiyar Allahnmu.

Suna cike da ruwa har tsufansu, * za su yi zamansu ɗanyu masu duhuwa,

suna shelar gaskiyar Yahweh, * shi Dutsena wanda ba cuta gare shi.

Zabura ta 93

Yahweh yana mulki, * yana sāye da ɗaukaka.

Yahweh na saye da alkyabba, * ya yi ɗamara da nasara.

    Ya kafa duniya sosai, * ba za ta ƙara girgiza ba.

    An kafa kursiyinka tun zamanin dā, * tuntuni kake.

        Igiyoyin teku sun tayas, Yahweh, * igiyoyin teku sun tayas da aradunsu, * igiyoyin teku sun tayas da tsawar
raƙumansu.

    Amma Yahweh ya fi tsawar ruwa ƙarfi, * ya fi raƙuman ruwan teku iko, * ya fi sama iko.

Kafawar sarautarka ta tabbata tun dā, * Yahweh, a cikin gidanka tsattsarka za su yabe ka, * har abada abadin.

Zabura ta 94

Ya Allah mai sakayya, Yahweh, * ya Allah mai sakayya, ka haskaka.

Ka tashi, ya alkalin duniya, * ka ba masu izgilanci hakkinsu.

    Har yaushe ne yan taurin kai, Yahweh, * har yaushe ne miyagu za su yi alfarma?

    Har yaushe za su yi ta maganar wulakanci, * dukan miyagu za su yi fahariya?

        Sun ragargaji mutanenka, Yahweh, * naka ne suke tsanatawa.

    Sun kashe gwauruwa da baƙo, * suna yi wa marayu kisan gilla.

    A zatonsu, Yahweh baya gani, * Allah na Yakubu baya yin laarki.

        Ku daƙiƙai, ku koyi hikima! * Ku wawaye, yaushe za ku fahinta?

            Wanda ya dasa kunne, ba ya iya ji? * wanda ya sifanta ido, ba ya iya gani?

            Mai koya wa alummai, ba ya iya yin hukunci? * ko kuwa malamin yan adan na rasa ilimi ne?

        Yahweh ya san shirye-shiryen mutane, * duk banza ne.

        Yahweh, mai albarka ne wanda ka koyawa,* wanda ka sanar da shariarka,

            kana ba shi hutu bayan miyagun kwanaki, * lokacin da ake gina rami don miyagu.

            Hakika Yahweh ba zai yas da jamaarsa ba, * ba zai ƙyale nasa ba.

        Amma Mai Kursiyin Adalci zai raya gaskiya, * da dukan masu kirki.

    Wa ya tsaya mani a game da miyagu? * a kan masu aikata mugunta wa ya goyi bayana?

    In da Yahweh bai zama mataimakina ba, * da tuni na daɗe a Kukuku.

        Saad da na ce, Ƙafata tana nutsewa, * Yahweh, ƙaunarka ce ta tallabe ni.

        Saad da damuwata ta yawaita, * taaziyyarka ce ta faranta mani rai.

    Anya, kursiyin zalunci zai iya yin tarayya da kai? * mai karya sharia zai sami kariya a wurinka?

    Sun taru don su kashe mai gaskiya, * a asirce suke hukunta mara aibu.

Amma Yahweh ya zama garu gare ni, * Allahna kuma dutsena na fakewa.

Ya sa muguntarsu ta koma kansu, * saboda sharrinsu ya hallaka su, * Yahweh Allanmu ya hallaka su.

Zabura ta 95

Ku zo, mu yi waƙar murna ga Yahweh, * mu gai da Dutsen da ya cece mu.

Mu zo gabansa da yabo, * mu gai da shi da waƙoƙi.

    Gama Yahweh Allah ne mai girma, * babban Sarki bisa dukan alloli.

    A hannuwansa ne Ramukan Ƙalƙashin Ƙasa suke, * tulluwoyin duwatsu ma nasa ne.

    Ruwan teku nasa ne, tun da shi ya yi shi, * busasshiyar ƙasa shi ya sifanta ta da hannuwansa.

        Ku zo, mu sunkuya, mu yi sujada, * bari mu durƙusa a gaban Yahweh Mahaliccinmu.

        Gama shi ne Allahnmu, * mu ne mutanen makiyayarsa, * garken filin kiwonsa.

    Yau sai ku saurari Mai Bantsoro yana magana: * Kada ku taurare zukatanku

    yadda ya faru a Mariba, * ko kamar ranan nan a Masaha cikin jeji,

    inda kakanninku suka jarabce ni, * suna tsokanata, ko da yake sun ga aikina.

Shekaru arbain na jure da tsaran nan, * sai da na ce:

Su mutane ne masu yawo da zuciya, * ba su san hanyoyina ba.

Daga nan a husace na yi rantsuwa, * Ba za su shiga hutuna ba har abada.

Zabura ta 96

Ku yi wa Yahweh sabuwar waƙa, * ku yabi Yahweh, dukan mutanen duniya, * ku yi wa Yahweh waƙa, ku yabi sunansa!

Ku yi zancen nasararsa daga teku zuwa teku! * A tsakkiyar alummai ku ba da labarin ɗaukakarsa, * da alajibansa a gaban dukan mutane!

    Domin Yahweh mai girma ne, mai cancantar yabo, * mai bantsoro ne fiye da dukan alloli, * amma allolin alummai tsummoki ne kawai.

    Yahweh ne ya yi sammai, * ɗaukaka da kwarjini suna gabansa, * ƙarfi da kyau a gefensa.

             Ku yi wa Yahweh, ku kabilan mutane, * ku yi wa Yahweh ɗaukaka da yabo, * ku yi wa Yahweh ɗaukakar da ta cancanci sunansa.

             Ku kawo baiko, ku shiga farfajiyarsa, * ku sunkuya wa Yahweh loton da Tsattsarkan nan ya bayyana, * ku yi rawar jiki a gabansa, ku dukan duniya!

    A tsakkiyar alummai ku ce, Yahweh yana mulki. * duniya ta kafu, ba za ta jijjigu ba. * Zai sharianta mutane da gaskiya.

    Bari sammai su yi murna, duniya ta yi farinciki, * bari teku da duk abin da ke cikinsa su yi ƙugi, * tuddai da duk abin da ke a kansu su ji daɗi!

Sannan dukan itatuwan kurmi za su yi sowar murna * a gaban Yahweh in ya zo, * in ya zo domin hukunta duniya.

Zai hukunta duniya da gaskiya, * alummai da amincinsa.

Zabura ta 97

Yahweh yana mulki, * bari duniya ta yi murna, * tsibirai masu yawa kuma su cika da faraa.

    Gajimarai da hadari suna kewaye shi, * adalci da gaskiya ne tushen kursiyinsa.

Wuta tana tashi a gabansa, * tana kuma bin bayansa.

    Walƙiyoyinsa suna haskaka duniya, * ƙasa ta gani tana rawar jiki.

    Duwatsu suna narkewa kamar kyandir * da ganin Yahweh, * da ganin Ubangijin duniya duka.

        Sammai suna faɗin hakkinsa na gaskiya, * dukan mutane kuma suna ganin ɗaukakarsa.

        Bari dukan masu bautar gumaka su kunyata, * masu rubar tsummokinsu. * Ku sunkuya masa, ku alloli duka.

    Bari Sihiyona ta ji, ta yi farinciki, * yayan Yahuda mata su yi murna, * saboda tabbacin ƙaunarka, Yahweh.

    Domin kai ne Yahweh Maɗaukaki, * Mafi Girma bisa dukan duniya, * kai ne bisa dukan alloli.

Yahweh na son masu ƙin mugunta, * yana kiyaye rayukan masu bautarsa, * zai cece su daga hannun miyagu.

An ƙaddara lambun aljanna domin masu adalci, * farinciki kuwa don zukatai masu gaskiya.

Ku yi farinciki da Yahweh, ku masu gaskiya, * ku yi wa tsattsarkan sunansa godiya.

Zabura ta 98

Ku yi wa Yahweh sabuwar waƙa, * domin ya yi alajibai.

Hannunsa na dama ya kawo masa nasara, * dantsensa kuma ya keɓe shi.

Yahweh ya sanar da nasararsa * a idanun alummai * ya nuna ramuwarsa.

    Ku tuna da ƙaunarsa da amincinsa, * ya gidan Israila!

    Dukan iyakokin duniya, * ku ga nasarar Allahnmu!

        Ku yi sowa ga Yahweh, dukan duniya, * ku yi hayaniyar murna da waƙoƙin farinciki.

        Ku raira waƙa ga Yahweh da molo, * da molo da murya mai daɗi.

        Da algaitu da muryar ƙahoni, * ku yi waƙa a gaban Yahweh Sarki!

    Bari teku da abin da ke ciki su yi ƙugi, * duniya da dukan mazaunanta.

    Bari igiyoyin teku su taɓa hannu, * duwatsu su yi sowa tare don murna

a gaban Yahweh, * in ya zo, * don ya hukunta duniya.

Zai hukunta duniya da gaskiya, * alummai kuma da adalci.

Zabura ta 99

Yahweh ne yake mulki, * bari mutane su yi rawar jiki.

Mai Zama a kan Kerubobi, * bari ƙasa ta girgiza.

Yahweh ya fi Sihiyona girma, * yana birbishin dukan ƙarfafan iskoki.

    Bari su yabi suanka, * ya Mai Duka, Mai Bantsoro. * Tsattsarka ne shi!

    Sarki mafi ƙarfi, * mai son gaskiya, * kai ne ka kafa adalci.

    Kai ne ka aikata adalci * da gaskiya a gidan Yakubu.

    Ku ɗaukaka Yahweh Allahnmu, * ku yi sujada a matashin ƙafafunsa. * Tsattsarka ne shi!

    Musa da Haruna ne tsakanin firistocinsa, * Samaila ma na cikin masu kiran sunansa.

    Ya amsa masu * daga ginshiƙin gajimare * ya yi magana da su.

Sun kiyaye dokokinsa, * shariar da ya ba su. * Yahweh Allahnmu, kai ne ka amsa masu.

A gunsu, kai Allah Mai Gafartawa, * wanda ka tsarkake su daga zunubansu.

Ku ɗaukaka Yahweh Allahnmu, * ku yi sujada a tsattsarkan dutsensa. * Gama Yahweh Allahnmu tsattsarka ne.

Zabura ta 100

Ku yi sowa ga Yahweh, dukan duniya, * ku bauta wa Yahweh da farinciki, * ku zo gabansa da waƙa ta murna.

    Ku san dai Yahweh Allah ne. * Mai Iko Duka ne, ya yi mu. * Mu mutanensa ne, garken da yake kiwo.

    Ku shiga ƙofofinsa da yin godiya, * farfariyarsa da waƙar yabo. * Ku gode masa, ku yabi sunansa.

Gama Yahweh mai alheri ne, * ƙaunarsa na nan tun filazal, * amincinsa kuma har dukan zamanai.

Zabura ta 101

Zan yi waƙar ƙaunarka da adalcinka, * Yahweh, a gare ka zan raira yabo.

Zan bayyana kammalalliyar sarautarka. * Yaushe ne za ka zo gare ni?

    Na zama da zuciya mara aibu * a cikin fādata.

    Ban taɓa sa abu mara moriya * a gaban idanuna ba.

    Na ƙi sanaar yin gumaka, * ba ta manne mani ba.

        Mai karkatacciyar zuciya ya yi nesa da ni, * ban ma yi abuta da mugu ba.

        Duk wanda ya yi tsegumin maƙwabcinsa a asirce, * na kwaɓe shi.

        Mai girman kai da zuciyar alfarma, * na gama da shi.

    Idanuna a kan amintattun yan ƙasata ne, * don su zauna da ni.

    Sai mutun mai kammalallen hali ne * zai yi mani hidima.

    Mai aikata yaudara bai taɓa zama a fādata ba, * wulli manajan ƙarya bai taɓa wali gaban idanuna ba.

Ina yanka dukan miyagun ƙasa * sai ka ce hurtuman shanu.

Masu aikata mugunta ɗaya da sauran, * ina hallakawa daga birnin Yahweh.

Zabura ta 102

Yahweh, ka ji adduata, * bari kukana ya kai gare ka!

Kada ka juya fuskarka daga gare ni * a cikin ranar wahalata.

Ka kasa kunne gare ni, ran da na yi kira, * ka gaggauta ka amsa mani.

    Gama kwanakina suna wucewa da sauri fiye da hayaƙi, * ƙasusuwana ma suna ƙonewa kamar kaskon wuta.

    Zuciyata ta ƙone kamar ciyawa, ta yankwane, * na rame saboda Mai Cinyewa.

    Muƙamuƙaina suna ciwo da nishina, * ƙasusuwana suna manne wa namana.

        Kamar ungulu nike a cikin daji, * na zama mujiya ta cikin kangaye.

        Bana barci, na zama kamar gwara * mai kuka a kan ɗaki wuni zubut.

    Magabcina yana zagina, * Mai tonona yana yin biki da ni.

    Toka ce abincina, * daga kwallana nike samun ruwan sha.

Saboda haushinka da hushinka, * kā ɗaga ni, ka kuma jefad da ni.

Kwanakina kamar inuwar da ke ƙara tsawo suke, * ina kuma yankwanewa kamar ciyawa.

    Amma kai, Yahweh, * kana sarauta tun filazal, * kursiyinka ma ya tabbata har abada.

    Za ka tashi, ka nuna tausayi ga Sihiyona, * gama lokacin a ji tausayinta ya yi, * i, ƙayyadadden lokacin ya zo.

        Bayinka suna jin daɗin duwatsunta, * suna kuma yin juyayin turɓayarta.

        Alummai za su ji tsoron sunanka, * Yahweh, * dukan sarakunan duniya ma za su ji tsoron ɗaukakarka,

            Loton da Yahweh ya sake gina Sihiyona, * ya bayyana gare ta da ɗaukakarsa,

                 loton da ya ji adduar matalauta, * bai ma ƙyale roƙonsu ba.

            Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, * don mutanen da za a halitta su yabi Yahweh.

        Yahweh ya zuba ido daga can tsattsarkan wurinsa, * daga sammai ya dubo ƙassai,

        don ya ji nishin bursunoni, * ya yanto waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa,

    domin a ji shelar sunan Yahweh a Sihiyona * da yabonsa a Ƙudus,

    saad da mutane ke taruwa, * tare da sarakuna don su bauta masa.

Yahweh ya raunana ƙarƙona da ikonsa, * Allahna ya gajarta kwanakin moriyata.

Kada ka sure ni kamin rabin kwanakina, * da yake shekarunka ba su da iyaka.

    Tuntuni kā sa harsashin duniya, * sammai kuma aikin hannuwanka ne.

    Su za su hallaka, amma kai za ka wanzu, * dukansu za su ƙoƙe kamar tufafi.

    Kana sauya su kamar riguna, * su ma suna shuɗewa.

Amma kai kana zama yadda kake, * shekarunka ma ba za su ƙare ba.

Yayan bayinka za su zauna a tabbace, * jikokinsu kuma za su kafu a gabanka.

Zabura ta 103

Yabi Yahweh, ya raina! * duk jikina, yabi sunansa mai tsarki!

Yabi Yahweh, ya raina! * kada ka manta da dukan alherinsa,

    shi wanda ke gafarta dukan muguntarka, * wanda ke warkad da dukan cututtukanka,

    wanda zai kuɓutad da ranka daga Rami, * wanda zai yi maka rawani da ƙauna da rahama.

    Shi ne wanda zai wadata dauwamarka da kyau, * lokacin da za a sabunta ƙuruciyarka kamar maiki.

        Yahweh ne ke tabbatad da sakamako * da adalci ga dukan waɗanda ke cikin ƙunci.

        Ya gaya wa Musa hanyoyinsa, * ayyukansa kuma ga yayan Israila.

            Yahweh mai tausayi ne da jinƙai—Arahamani Arahimi, * sarkin haƙuri ne da yalwar ƙauna.

            Ba zai yi tankiya ko surutu kullun ba, * ba kuwa zai riƙe hushinsa har abada ba.

                 Ba bisa ga zunubanmu yake yin maamilla da mu ba, * bai ma saka mana gwalgwadon miyagun ayyukanmu ba.

                      Amma kamar yadda sama ke birbishin duniya, * haka ne girman tausayinsa yake ga masu tsoronsa.

                 Kamar yadda gabas ke nesa da yamma, * haka ne yake nesanta kansa daga ayyukan tawayenmu.

            Kamar yadda uba ke tausayin yayansa, * haka ne Yahweh ke jin tausayin masu tsoronsa.

            Domin ya san abin da aka yi mu da shi, * ya tuna mu yamɓu ne kawai.

        Jikan Adamu, kwanakinsa kamar ciyawa ne, kamar furan jeji, haka yake yin zamaninsa.

        Da iska ta kaɗa shi, sai ya shuɗe, * gidansa baya ƙara tunawa da shi.

    Amma ƙaunar Yahweh tun filazal take, * har abada za ta zauna kuma ga masu tsoronsa.

    Alherinsa zai bi jikokin jikoki, * ga waɗanda ke kiyaye yarjejeniyarsa, * suke kuma tunawa da cika kaidondinsa.

    Ko da yake Yahweh ya kafa kursiyinsa a sama, * da sarautarsa yake mulkin komai.

Ku yabi Yahweh, ku malaikunsa, * jarumawa ƙarfafa, ku cika umurninsa, * kuna sauraren muryar maganarsa.

Ku yabi Yahweh, dukan sojojinsa, * da wakilai masu hidima waɗanda ke aikata nufinsa.

Ku yabi Yahweh, dukan ayyukansa, * a dukan wurare, ku talakawansa. * Halelu-Yahweh, ya raina!

Zabura ta 104

Halelu-Yahweh, ya raina!

Yahweh Allahna, kai mai girma ne ƙwarai, * kana yafe da kwarjini da ɗaukaka!

    Kā lulluɓe jikinka da hasken rana kamar riga, * kā warware sammai kamar tanti.

    Shi ne wanda ya tara ruwa a rumbunansa na sama, * yā sa karusansa a kan gajimarai,

yana tafiya da fukafukai miƙaƙƙu, * iska tana kai saƙonsa, * halshen wuta mai ci ne mai hidimarsa,

    wanda ya kafa ƙasa a kan harsashinta, * don ta tsaya daram ba tare da jijjiguwa ba.

    Kā rufe ta da teku kamar riga, * har ruwaye sun tsaya bisa duwatsu.

        Amma da jin tsawarka sun gudu, * da jin ƙarar aradunka sun ranta a noman kare.

    Wasu sun gudu zuwa samar duwatsun, * amma wasu sun gangara zuwa ƙalƙashin ƙasa, * wurin da ka tanada masu.

    Kā sa iyaka da ba za su ƙetare ba, * don kada su sake rufe ƙasa.

        Yā saki idanun ruwa da ƙoramu, * don su riƙa malala a tsakanin duwatsu,

        suna shayar da kowace dabbar jeji, * don jakan daji su jika makwogaronsu.

        Kusa da su tsuntsayen sama ke zama, * daga tsakkiyarsu hankaki suke surutu.

            Yana ba duwatsu ruwa daga rumbunan tara ruwansa na sama, * daga matararsa ƙasa ke wadata da ruwa.

                 Yana sa ganyaye su tsiro don dabbobi, * da ciyawa don shanu masu huɗar gona.

                      I, yana ba da hatsi daga ƙasa, * da abinshan inabi ya faranta zuciyar mutun.

                           I, yana sa fuska mai ƙiba haske, * da abinci yake ƙarfafa zuciyar mutun.

                      An ba itatuwan Yahweh ruwa sosai, * su alul na Labanan waɗanda ya dasa,

                 inda tsuntsaye ke yin sheƙarsu, * shamuwa ita kam, icen fir ne gidanta.

                      Dogayen duwatsu na bareyin daji ne, * kogunan duwatsu kuma na remaye.

                 Wata na canzyawa a kan kari, * rana ta san lokacin da za ta faɗi.

                      Da almuru ya iso, sai dare ya yi, * sannan ne dukan namun jeji ke zagawa.

                           Kuyakuyan zakoki suna ruri don ganimarsu, * suna neman abin sa wa baka daga wurin Allah.

                      Da rana ta fito, sai su janye jiki, * su kwanta a maɓoyunsu.

                 Sai mutun ya fita wurin leburancinsa, * ya dinga huɗa har maraice.

            Yaya yawan aikinka yake, Yahweh! * Da Hikima a gefenka kā yi dukansu, * duniya cike take da halittarka.

        Uban Gidan Teku, * mai tsawo, mai faɗi,

        kai ne ka halicci masu iyo ba iyaka, * rayayyun dabbobi, manya da ƙanana,

        kā yi jirage don tafiya, * da Lawiyatan, wanda ka yi don ka yi wasa da shi:

    Dukansu suna dubanka, * don ka ba su abincinsu a kan kari.

        In ka ba su, sukan tara, * in ka buɗe hannunka, ya Mai Nagarta, sukan wadatu.

        Amma da ka kau da fuskarka, sai su suma, * in ka ɗauke ruhunka, sai su mutu, * su koma yamɓunsu.

    Ka aiko da ruhunka, a sake halittarsu, * ka sabunta fuskar ƙasa.

Bari ɗaukakar Yahweh ta tabbata har abada, * da ma Yahweh ya gamsu da aikinsa!

    Da ya kalli duniya sai ta gigice, * in ya taɓa duwatsu ma suna yin hayaƙi.

    Bari in yi wa Yahweh waƙa duk tsawon rayuwata, * in yabi Allahna matuƙar ina numfashi.

Da waƙata ta shiga kunnensa, * zan yi farinciki da Yahweh.

Bari masu zunubi su ɓace daga duniya, * miyagu ma kada su sake wanzuwa.

Halelu-Yahweh, ya raina!



Zabura ta 105

Ku yi wa Yahweh godiya, ku kira sunansa, * ku sanar da ayyukansa a cikin alummai!

Ku yabe shi, ku raira masa waƙa, * ku wallafa labarun alajibansa.

Ku yi alfahariya da sunansa tsattsarka, * masu neman Yahweh, ku faranta zukatanku.

Ku nemi Yahweh da ikonsa, * kasancewarsa ta dindindin za ku biɗa.

Ku tuna da alajiban da ya yi, * da alamomi da hukuntan da bakinsa ya furta,

ku jikokin baransa Ibrahimu, * da yayan Yakubu zaɓaɓɓensa!

    Gama shi ne Yahweh Allahnmu, * ikonsa yana bisa dukan duniya.

    Yana sane da yarjejeniyarsa har abada, * kaidar da ya ƙulla don tsara biye da tsara har dubu.

    Ya yi ta da Ibrahimu, * ya ma sabunta ta da Isiyaku.

        Domin ya tabbatad da ita ga Yakubu kamar a matsayin sharia, * ga Israila kuwa kamar yarjejeniya ce ta har abada.

        Cewa: Kai zan ba ƙasar, * tuddan Kanana za su zama abin gadonku.

    Saad da ba su da yawa, * baƙi kima ne a cikinta,

    suna yawo daga wannan alumma zuwa wata, * daga wannan sarauta da mutane zuwa wata,

bai bar wani ya zalunce su ba, * saboda su ma har sai ya tsawata wa sarakuna,

ya ce: Kada ku taɓa shafaffen sarkina, * kada kuma ku yi wa annabawana lahani!

    Daga nan sai ya sa aka yi yunwa a ƙasar, * ya karya kowane karan hatsi.

        Ya aike masu da wani mutun, * Yusufu da aka sayar bawa.

        Sun ɗaure ƙafafunsa da marī, * wuyansa kuma ya sha sarƙa,

            sai lokacin da maganarsa ta kai gaban Firaauna, * wanda maganar Yahweh ta tabbata ta wurinsa.

            Ya aika sarki ya sake shi, * shugaban mutane ya ba shi yanci.

                 Ya naɗa shi shugaban fādarsa, * mai sarrafa duk abin da ya mallaka,

                 don ya koya wa fadawansa, * ya koya wa dattawansa hikima.

                      Sannan Israila ya zo Masar, * Yakubu kuma ya baƙunci ƙasar Hamu.

                      Mai Duka ya riɓanɓaya mutanensa, * sun yalwata fiye da abokan hamayyarsu.

                      Ya juye zukatansu su ƙi mutanensa, * su yaudari bayinsa.

                           Sai ya aiko Musa bawansa, * da Haruna wanda ya zaɓa.

                           Sun aikata alamominsa a jeji, * da alamunsa a ƙasar Hamu.

                      Ya aiko duhun da ya duhunta, * ba su iya ganin aikinsa.

                      Ya mai da ruwan shansu jini, * ya karkashe kifayensu.

                 Ya cika ƙasarsu da kwaɗi, * har ɗakunan sarakunansu.

                 Ya yi magana, ya sa ɗumbin kudaje, * da ƙwarƙwata a koina.

            Ya sauko masu ƙanƙara maimakon ruwa, * an yi ta rabka tsawa a ƙasarsu.

            Ya rabke kuringar inabi da itatuwan ɓaurensu, * ya kakkarya itatuwan tuddansu.

        Ya yi magana, ya kawo fara, * ga ɗango nan ba iyaka.

        Sun cinye kowane ganye a ƙasar, * sun kuma cinye amfanin gonakinsu.

    Ya karkashe kowane ɗan fari a ƙasarsu, * kowace yabanyar fari ta haifuwarsu.

Daga nan ya fito da su da azurfa da zinari, * ba wani kumama a cikin kabilunsa.

Masar ta yi murna da tafiyarsu, * domin tsoronsu ya kama su.

    Ya baza gajimare don ya rufe su, * da wuta don ta haskaka daren.

        Sun nema ya kawo masu fakara, * da alkama daga sama ya ƙosad da su.

            Ya buga dutse, ruwa ya malalo, * ya gudano kamar kogi a busasshiyar ƙasa.

        Domin ya tuna da tsattsarkar kaidarsa * da ya yi da Ibrahim baransa.

    Ya zaro mutanensa da murna, * zaɓaɓɓunsa suna tafe suna waƙa.

Daga nan ya ba su ƙasashen alummai, * suka ƙwace har da dukiyar mutane,

muddun suna kiyaye dokokinsa, * da tsare sharioinsa.

Halelu-Yah!



Zabura ta 106

Halelu-Yah!

                      Ku gode wa Yahweh don mai alheri ne, * gama ƙaunarsa har abada ce.

                      Wa ke iya faɗin ikon Yahweh? * ko furta dukan yabonsa?

Albarka ga masu lura da adalci, * da ke aikata gaskiya a kowane lokaci.

    Ka tuna da ni, Yahweh, * da sonka mai ƙarfi, * ka taimake ni da cetonka,

    don in ci arzikin zaɓaɓɓunka, * in ji daɗin murna ta jamaarka, * in kuma yi alfahari da gādonka.

Mun yi zunubi kamar kakanninmu, * mun yi ƙeta da ashararanci.

    Bayan Masar, kakanninmu ba su fahinci alajibanka ba, * sun mance da yawan ƙaunarka.

    Daga Bahar Kyamare ne suka yi wa Maɗaukaki tawaye, * duk da ya cece su saboda sunansa, * don ya sa su kan ikonsa.

        Ya tsawata wa teku, * kyamare ya bushe, * ya sa sun ratsa zurfin sai ka ce tamkar hamada.

        Ya cece su daga hannun maƙiyi, * ya sa sun tsira daga hannun magabci.

        Ruwaye sun rufe abokon gabarsu, * ba ko ɗayansu da ya rage.

        Sannan ne suka gaskanta da maganarsa, * suka yi waƙoƙin yabonsa.

    Nandanan kuwa sai suka mance da ayyukansa, * ba su jira shawararsa ba.

    Sun nuna matuƙar ɓacin ransu a jeji, * suna gwada Allah a hamada.

    Duk da haka ya biya masu bukatarsu, * ya kori yunwa daga maƙogwaronsu.

        Sun yi ƙyashin Musa a sansanin, * da Haruna mai tsabtan nan na Yahweh.

            Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan, * ta kuma binne bangaren Abiram.

            Wuta ce ta babbake ɓangarensu, * harsunan wuta suka lashe mamugunta.

                 Suka mulmula ɗan maraki a Horeb, * suka yi wa sura mai narkewa sujada.

                 Suka musaya addininsu * da kamannin sa mai cin ciyawa.

                      Sun mance da Allah Macecinsu, * da ya yi ayyuka masu girma a Masar,

                      alajibai a ƙasar Ham, * da alamomin bantsoro a Bahar Kyamare.

                           Sai ya ce zai hallaka su, * ba don Musa zaɓaɓɓensa ba,

                           wanda ya tsaya tsaka a gabansa, * yana tausar hushinsa don kada ya hallaka su.

                           Sai suka rena ƙasar da suka nema, * ba su gaskanta da maganarsa ba.

                           Amma suka yi gunaguni a bukkokinsu, * ba su saurari maganar Yahweh ba.

                      Don haka ya ɗauke hannunsa a kansu, * ya tunkuɗa su jeji,

                      ya hargitsa zuriyarsu a cikin alummai, * ya warwatsa su a ƙasashen waje.

                 Suka gama kai da Baal na Feyor, * suka yi bikin bautar matattu.

                 Suka fusata shi da ayyukansu, * sai alloba ta afko masu.

            Sai Finihas ya tashi tsaye ya yi roƙo, * har aka tsai da allobar.

            An sanya wannan ga kirkinsa * daga zamani zuwa zamanu har abada.

        Suka fusata shi a ruwayen Mariba, * sai da Musa ya sha wuya saboda su,

        don sun yi wa ruhunsa tawaye, * sai ya faɗi abin da bai kamata ba.

    Ba su hallaka mutanen ba, * yadda Yahweh ya umurce su.

    Amma sun aurayya da alummai, * suna koyon aladunsu.

        Sun kuma bauta wa gumakansu, * da suka zamam masu tarko.

        Suna miƙa yayansu maza * da mata ga aljanu.

        Suna zub da jinin adalai, * jinin yayansu maza da mata,

        da suka yanka wa gumakan Kanana, * suka ƙazanta ƙasar da jini mai yawa.

        Sun ƙazanta kansu da ayyukansu, * suna yin zina wajen bajirewarsu.

    Sannan hushin Yahweh ya yi ƙuna a kan jamaarsa, * sai ya ƙi abin gādonsa.

    Ya bashe su a alummai, * don maƙiyansu su mulke su.

    Magabtansu sun matsa masu lamba, * sai da suka ƙasƙantu a hannunsu.

Sau da yawa ya cece su, * amma kuma suna ci gaba da taurin kansu * sai da mugun nufinsu ya komo masu.

    Sai dai ya tausaya wa ɓacin ransu, * yana jin kukansu.

    Ya tuna yarjejeniyarsa da su, * yana bi da su da yalwar alherinsa.

Ya ba su rahamomi masu yawa, * a gaban dukan iyayengijinsu.

Ka cece mu, Yahweh Allahnmu, * ka tattaro mu daga alummai,

don mu gode wa sunanka mai tsarki, * mu ɗaukaka shi ta yabonka.

Yabo ga Yahweh Allah na Israila, * tun filazal har abada! * Bari dukan mutane ma su ce, Amin.

Halelu-Yah!

Zabura ta 107

Ku gode wa Yahweh domin mai alheri ne, * gama jinƙansa har abada ne.

Bari kuɓutattun Yaweh su ce, * shi ne ya kuɓutad da su daga hannun mai zalunci.

Ya fid da su daga ƙasashen waje, * daga gabaci da yammaci, * daga arewaci da kuma tekun kudu.

    Sun yi yawa a jeji, * ta hamada ne suka bi, * amma ba su ga garin zama ba.

    Sun ji yunwa da ƙishinruwa, * kamar ransu zai fita.

        Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

        Ya bi da su ta miƙaƙƙar hanya, * sai da suka kai birnin da za su zauna ciki.

    Bari su buɗe baki su yabi jinƙan Yahweh, * alajibansa kuma ga yan adan,

    domin ya ƙosad da maƙoshi mai jin ƙishinruwa, * ya ma ci da mayunwacin maƙogwaro da abubuwa masu kyau.

        A game da mazauna cikin baƙin duhu, * da ke ɗaure da marurai masu azaba,

        domin sun tayar wa umurnan Allah ne, * sun shure shawarar Maɗaukaki,

        ya shawo kansu da wahala, * sun yi ta tuntuɓe, ba mataimaki.

            Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

            Ya fito da su daga baƙin duhu, * ya karkatsa sarƙoƙinsu.

        Bari su buɗe baki su yabi jinƙan Yahweh, * alajibansa kuma ga yan adan.

        Domin ya tsintsinke ƙofofin janƙarfe, * mulmulallun ƙarafa yana yin gunduwa da su.

            Ba su da kuzari don tawayensu, * sun shiga uku don ƙetar da suka yi.

            Maƙogwaronsu ya ƙi kowane irin abinci, * har sun kai gab da ƙofofin Mutuwa.

                 Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

                 Ya aiki maganarsa tana warkad da su, * tana warkad da maruransu.

            Bari su buɗe baki su yabi jinƙan Yahweh, * alajibansa kuma ga yan adan.

            Bari su miƙa hadayun godiya, * suna ƙidaya alherinsa da waƙar farinciki.

        Game da masu tafiya bahar da jirage, * suna kasuwanci hayin manyan ruwaye,

            sun ga ayyukan Yahweh, * da alajibansa a ruwa mai zurfi.

                  Ya yi umurni, iska ta taso, * da hadari wanda ya ɗaga raƙuman ruwansa.

            Sun yi sama, sun kuwa sauka zurfafa, * bakinsu ya yi rawa saboda hatsarin.

        Sun kai sun kawo, suna tangaɗi kamar bugaggu, * gwanintarsu duk ta zama ta banza.

            Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

            Ya sa hadiri ya yi shuru, * ya kwantad da motsin raƙuman ruwa.

            Sun yi murna da wurin ya yi tsit, * da ya yi masu jagora zuwa wurin kasuwancinsu.

        Bari su buɗe baki su yabi jinƙan Yahweh, * alajibansa kuma ga yan adan.

        Bari su ɗaukaka shi a taron jamaa, * a majalisar dattawa kuma su yabe shi.

    Ya sa koguna sun zama daji, * idanun ruwa sun bushe ƙayau,

    ƙasa mai niima ta koma hamada mai kanwa, * don ƙetar mazauna wurin.

        Ya sa jeji ya zama tabkunan ruwa, * busasshiyar ƙasa ta koma kandami.

            Ya zaunad da mayunwata a wurin, * sun ma kafa garin zama.

                 Sun shuka gonaki, * sun dasa garkar inabi, * sun yi girbi mai matuƙar yawa.

            Ya yi masu albarka, sun ma yawaita ƙwarai, * bai rage yawan garkunan shanunsu ba.

        Amma ya sassafta masu, ya kau da * zalunci da hatsari da ɓacin rai.

    Mai jibga wa sarakuna wulakanci, * mai sa su su yi yawo a hamada da ba hanya,

    ya kare mabukaci a ƙasarsa, * ya ninka kabilansu kamar tumaki.

Bari masu gaskiya su gani su ji daɗi, * duk mugu kuwa ya yi tsit.

Duk mai hikima zai yi laakari da abubuwan nan, * zai kuma yi tunani da yawan jinƙan Yahweh.

Zabura ta 108

Na shirya zuciyata, ya Allah,* zan yi waƙa in yabe ka.

Ki falka, zuciyata! * Ku falka, molona da garayata! * Zan farkad da safiya!


Zan gode maka a cikin jamaa, Yahweh, * zan yabe ka a cikin alummai, ya Mai Girma.

Domin ƙaunarka tana birbishin sammai, * amincinka kuma ya kai har sararin sama.

    Tsawonka ya kere sammai, ya Allah, * ɗaukakarka kuma ta shafe dukan duniya.

    Don a kuɓutad da ƙaunatattunka, * ka ba ni rinjaye da nasara da hannunka na dama.

        Allah ya faɗa daga tsattsarkan gidansa, * Zan raba Shakem, * in kuma auna kwarin Sukkot.

        Gileyad nawa ne, har da na Manassa, * Ifraimu ne hular kwanona, * Yahuda kuma sandan sarautata.

        Mowab ne bangajin wankina, * a kan Edom ne zan aza takalmina, * a Filistiya zan yi kirarin nasara.

    Wa zai kai ni Birnin Mafaka? * Wa zai ba ni gadon Edom?

    Amma kai, ya Allah, za ka husata da mu? * ba za ka sake fita da sojojinmu ba?

Ka yanta mu daga abokin gaba, * tun da yake taimakon mutane banza ne.

Da ikon Allah za mu ci nasara, * shi ne zai tattake magabtanmu.

Zabura ta 109

Ya Allahna, * kada ka bebanta ga waƙata.

    Domin bakin miyagu * da bakin mayaudara * duk sun wo mani caa.

        Suna yanka mani ƙarya da halshensu, * da kalmomin ƙiyayya kuma suna kewaye ni.

        Suna yaƙina ba dalili, * maimakon ƙauna da nike masu * suna yin tsegumi.

    Suna zargin adduar da nike yi masu, * suna rama mani alheri da mugunta, * ƙiyayya da soyayyata.

        Ka ɗora Mugun a kansa, * bari Sheɗan ya tsaya a hannun damansa.

        In ana yi masa sharia, a same shi da laifi, * adduarsa kuma ta zama wani laifin.

        Kwanakinsa su gaza, * wani ya ɗauki matsayinsa.

            Yayansa su zama marayu, * matarsa kuwa gwauruwa.

            Yayansa su yi yawon bara, * mai aunawa ya ƙayyade kuɗin gidansa.

        Mai bin bashi ya ƙwace dukan kayansa, * baƙi kuma su wawashe amfaninsa.

        Kada kowa ya yi masa alheri, * ko ya ji tausayin marayun yayansa.

            A hana shi madauwamin rai, * a kuwa goge sunansa daga zamani mai zuwa.

                 Bari a rubuta zunubin ubansa * wurin Allah Yahweh, * kada a shafe zunubin uwarsa.

                 Waɗannan zunubai su kasance a gaban Yahweh kullun, * loton da yake shafe tunawa da shi a duniya,

                 tun da baya tunanin nuna ƙauna, * sai baƙantawa gajiyayye da mabukaci, * har yana kashe mai ɓacin zuciya.

                      Tun da yana so laana, * ta koma kansa.

                      Tun da yana ƙin albarka, * ta yi nesa da shi.

                 Ya sa laana kamar kaftani, * ta kuwa ratsa jikinsa kamar ruwa, * kamar mai ta game ƙasusuwansa.

                 Bari ta zama kamar tufar da ta lulluɓe shi, * kamar ɗamarar da ta ɗaure shi kullun.

            Ka ƙara kunyar matseguntana * sau ɗari, Yahweh, * da ta masu yi mani baƙar magana.

        Sai ka zo, Yahweh Ubangijina, * ka aika alajibi domina, * saboda sunanka managarci.

        Da alherinka ka cece ni, * domin ni gajiyayye ne mabukaci, * a cikina kuma zuciyata ta soku.

            Na yi kama da inuwa dab da faɗin rana, * ina ta wucewa, * ƙuruciyata ta kare, na tsufa.

            Gwiwowina sun yi sanyi saboda hana kai abinci, * dā ni ƙosasshe ne, amma yanzu na rame.

            Ga masu zuwa wurina * na zama abin zagi, * da sun gan ni sai su kaɗa kai.

        Ka taimake ni, Yahweh Allahna, * ka cece ni yadda ya dace da ƙaunarka,

        don su san wannan aikin hannunka ne, * wanda kai, Yahweh, ka aikata.

    Bari su laanta, * in dai kana sa albarka.

    In sun yunƙuro su ƙasƙanta, * amma bawanka ya yi farinciki.

    Bari matseguntana su sa kaftanin wulakancinsu, * su rufe kansu da kunya kamar mayafi.

Zan yabi Mai Girma da bakina, * a tsakkiyar dattawa zan yabe shi,

domin yana tsaya wa hannun daman mabukaci, * don ya cece shi daga alkalin.

Zabura ta 110

Yahweh ya ce da ubangijina,

Zauna a kursiyin dama da ni. * Na mai da magabtanka kujera, * matashin ƙafafunka.

    Ya ƙera sandarka mai nasara, * Yahweh na Sihiyona ya koɗa ta.

    Shi Ikonka ne a cikin yaƙin magabtanka, * Ƙarfinka kuma a ranar nasararka.

    Tsattsarkan Mai Tallafinka ya bayyana, * Asubahin rayuwarka * Raɓar ƙuruciyarka.

        Yahweh ya rantse, * ba ma zai canza nufinsa ba:

            Kai firist ne na Madauwami, * bisa ga alkawalinsa,

        hakikantaccen sarkinsa, ubangijina, * yadda hannun damanka ya shaida.

    Ya runtumi sarakuna a ranar hushinsa, * ya karya alummai.

    Ya jibge gawarwaki, * ya rafke kawuna * a bisa ƙasa mai fāɗi.

Mai Zaɓen Sarakuna ya naɗa shi, * Maɗaukakin Zati ya ɗaga matsayinsa.

Zabura ta 111

Halelu-Yah!

Zan yi godiya ga Yahweh * da dukan zuciyata * a majalisar masu gaskiya da cikin taron jamaa.

    Ayyukan Yahweh manya ne, * don duk masu jin daɗinsu su yi binbininsu.

        Ayyukansa suna da girma da ɗaukaka, * alherinsa na ɗorewa har abada.

        Ya yi alajiban da ba za a manta da su ba, * shi ne Yahweh Arahamani Arahimi.

            Yana ba masu tsoronsa abinci, * ya tuna da yarjejeniyarsa ta tuntuni.

            Ta ayyukansa yake nuna wa jamaarsa ikonsa, * yana ba su gallar alummai.

        Ayyukan hannuwansa su ne gaskiya da aminci, * dukan dokokinsa amintattu ne.

        Sun kafu tuntuni har abada, * bisa tushen gaskiya da aminci.

    Ya aika fansa ga jamaarsa, * ya kafa yarjejeniyarsa har abada, * sunansa tsattsarka ne da mai bantsoro.

Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, * duk masu nemanta sun fainci Mai Nagarta.

Bari a yabe shi har abada!

Zabura ta 112

Halelu-Yah!

Albarka ga mai tsoron Yahweh, * wanda ke jin daɗin umurnansa.

Zuriyarsa za ta yawaita a ƙasar, * gidan mai gaskiya zai yi albarka.

    Akwai wadata da dukiya suna gidansa, * alherinsa zai ɗore har abada.

    Ga masu gaskiya, a cikin Duhu, Ranar Asuba za ta keto, * ta Mai Jinƙai, Mai Tausayi, Mai Adalcin nan.

        Mutumin kirki baya hana rance, * yana yin alamuransa da adalci.

        Ba zai taɓa yin tuntuɓe ba, * za a riƙa tuna mai gaskiya har abada.

    Baya jin tsoron mugun labari, * zuciyarsa ba ta falgaba, don yana dogara ga Yahweh.

    Ba falgaba a zuciyarsa, baya jin tsoro, * yana murna kullun, yana yi wa magabtansa dariya.

Yana ba mabukata hannu sake, * alherinsa na ɗorewa, * za a ƙara masa girma da mutunci.

Mugu yana yin kallon kishi da ɓacin rai, * yana cizon haƙoransa da kuka, * gidajen miyagu za su warwaje.

Zabura ta 113

Halelu-Yah!

Ku yabi ayyukan Yahweh, * ku yabi sunan Yahweh.

Yabo ga sunan Yahweh, * daga yanzu har abada!

Yabo ga sunan Yahweh, * daga fitowar rana zuwa faɗuwarta!

    Yahweh ne saman dukan alummai, * bisa sammai ɗaukakarsa take.

        Wa ke kama da Yahweh Allahnmu, * da ke da kursiyi a sama,

    wanda ke karkatowa daga sama * don ya duba ƙasa.

Yana ɗaga matalauci daga turɓaya, * daga juji yake ta da mabukaci,

don ya zaunad da shi tare da sarakuna, * i, da sarakunan jamaarsa.

Yakan ba mara yaya gida, * ta zama uwar yaya cike da murna.

Zabura ta 114

Bayan fitowar Israila daga Masar, * Yakubu daga masu ƙeta,

ƙasar Yahuda ta zama tsttsarkan wurinsa, * Israila kuma abin mulkinsa.

    Tekun Araba ya gan shi, ya gudu, * Kogin Urdun ya koma da baya.

    Duwatsu sun yi tsalle kamar raguna, * tuddai kuma kamar yayan bareyi.

    Me ya same ka, ya Teku, har ka gudu? * Urdun, don me ka ja da baya?

    Ku duwatsu, don me kuke yin tsalle kamar raguna? * ku ma tuddai kamar awaki?

Ki yi makyarkyata, ƙasa, a gaban Ubangiji, * da zuwan Allah na Yakubu,

wanda ke canza dutse zuwa tafkin ruwa, * da maƙyashi zuwa maɓuɓɓugan ruwa.

Zabura ta 115

Ba don halinmu ba, Yahweh, * ba don halinmu ba,

    amma don sunanka * ka nuna ɗaukakarka,

    saboda ƙaunarka, * da amincinka,

don kada alummai su ce, * Ina Allahnsu yake?

    Ko da shi ke Allahnmu a sama yake, * yana yin duk abin da ya ga dama.

    Gumakansu su ne azurfa da zinariya, * aikin hannuwan mutun.

        Suna da baki, amma ba sa magana.

            Suna da idanu, amma ba sa gani.

            Suna da kunnuwa, amma ba sa jin murya.

                 Suna da hanci, amma ba sa jin ƙamshi.

                 Suna da hannuwa, amma ba sa taɓawa.

            Suna da ƙafafu, amma ba sa tafiya.

            Ta maƙogwaronsu, ba sa iya yin amo.

        Masu yinsu za su zama kamarsu, * da kowa da ya dogara da su.

            Ya Israilawa, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

            Ya gidan Haruna, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

            Masu tsoron Yahweh, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

        Yahweh ya yi wa kursiyimmu albarka,

            ya yi wa gidan Israila albarka,

            ya yi wa gidan Haruna albarka.

                 Ya yi wa masu tsoronsa albarka,

                 manya duk da ƙanana.

            Yahweh ya riɓanɓanya ku,

            ku da yayanku.

        Yahweh ya yi maku albarka, * wanda ya yi sama da ƙasa.

    Birbishin sama na Yahweh ne, * amma ya ɗora yan adan bisa duniya.

    Matattu ba sa yabon Yahweh, * ko dukan masu gangara wa Kurkuku.

Amma mu za mu yabi Yahweh, * daga yanzu har abada.

Halelu-Yah!


Zabura ta 116

Saboda ƙaunar Yahweh gare ni, * ya ji roƙona don jinƙai.

I, ya kasa kunne gare ni, * lokacin da nike kira.

    Igiyoyin Mutuwa sun nannaɗe ni, * jakadun Shawol sun same ni.

    Da damuwa da ɓacin rai sun same ni, * amma na kira sunan Yahweh:

        Ina cewa, Ina roƙonka, Yahweh, * ka fanshi raina.

    Arahamani, shi ne Yahweh mai gaskiya, * Allahna Arahimi ne.

    Yahweh ne mai kiyaye mai sauƙin kai, * an ƙasƙanta ni, amma ya cece ni.

        Ka koma wurin hutunka, ya raina, * gama Yahweh ya kyauta maka.

        Gama an fanso ka daga Mutuwa, ya raina, * idona daga Hawaye, * ƙafata kuma daga gudun Hijira.

            Zan yi tafiya a gaban Yahweh * a Lambun Rayayyu.

        Na yi aminci ko da yake an runtume ni, * ko da yake Masifa tana wulakanta ni.

        Saboda tunzurina na zaci, * Kowane mutun maƙaryaci ne.

    Ta yaya zan mayas wa Yahweh * da dukan alherin da yake yi mani?

    Zan ɗauki ƙoƙon ceto, * in yi kira da sunan Yahweh.

    Zan cika waadodina ga Yahweh * a gaban dukan jamaarsa.

        Mutuwar masu bauta wa Yahweh * babbar daraja ce a gare shi.

    Hakika, Yahweh, * ni bawanka ne.

    I, ni bawanka ne, * amintataccen ɗanka, * ka kwance mani ɗaurina.

    Yahweh, zan miƙa maka hadayar godiya, * ina kiran sunanka.

Zan cika waadodina gun Yahweh, * a gaban dukan jamaarsa,

a farfajiyun gidan Yahweh, * a tsakkiyar Birnin Ƙudus.

Halelu-Yah!



Zabura ta 117

Ku yabi Yahweh, dukan alummai, * ku ɗaukaka shi, ku dukan malaiku.

Gama ƙaunarsa gare mu da girma take, * amincin Yahweh har abada ne.

Halelu-Yah!



Zabura ta 118

Ku yabi Yahweh mafi nagari, * ƙaunarsa har abada ce.

    Bari Israila ya ce, * Ƙaunarsa har abada ce.

    Bari gidan Haruna ya ce, * Ƙaunarsa har abada ce.

Bari masu tsoron Yahweh su ce, Ƙaunarsa har abada ce.

    Daga bakin Kurkuku na kira Yahweh, * ya ji ni daga sararin sama.

Yahweh na tare da ni, bana jin tsoro, * menene mutun ya iya yi da ni?

    Yahweh na tare da ni, Babban Jarumina, * zan ga bayan magabtana.

    Gwamma neman mafaka wurin Yahweh * da dogara ga mutun.

Gwamma neman mafaka wurin Yahweh * da dogara ga sarakuna.

    Dukan alummai sun kewaye ni, * amma da sunan Yahweh na mai da loɓarsu abin tarihi.

    Sun matsa mani lamba, * amma da sunan Yahweh na mai da loɓarsu abin tarihi.

    Sun yayyaɓe ni kamar ƙudan zuma, * amma da sunan Yahweh na mai da loɓarsu abin tarihi.

        Ka angaje ni don in faɗi, * amma Yahweh ya taimake ni.

        Yahweh mafakata ne da marayata, * yana sa ni cin nasara.

            Daga alfarwar masu nasara * ana ta yin sowar bangirma.

            Hannun dama na Yahweh ya yi nasara, * hannun daman Yahweh ya sami ɗaukaka, * hannun dama na Yahweh ya yi nasara.

        Ban mutu ba, amma na rayu, * don in ba da labarin ayyukan Yahweh.

        Yahweh ya yi mani horo mai tsanani, * amma bai sallama ni ga Mutuwa ba.

    Ku buɗe mani ƙofofin nasara, * zan shiga in yabi Yahweh.

    Ƙofar ta Yahweh ce, * sai maciya nasara su shiga.

Na gode maka saboda rinjayena, * kā ba ni nasara.

    Dutsen da magina suka ƙi * shi ne ya zama harsahin gini.

    Wannan aikin Yahweh ne, * abin mamaki ne kuma a idanunmu.

Yahweh ne ya yi ranan nan, * mu yi murna, mu yi farinciki da shi.

    Muna roƙonka, Yahweh, ka ba mu nasara, * muna roƙonka, Yahweh, ka ba mu arziki.

Albarka ga wanda ya shiga da sunan Yahweh, * muna yi maka albarka a gidan Yahweh, * Allah Yahweh ya haskaka mu.

    Ku daza rassa a masujada, * ku yi wa ƙahonin bagadi ado.

    Kai ne Allahna, na gode maka, * ya Allahna, ina ɗaukaka ka.

Ku yabi Yahweh mafi nagarta, * ƙaunarsa har abada ce.

Zabura ta 119

1-8 a

Masu albarka ne kammalallu a hanyarsu, * suna tafiya bisa ga shariar Yahweh.

Masu albarka ne waɗanda ke riƙe sharaɗunsa, * suna binsa da dukan zuciyarsu.

Basa yin mugunta, * amma suna bin hanyoyinsa.

Kā yi doka * a kiyaye umurnanka da himma.

Inā ma a ce an daidaita hanyata * don in kiyaye kaidondinka.

Sannan ba zan ji kunya ba * zan fuskanci dukan dokokinka.

Ina yabon ka saboda adalcin zuciyarka, * lokacin da nike koyon hukuntanka.

Zan kiyaye kaidodinka, * ya Madauwamin Mai Girma, * kada ka yashe ni.

9-16 b

Ta yaya saurayi zai zauna da tsarki? * Ta yin tafiya bisa ga maganarka.

Ina nemanka da dukan zuciyata, * kada ka bari in bauɗe wa dokokinka.

Ina riƙe alkawalinka a zuciyata, * don kada in yi maka zunubi.

Albarka gare ka, Yahweh! * Ka koya mani kaidodinka.

Da leɓunana nike shelar * dukan kalmomin da bakinka ke faɗi.

Ina jin daɗin bin sharaɗunka, * fiye da dumbin wadata.

Ina ta yin nazarin umurnanka, * ina bimbinin hanyoyinka.

Ina jin daɗin kaidodinka, * ban taɓa manutuwa da kalmominka.

17-24 g

Ka kyauta wa bawanka don in rayu, * in kuma kiyaye maganarka.

Ka buɗe idanuna don in kalli * alajiban shariarka.

Baƙo ne ni a duniya, * kada ka ɓoye mani dokokinka.

Raina yana jira da dokin * hukuntanka a kullun.

Ka tsawata wa laanannun masu izgilanci, * da ke bauɗe wa dokokinka.

Ka ɗauke mani zargi da wulakanci, * domin ina kiyaye sharaɗunka.

Duk da yake yan iska na zaune suna yi da ni, * bawanka yana tunani a kan kaidodinka.

Sharaɗunka suna faranta mani rai, * su ne ma mashawartana.

25-32 d

Wuyana yana manne wa ƙura, * ka raya ni bisa ga alkawalinka.

Na ba da labarin tafarkinka, kana saurarena, * ka koya mani kaidodinka.

Ka sa in gane hanyar umurnanka, * don yin nazarin alajibanka.

Ina ruɗewa don ɓacin rai, * ka agaje ni bisa maganarka.

Ka raba ni da hanyar ƙarya, * ta wurin shariarka ka yi mani jinƙai.

Na zaɓi hanyar gaskiya, * ina girmama hukuntanka.

Na manne wa sharaɗunka, * Yahweh, kada ka kunyata ni.

Zan tsere a kan hanyar dokokinka, * in ka fāɗaɗa fahintata.

33-40 h

Ka koya mani hanyar kaidodinka, * Yahweh, * don in kiyaye su kamar dukiya.

Ka ba ni hangen nesa don in kiyaye shariarka, * in kuwa bi ta da dukan zuciyata.

Ka bi da ni cikin dokokinka, * domin ina jin daɗinsu.

Ka juya zuciyata ga sharaɗunka, * ba ga ribar cuta ba.

Ka kau da idanuna daga kallon gumaka, * ka raya ni da ikonka.

Ka cika alkawalinka ga bawanka, * don a gaskiya ina jin tsoronka.

Ka kau da zargina domin ina girmama ka, * gama hukuntanka nagargattu ne.

Dubi yadda nike marmarin umurnanka, * ka raya ni da adalcinka.

41-48 w

Yahweh, bari ƙaunarka ta zo mani,* cetonka kuma bisa ga alkawalinka.

Zan ba da amsa ga mai zargina, * don na dogara ga maganarka.

Kada ka kauda zancen gaskiya daga bakina, * ya Madauwami Mai Girma! * Ina jiran umurnanka.

Ka sa in bi shariarka, * ya Madauwami, * har abada.

Bari in yi tafiya da yanci, * lokacin da nike bin umurnanka.

Bari in yi shelar sharaɗunka * a gaban sarakuna, * ba tare da jin kunya ba.

Ina jin daɗin dokokinka, * waɗanda na ƙauna ne.

Zan ɗaga hannuwana * bisa ga dokokinka da nike ƙauna, * ina yin nazari kuma a kan kaidodinka.

49-56 z

Ka tuna da maganarka ga bawanka, * wadda ka sa in sa zuciya a gare ta.

Wannan ita ce taaziya cikin wahalata, * domin maganarka ke raya ni.

Masu izgilanci suna yi mani baa, * ya Madauwami Mai Girma, * amma ban kauce daga shariarka ba.

Da nike tunawa da hukuntanka na tuntuni, * Yahweh, na taazantu.

Na hassala * saboda miyagun da ke ƙyale shariarka.

Kaidodinka sun zama matserata * a cikin gidan da nike baƙunci.

Da dare ina tunawa da sunanka, * Yahweh, * shariarka kuma da goshin asuba.

Na zama abin cin mutunci, * domin ina riƙe da umurnanka.

57-64 x

Yahweh Mahaliccina, na alkawalta * bin dokokinka.

Na nemi alherinka da dukan zuciyata, * ka tausaya mani bisa ga alkawalinka.

Da na yi tunanin hanyoyinka, * sai na maida matakaina ga sharaɗunka.

Na yi hamzari, ba da jinkiri ba, * don bin dokokinka.

Duk da taron miyagu ya kewaye ni, * ban manta da shariarka ba.

Da tsakar dare nike tashi don in gode maka, * domin hukuntanka na gaskiya.

Ni ne abokin dukan masu tsoronka, * da dukan masu bin umurnanka.

Duniya cike take da ƙaunarka, * Yahweh, * ka koya ni kaidodinka.

65-72 j

Yahweh, ka yi wa bawanka alheri, * bisa ga maganarka.

Ka koya mani ilimi da hikima, * domin na gaskanta da dokokinka.

Kafin in sha wuya, na bauɗe, * amma yanzu ina kiyaye kalmarka.

Kai nagari ne, kana kuma nagartawa, * ka koya mani kaidodinka.

Masu izgilanci suna ɓata sunana da ƙarairayi, * amma ni, da dukan zuciyta nike kiyaye umurnanka.

Zuciyarsu ta daskare kamar kitse, * ni kuwa ina jin daɗin shariarka.

Ya yi kyau da na sha wahala, * domin in koyi kaidodinka.

Shariar bakinka tana yi mani kyau * fiye da ɗumbin azurfa da zinariya.

73-80 y

Hannuwanka ne suka yi ni, suka sifanta ni, * ka ba ni basira don in koyi dokokinka.

Masu tsoronka za su gan ni, su yi farinciki, * domin ina jiran maganarka.

Yahweh, na sani * kai adili ne wajen hukuntanka, * ka tsananta mani kan gaskiya.

Bari ƙaunarka ta zama taaziya a gare ni, * bisa ga alkawalinka ga bawanka.

Bari rahamominka su zo guna don in rayu, * domin shariarka tana sa in ji daɗi.

Bari masu izgilanci su kunyata, * sun so su karkata ni ta yaudara, * amma ni na yi nazarin umurnanka.

Bari masu tsoronka su juyo mani, * don su san sharaɗunka.

Bari zuciyata ta zama kamila game da kaidodinka, * don kada in kunyata.

81-88 k

Raina ya ɗokanta ga begen cetonka, * ina ta jiratan maganarka.

Idanuna sun gaji suna ta jiran kalmarka, * har ina cewa, Yaushe za ka sanyaya mani rai?

Gama na zama kamar mai kuka saboda hayaƙi, * duk da haka ban mance kaidodinka ba.

Nawa ne kwanakin bawanka? * Yaushe ne za ka yi wa masu tsananta mani hukunci?

Masu girman kai sun haƙa mani ramu, * ba su kula da shariarka ba.

Dukan dokokinka gaskiya ne, * amma suna tsananta mani da ƙarya, ka agaje ni.

Sun kusa hallaka ni a duniya, * amma ni ban yi watsi da umurnanka ba.

Saboda ƙaunarka ka kare raina, * don ina bin sharaɗun da ka faɗi.

89-96 l

Yahweh, kalmarka madauwamiya ce, * ta tabbata fiye da sammai.

Gaskiyarka ta tabbata daga tsara zuwa tsara, * ta kafu fiye da ƙasa.

Ta hukuncinka ta tabbata har kwanan gobe, * domin dukan abubuwa bayinka ne.

Da shariarka ba ita ce daɗina ba, * da na hallaka saboda wahaluna.

Har abada ba zan mance da umurnanka ba, * domin ta wurinsu kake raya ni.

Naka ne ni, ka cece ni, * domin ina bin umurnanka.

Miyagu sun fake domin su hallaka ni, * amma ni ina nazarin sharaɗunka.

Fiye da dukan alajiban da na taɓa gani, ya Ƙarshe, * dokarka ta rungumi kome, ya Mai Girma.

97-104 m

Dubi yadda nike ƙaunar shariarka, * ita ce nike nazari kanta wuni zubut.

Dokokinka sun mai da ni mai hikima fiye da magabtana, * domin suna tare da ni har abada.

Ganewata ta fi ta dukan malamaina, * domin nikan yi nazarin sharaɗunka.

Na fi tsofaffi hikima, * domin na riƙe umurnanka.

Na hana ƙafafuna bin kowace irin muguwar hanya, * don in bi maganarka.

Ban goce daga hukuntanka ba, * domin kai ne ka koya mani.

Kalmarka tana da daɗin ɗanɗano, * kamar zuma take a bakina!

Ta wurin umurnanka nike samun basira, * Maɗaukakin Zati, * ina ƙin dukan hanya ta ƙarya.

105-112 n

Maganarka fitila ce ga ƙafafuna, * da haske a kan hanyata.

Na rantse zan ci gaba * da bin hukuntanka masu gaskiya.

Azabata ta kai Masifa, * Yahweh, ka raya ni bisa ga maganarka.

Yahweh, ka faranta raina da jawabi mai daɗi, * ka koya mani hukuntanka.

Raina yana hannunka, ya Madauwami, * don haka bana mance shariarka.

Miyagu suna ɗana mani tarko, * amma ban goce daga umurnanka ba.

Na yi gadon sharaɗunka, ya Madauwami, * i, su ne ke faranta mani zuciya.

Na juya zuciyata in aikata kaidodinka, * ladana zai zama na har abada.

113-120 s

Na tsargi masu zuciya biyu, * amma ina son shariarka.

Kai ne Makarina da Shugabana, * ina ta jiran maganarka.

Ku rabu da ni, ku miyagu, * don in kiyaye dokokin Allahna.

Ka tallafa mani bisa ga alkawalinka, don in rayu, * kada ka bari in kunyata ga sazuciyata.

Ka rungume ni don in kuɓuta, * in girmama kaidodinka, ya Madauwami.

Ka yi juji na dukan masu bauɗe wa kaidodinka, * domin bautar gumakansu banza ce.

Kā yas da dukan miyagun duniya kamar sharā, * saboda haka nike son sharaɗunka.

Jikina yana rawa saboda tsoronka, * ina tsoron hukuntanka.

121-128 Ɗ

Ka kare hakkina na gaskiya, * kada ka bar ni ga masu tsananta mani.

Ka ba bawanka tabbaci, ya Managarci, * don kada masu girman kai su zalunce ni.

Idanuna suna begen cetonka, * da kuma alkawalinka na gaskiya.

Ka aikata wa bawanka alherinka, * ka koya mani kaidodinka.

Ni bawanka ne, ka ba ni ganewa, * domin in san sharaɗunka.

Lokacin aikatawa ya yi, Yahweh, * sun banzata shariarka.

Maɗaukakin Zati, * ina ƙaunar dokokinka * fiye da zinari komi kyansa.

Maɗaukakin Zati, * ina gaskanta dukan umurnanka, * na tsargi kowane irin rashin gaskiya.

129-136 p

Sharaɗunka masu banmamaki ne, * ya Maɗaukakin Zati, ina bin su.

Ka buɗe hasken maganarka, * ka ba marasa sani ganewa.

Ina haki da baki buɗe, * domin ina ɗokin dokokinka.

Ka juyo gare ni, ka ji tausayina, * yadda kakan yi wa masu son sunanka.

Ka kafa sawayena a kalmarka, * kada ka bari mugunta ta rinjaye ni.

Ka fanshe ni daga zaluncin yan adan, * don in bi umurnanka.

Ka sa fuskarka ta haskaka bawanka, * sannan ka koya mani kaidodinka.

Idanuna suna zub da ƙoramun hawaye, * ya Maɗaukaki, ba su kiyaye shariarka ba.

137-144 c

Kai mai gaskiya ne, Yahweh, * mai adalci kuma a cikin hukuntanka.

Ka umurci sharaɗunka da gaskiya * da aminci, ya Mai Girma.

Abokan hamayyata suna so su hallaka ni, * magabtana ba su kula da dokokinka ba.

An gwada kalmarka, * ya Maɗaukaki, * bawanka kuma yana ƙaunarta.

Ko da nike matashi renanne, * ban mance da umurnanka ba.

Adalcinka na gaskiya ne, * ya Madauwami, * shariarka kuma ta hakikanta.

Duk da ina cikin wahala da damuwa, * ina jin daɗin dokokinka.

A game da hakikancin sharaɗunka, * ya Madauwami, * ka ba ni ganewa don in rayu.

145-152 q

Na yi kira da dukan zuciyata, * ka amsa mani, Yahweh, * don in kiyaye kaidodinka.

Ina kiranka, ka cece ni, * don ina bin sharaɗunka.

Da sassafe na dube ka da kukan neman taimako, * ana jiran maganarka.

Na raba dare ina zuba idanu gare ka, * da nike nazari akan alkawalinka.

Cikin alherinka ka ji muryata, * Yahweh, * da adalcinka ka kiyaye raina.

Masu bautar gumaka suna matsowa, * sun yi nesa da shariarka.

Amma kai ne Makusanci, Yahweh, * dukan dokokinka kuma gaskiya ne.

Ya Farko, na yarda da sharaɗunka, * domin ka kafa su tuntuni.

153-160 r

Ka dubi wahalata, ka cece ni, * domin ban mance da shariarka ba.

Ka bi hakkina, ka fanshe ni, * bisa ga alkawalkinka ka raya ni.

Ka nisanta miyagu da cetonka, * domin basa bin kaidodinka.

Rahamominka masu yawa ne, Yahweh, * bisa ga hukuntanka ka raya ni.

Duk da matsanantana da abokan gabata sun yi yawa, * ban bauɗe daga sharaɗunka ba.

Na dubi maciya amana, na ji ƙyama, * domin ba sa kiyaye maganarka.

Dubi yadda nike son umurnanka, * Yahweh, a cikin alherinka ka raya ni.

Cibiyar maganarka ita ce gaskiya, * ya Madauwami, * hukuncinka kuma adalci ne.

161-168 v

Yan iska suna tsananta mani ba dalili, * zuciyata kuma ta firgita da masu bina.

Na yi murna da kalmarka, * domin maganarka babbar riba ce gare ni.

Na tsargi ƙarya, na ƙi ta, * amma ina ƙaunar shariarka.

Ina yabonka sau bakwai kowace rana, * saboda hukuntanka masu gaskiya.

Akwai babbar albarka ga masu ƙaunar shariarka, * babu sanadin tuntuɓe gare su.

Na sa zuciya ga cetonka, * Yahweh, * na kuwa aikata dokokinka.

Raina ya kiyaye sharaɗunka, * ina ƙaunarsu matuƙa.

Ina kiyaye umurnanka da sharaɗunka, * domin dukan alamurana suna gabanka.

169-176 t

Bari kukana ya kai gare ka, * Yahweh, * bisa ga maganarka ka ba ni ganewa.

Bari adduata ta zo gare ka, * bisa ga alkawalinka ka cece ni.

Bari leɓunana su dinga yabonka, * domin kana koya mani kaidodinka.

Bari halshena ya maimaita kalmarka, * domin cikamakin dokokinka adalci ne.

Bari ka shirya hannunka don taimakona, * gama na zaɓi umurnanka.

Ina begen cetonka, * Yahweh, * shariarka kuma tana faranta mani rai.

Raina ya daɗe don ya yabe ka, * hukuntanka kuma su taimake ni.

Ko da na ratse kamar ɓatattar tunkiya, * ka neme ni, bawanka, * domin ban mance da dokokinka ba.

Zabura ta 120

Da aka kai mani hari * na yi kira ga Yahweh, * ya kuwa amsa mani.

    Yahweh, ka cece ni * daga leɓuna maƙaryata, * daga halshe mai hainci.

    Yadda zai saka maka! * zai ninka horonka, * ya halshen hainci!

        Zai zama kamar tsinanan kiban jarumi, * da garwashin wuta.

    Kaitona! Ko da na je baƙunci a Mashak, * ko na tafi sansanin Kedar,

    na zauna kurkusa * da maƙiyin salama.

Ni dai, ina maganar salama, * amma su, sai ta yaƙi.

Zabura ta 121

Na ɗaga idanuna ga Dutsen, * daga ina taimakona zai zo?

    Taimakona zai zo daga wurin Yahweh, * Mahaliccin sama da ƙasa.

        Ba zai sa ƙafarka a Tabon ba, * Matsarinka ba zai yi gyangyaɗi ba.

            I, baya gyangyaɗi ko barci, * Matsarin Israila.

            Yahweh ne matsarinka, * Yahweh ne inuwarka, * Maɗaukaki shi ne hannun damanka.

        Da rana, rana ba za ta yi maka lahani ba, * ko wata da daddare.

    Yahweh zai kare ka * daga kowace irin mugunta, * zai tsare ranka.

Yahweh zai kare fita da dawowarka * daga yanzu da har abada.

Zabura ta 122

Na yi murna da masu cewa da ni: * Bari mu je gidan Yahweh.

Ƙafafuna suna tsaye * a hayin ƙofofin Urushalima.

    Urushalima da aka gina tamkar birninsa, * wanda shi kaɗai ne ya kammala ginin.

    A can ne kabilu ke hawa, * kabilun Yahweh.

        Sharaɗi ne, ya Israila, * ka yi godiya ga sunan Yahweh,

        domin can ne suka zauna * a kursiyun sharia, * kursiyun gidan Dauda.

    Bari su yi addua don salamarki, ya Urushalima, * bari masoyanki su arzuta!

    Bari salama ta wanzu a kewayen ganuwoyinki, * wadata kuma a cikin fādodinki.

Saboda yanuwana da abokaina ,* ina cewa, Salama a gare ki.

Saboda gidan Yahweh Allahnmu, * ina neman alherinki.

Zabura ta 123

Ina zuba idanuna gare ka, * ya Mai mazauni a sama.

    I, kamar idanun bayi * da ke duban hannun iyayangijinsu,

        kamar idanun baiwa * da ke duban hannun uwargijiyarta,

            haka ne idanunmu * ke duban Yahweh Allahnmu, * har sai ya ji tausayinmu.

        Ka ji tausayinmu, Yahweh, * ka ji tausayinmu, ya Rabbi,

    mun gaji da wulakanci. * Mun daɗe maƙogwaronmu yana cika

da zagin yan iska, * da kuma renin masu izgilanci.

Zabura ta 124

Da ba Yahweh ne tare da mu ba, * bari Israila ya ce,

da ba Yahweh ne tare da mu ba, * saad da mutane suka tasam mana,

    da sun haɗiye mu da rai, * saad da hushinsu ya yi ƙuna a kan mu,

        da ruwaye sun sha kan mu * kamar ƙorama * ta shanye wuyanmu,

            da ruwaye masu toroƙo * sun gudado bisa wuyanmu.

            Yabo ga Yahweh, * da bai ba da mu * kamar ganima su ci ba.

        Wuyanmu ya kuɓuce kamar tsuntsu * daga tarkon mafarauci.

    Tarkon ya tsinke, * mu kuma mun tsira.

Taimakonmu yana cikin sunan Yahweh, * wanda ya halicci sama da ƙasa.

Zabura ta 125

Masu dogara ga Yahweh * kamar dutsen Sihiyona suke.

Mai kursiyin Urushalima * har abada ba zai jijigu ba.

    Kamar duwatsun da ke kewaye da ita, * haka ne Yahweh ke kewaye da jamaarsa * daga yanzu har abada.

        Sandan mugu ba zai tsaya * a kan ƙasar da aka raba wa masu gaskiya ba,

    in masu gaskiya ba su sa hannu * a cikin aikin cuta ba.

Nuna nagartarka, Yahweh, ga masu nagari, * da zuciyarsu ke daidai.

Amma masu shan kaye saboda baki biyunsu, * Yahweh ya kore su da masu aikata mugunta.

Salama ga Israila!


Zabura ta 126

Saad da Yahweh ya sake arzuta Sihiyona, * mun zama kamar yashin teku.

    Sannan bakinmu ya cika da murmushi, * halshenmu kuma da sowar murna.

        Sannan sai alummai suka ce, * Yahweh ya nuna girmansa * ta yi masu aiki.

            Yahweh ya nuna girmansa * ta yi mana aiki, * mun zama masu murna.

            Yahweh ya sake arzuta mu, * kamar ƙoramun Nagab.

        Waɗanda suka yi shuka da hawaye * suna yin girbi da sowa ta murna.

    Ko da yake ya tafi yana kuka, * yana ɗauke da ƙwaryar iri,

ya dawo gida da sowa ta murna, * yana zuwa da dammunansa.

Zabura ta 127

Idan ba Yahweh ne ya gina fadar ba, * aikin banza maginanta suke yi.

Idan ba Yahweh ne ya tsare birnin ba, * tsaron banza matsaranshi suke yi.

    A banza ne kuke saurin tashi, * ku da ke kwanciya a makare,

        kuna ta cin abincin gumaka. * Amma Amini yana ba da wadata ga ƙaunatattunsa.

        I, yaya kyauta ce daga wurin Yahweh, * albarkar mahaifar mace lada ne daga gare shi.

    Kamar kibau a hannun jarumi, * haka yayan da aka haifa a ƙuruciya suke.

Albarka ga mutumin * da ya cika kwarinsa da su.

Ba zai kunyata ba, * amma zai kori magabtansa tun daga bakin ƙofa.

Zabura ta 128

Albarka ga kowane mai tsoron Yahweh, * yana bin hanyarsa!

I, za ka ci aikin hannunka, * za ka yi farinciki ka arzuta.

Matarka za ta zama kamar kuringar inabi * mai yaya a gidanka.

Yayanka kamar rassan zaitun, * suna kewaye da teburinka.

    Ga yadda Amini yakan yi albarka * ga mai tsoron Yahweh.

Yahweh na Sihiyona ya yi maka albarka!

Ka ji daɗin wadatar Urushalima * dukan kwanakin ranka!

Ka ji daɗin jikokinka, * da kuma salama daga Maɗaukakin Israila.

Zabura ta 129

Sun tsananta mani sosai tun ƙuruciyata, * haka Israila ya ce.

Sun tsananta mani sosai tun ƙuruciyata, * amma ba su rinjaye ni ba.

Mahuɗa sun huɗe gadon bayana, * sun yi dogayen kunyai a kansa.

    Bari Yahweh Mai Gaskiya ya tsinke * karkiyar miyagu.

    Bari dukan masu ƙin Sihiyona * su kunyata, su koma da baya.

Bari su zama kamar ciyawar kan soro, * da ke bushewa a gaban mai tumɓukewa,

don kada mai girbi ya cika hannunsa, * ko mai ɗaura dami ya cika ƙirjinsa da ita,

kada kuma masu wucewa su ce, * Albarkar Yahweh a kan ku! * Mun yi maku albarka da sunan Yahweh!

Zabura ta 130

Daga Zurfafa nike yin kuka gare ka, Yahweh, * ya Ubangiji, ka ji muryata.

Bari kunnuwanka su ji * roƙon da nike yi don jinƙai.

    Da kana lissafa mugunta, Yahweh, * Ubangiji, wa zai iya jurewa?

        Amma wurinka akwai gafara, * domin a tsorace ka.

        Ina kiran Yahweh, * raina yana kira, * ina jiran maganarsa.

    Raina yana sauraren Ubangijina, * daga tsaron dare har safe, * da tsaron dare har safe.

Israila, ka dakaci Yahweh, * domin a wurin Yahweh akwai ƙauna, * a wurinsa da fansa mai yawa.

Shi kansa zai fanshi Israila * daga dukan kurakuransa gare shi.

Zabura ta 131

Yahweh, zuciyata ba mai alfarma ba ce, * idanuna kuma ba masu rena kowa ba ne.

    Ban shiga alamuran da suka zarce ni ba, * ban kuma shiga zantuttukan da suka fi ƙarfina ba.

        Amma na kwantad da raina,

    kamar jinjirin da ke kwance a gun uwarsa, * raina ma kamar jinjiri ne a gunsa.

Israila, ka dakaci Yahweh, * daga yanzu har abada.

Zabura ta 132

Dauda, ka tuna da Yahweh,* da dukan nasarorinsa.

    Dauda ya yi wa Yahweh rantsuwa, * ya yi waadi ga Mai Girma na Yakubu da ya ce:

        Ba zan shiga labulen wurin kwanciyata ba, * ba ma zan hau gadon da aka shimfiɗa mani ba.

        Ba zan bar idanuna su yi barci ba, * ko maƙiftaina su yi gyangyaɗi,

    sai na samar wa Yahweh wuri, * mazauni don Mai Girma na Yakubu.

    Duba, mun ji wannan labarin a Efrata, * an gaya mana ma a filin Jayar.

        Bari mu tafi mazauninsa, * mu yi sujada a matashin sawunsa.

        Tashi, Yahweh, ka je wurin hutuwarka, * kai da akwatin da ke mafakarka.

    Bari a tufatar da firistocinka da gaskiya, * masu bautarka kuma su yi sowa ta murna,

            su ce: Saboda bawanka Dauda, * kada ka ya da shafaffen sarkinka.

    Dauda, Yahweh ya yi rantsuwa, * hakika ba zai canza ba:

        cewa, Ɗan jikinka * zan sa a kan kursiyinka,

        in yayanka sun kiyaye yarjejeniyata, * da sharaɗun da zan koya masu.

    Yayansu ma za su zauna * a kan kursiyinka har abada.

    Gama Yahweh ya zaɓi Sihiyona, * yana marmarinta don ta zama mazauninsa.

        Ga wurin hutuwata har abada, * a nan zan zauna don ina marmarinta.

        Zan yi wa alhazanta albarka mai yawa, * zan ƙosad da gajiyayyunta da abinci.

    Zan tufatad da firistocinta da ceto, * masu bautata kuma za su riƙa yin sowa ta murna.

Dauda, can zan sa ƙahonka ya riƙa haske, * zan kuma kunna fitilarka, ya shafaffena.

Magabtansa zan tufanta su da kunya, * amma kambinsa zai yi ƙyalli a kansa.

Zabura ta 133

Abu ne mai kyau da faranta rai, * in yanuwa suna zaman salama!

    Kamar kyakkyawan mai ne da aka zuba a ka, * ya yi naso har kan gemu,

        gemun nan na Haruna, * yana naso har wuyan rigarsa,

    kamar ma raɓar Harmon ce, * in ta sauko a kan duwatsun Sihiyona.

A can ne Yahweh yake ba da albarka, * ta rai na har abada.

Zabura ta 134

Ku zo, ku yabi Yahweh, * ku dukan ayyukan Yahweh!

    Ku da ke tsaye a gidan Yahweh * har tsakar dare,

    ku ɗaga hannuwanku ga tsattsarkan wuri, * ku yabi Yahweh.

Yahweh na Sihiyona ya yi maku albarka, * wanda ya yi sama da ƙasa.

Zabura ta 135

Halelu-Yah!

Ku zo, ku yabi sunan Yahweh, * ku yabi dukan ayyukan Yahweh,

    ku da ke tsaye a gidan Yahweh * a farfajiyar gidan Allahnmu.

    Ku yabi Yahweh, gama shi nagari ne, * ku yi waƙar sunansa mai daɗi.

Don Yahweh ya zaɓi Yakubu ya zama nasa, * Israila kuma tamkar mallakarsa.

    I, na yarda Yahweh mai girma ne, * Ubangijinmu kuma ya fi dukan alloli girma.

        Duka abin da Yahweh ya ga dama * shi zai yi,

            a sama da ƙasa, * a tekuna da dukan zurfafa.

        Yana ta da gajimarai * daga bangon duniya,

    yana yin walƙiya don ruwan sama, * yana kawo iska daga taskokinsa.

        Shi ne ya mazge yayan fari a Masar, * na mutun da na dabba.

        Ya aiki alamomi da alajibai, * a tskar Masar, * kan Firaauna da dukan bayinsa.

            Shi ne ya mazge manyan alummai, * ya karkashe manyan sarakuna,

            har da Sihon, sarkin Amoriyawa, * da Og, sarkin Bashan, * i, da dukan sarakunan Kanana.

            Ya ba da ƙasarsu a gada, * gado ga jamaarsa Israila.

        Yahweh, sunanka madauwami ne, * Yahweh, martabarka tana kan dukan tsararraki.

        I, Yahweh yana kare jamaarsa, * yana jin tausayin bayinsa.

    Amma gumakan alummai azurfa da zinari ne, * aikin hannuwan mutun.

        Suna da baki, ba sa magana, * suna da idanu, ba sa gani.

        Suna da kunnuwa, ba sa jin murya, * ba su ma lumfashi.

    Masu yinsu za su zama kamar su, * da duk wanda ya dogara gare su.

Ya Israilawa, ku yabi Yahweh, * ya gidan Haruna, ku yabi Yahweh!

    Ya gidan Lawi, ku yabi Yahweh! * Masu tsoron Yahweh, ku yabi Yahweh!

Yabo ga Yahweh na Sihiyona, * Mai Zama a Urushalima!

Halelu-Yah!


Zabura ta 136

Ku gode wa Yahweh don shi nagari ne, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

Ku gode wa Allah mai alloli, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

Ku gode wa Ubangijin iyayengiji, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

    Ga Mai yin manyan muujizai shi kaɗai, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

    Ga Mai yin sammai da hikima, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

        Ga Mai shimfiɗa ƙasa a birbishin ruwaye, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

        Ga Mai yin manyan haskoki, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

            Rana mai mulkin rana, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

            Wata da taurari masu mulkin dare, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya mazge yayan farin Masarawa, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Ya fito da Israila daga cikinsu, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Da ƙaƙƙarfan hannu da miƙaƙƙen dantse, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                      Wanda ya raba Bahar Kyamare biyu, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                           Ya hayar da Israila ta cikinta, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                      Amma ya birkice Firaauna da mayaƙansa, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya sa jamaarsa haye hamada, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya mazge manyan sarakuna, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

                 Ya ma kashe shaharrarrun sarakuna, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

            Har da Sihon, sarkin Amoriyawa, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

            Da Og, sarkin Bashan, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

        Ya ba da ƙasarsu abin gado, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

        Gado ga Israila bawansa, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

    Wanda ya tuna mu cikin ƙasƙancinmu, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

    Ya fyauce mu daga abokan gabanmu, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

Wanda yake ba kowace dabba abinci, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

Ku yabi Allah na sama, * ƙaunarsa madauwamiya ce.

Zabura ta 137

A bakin kogunan Babila, * can muka zauna,

muka yi kuka mai tsanani, * saad da muka tuna da ke, Sihiyona.

    A gefen itatuwan da ke can, * muka rataye garayunmu.

    Domin masu kama mu sun ce * mu yi masu waƙa.

    Masu zaginmu sun biɗi murna, * Ku raira mana daga cikin waƙoƙin Sihiyona.

        In na mance da ke, * ya Urushalima, * hannuna na dama ya shanye!

        Bari halshena ya liƙe wa bakina * in ban tuna da ke ba,

        in ban saɓa ki, ya Urushalima, * a kafaɗata cikin shagali ba!

    Ku tuna da Yahweh, ku Edomawa, * game da ranar Urushalima,

    saad da kuka ce, Tuɓe, tuɓe, * har zuwa harsashinta!

Ya Ya Babila, mai hallakawa, * albarka ga wanda ya saka maki * da mugun da kika yi mana!

Albarka ga wanda ya kwashi jariranki, * ya fyaɗa su a kan dutse!

Zabura ta 138

Ina yi maka godiya da dukan zuciyata, * ina raira maka waƙa a gaban malaiku.

Ina yin sujada zuwa ga tsattsarkan Haikalinka, * ina yi wa sunanka godiya.

    Ta ƙaunarka da amincinka * lalle ka ɗaukaka * sunanka da alkawalinka a gaban kowa.

    Da na kira, kā ba ni nasara, * kā taimake ni da ƙarfin hali don kai hari.

        Dukan sarakunan duniya za su yabe ka, Yahweh, * in suka ji kalmomin bakinka.

            Za su kuwa yi waƙar sarautar Yahweh, * cewa, Ɗaukakar Yahweh da girma take!

        Ko da yake Yahweh Maɗaukaki ne, * yakan dubi mai ƙasƙanci, * ko da yake Mai Sama, yana ji daga nesa.

    Da nike tafiya a tsakar abokan gabata, * ka raya ni a cikin haushin magabtana.

    Ka miƙo hannunka na hagu, * ka ba ni nasara da hannun damanka. * Yahweh ya rama mani muddin rayuwata.

Yahweh, ƙaunarka madauwamiya ce, * kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

Zabura ta 139

Yahweh, ka bincike ni, * ka gane ni da kanka!

    Kana sanin zamana da tashina, * ka gane tunanina daga nesa.

        Kana safiyon fitowata da dawowata, * ka lura da dukan tafiyata.

            Ba kalmar da ke fita daga bakina, * sai ka san ta duka.

        Kā yi mani shinge gaba da baya, * kā rungume ni da tafin hannuwanka.

    Saninka ya fi ƙarfina, * ya sha kaina, bana iya haddace shi.

        Ina zan je guje wa ruhunka? * Ina zan gudu daga fuskarka?

            In na hau sammai, kana can, * in na kwanta a Shawol, kana can!

            In na ta da fukafukaina daga gabas * don in sauka a ƙurin yamma,

        can ma za ka ɗora hannun hagunka a kaina, * kana kama ni da hannun damanka.

            Sannan na sansance ko cikin duhu yana kallona, * da dare kuma haske yana kewaye ni.

            Duhun bai duhunta gare ka ba, * Daren yana haskaka maka kamar rana, * daren ma sai ka ce haske.

                 I, ka siffanta ƙodata, * kā kare ni tun ina cikin mahaifar uwata.

            Ina yabonka, ya Maɗaukaki, * domin kai mai bantsoro ne.

            Na rusuna don yi maka sujada, * ya mai banrazana ta wurin ayyukanka.

        Kā san ruhuna tuntuni, * ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

            tun da aka zaɓi yumɓun a Asirtaccen Wuri, * aka mulmula ni a zurfafan Ƙalƙashin Ƙasa.

            Idanunka sun ga matakan rayuwata, * don an rubuta dukansu a littafinka.

        An siffanta kwanakina * tun kafin waninsu ya gan ni.

    Amma a gare ni tunaninka suna da nauyi, * ya Allah, tulawarsu tana ta ƙarfi!

    Da zan iya ƙirga su, da sun fi yashi yawa! * Bari in tashi in zama tare da kai har abada!

        Ya Allah, ina ma a ce za ka kashe mugun, * masu bautar gumaka, ku yi nesa da ni!

        Suna kallon kowane gunki, * suna zura ido ga abubuwan banza da aka baje kolinsu.

    I, Yahweh, ina ƙin masu ƙinka, * ina ƙyamar masu yi maka tawaye.

    Ina ƙinsu da matuƙar ƙiyayya, * sun zama abokan gabata.

Ka bincike ni, ya Allah, ka san zuciyata, * ka gwada ni, ka ma gane damuwata.

Ka ga ko wani gunki ya taɓa mallakata, * kāna ka kai ni madauwamin mulkinka.

Zabura ta 140

Yahweh, ka cece ni daga mugun mutun, * ka tsare ni daga mai ɗacin rai,

    domin suna shirya ƙeta a zukatansu, * wuni zubut suna shirin yaƙi.

    Suna wasa da halshensu kamar maciji, * ko kububuwa ba ta kai ɗafin leɓensu ba.

        Yahweh, ka kiyaye ni daga hannuwan mugu, * ka kare ni daga mafaɗaci,

        domin sun yi shirin tadiye ƙafafuna, * masu izgilanci sun ɗana mani tarko.

        Yan taadda sun ɗana tarko, * a gefen hanya suka baza mani raga.

            Ina cewa, Yahweh, kai ne Allahna, * ka kasa kunne, Yahweh, ga roƙona don jinƙai.

            Yahweh Ubangijina, mafakar cetona, * ka zama garkuwata a fagen fama.

        Yahweh, kada ka biya bukakan miyagu, * ya Maɗaukaki, kada ka inganta maƙarƙashiyarsu.

        Abokan gaba da suka kewaye ni, * bari su nutse a cikin dafin leɓunansu.

        Bari ya zuba masu garwashin wuta, * ya ingiza su cikin Wutar, * kada su iya fita daga kududdufinta!

    Mai kakkausan harshe, * kada ya sami masauki a ƙasa.

    Azzalumi ma, * bari Mugun nan ya farauce shi zuwa Bayan Duniya.

    Na san Yahweh zai kare zaluntacce * ya bi hakkin matalauta.

Lalle, adalai za su yabi sunanka, * masu gaskiya kuma za su dauwama a gaban fuskarka.

Zabura ta 141

Ina kiranka, Yahweh, * amsa mani mana.

    Ina kiranka, * ka saurare ni!

        Bari adduata ta kasance * kamar turaren ƙanshi a gabanka,

        ɗagaggun hannuwana kuma * kamar hadayar maraice.

    Yahweh, ka danne bakina, * ya Maɗaukaki, ka ƙulle leɓunana.

Ka hana zuciyata kitsa mugunta, * da shaawar ayyukan miyagu.

        Idan na taya miyagu * cin abincin garaɓasarsu,

            bari Mai Gaskiya ya mazge ni, * Mai Alherin nan ya hore ni.

        Haka ma idan mansu mai daraja ya haskaka kaina, * domin ina ci gaba da yin addua a kan miyagun ayyukansu.

Bari alkalansu su fāɗa a hannuwan Dutsen, * su kuwa ɗanɗana hukuncinsa!

    Kamar wanda aka sassare aka yanyana a Lahira, * haka ƙasasuwana suka barbaje a bakin Shawol.

        Amma gare ka, * Yahweh Ubangiji, * nike zuba ido.

        Na nemi tsira a gunka, * ya Allah, * ka kare raina.

    Ka kiyaye ni daga tarkon da suka ɗana mani * da kiban azzaluman nan.

Bari miyagun nan duka * su fāɗa tarkunan Yahweh, * ni kuwa in tsira.

Zabura ta 142

Ina kuka ga Yahweh da ƙarfi, * ina kuka ga Yahweh don neman tausayi!

    A gare shi nike bulbula ƙarrarakina, * ina gaya mashi wahaluna:

        Ruhuna ya gaza, * amma kai ne ka san inda zani.

    Sun ɗana mani tarko * a kan hanyar da nike bi.

        Ka dubi kewaye da ni, * ba wanda ya san ni.

            Ba ni da damar tsira, * babu mai kula da ni.

        Na yi ruri gare ka, Yahweh, * na ce kai ne mafakata,* da rabona a ƙasar madauwamin rai.

    Ya Allah, ka saurari kukana, * ya Mai Girma, na gaza!

        Ka cece ni daga mafarautana, * domin sun fi ni ƙarfi.

    Ka tsamo ni daga kurkuku, * don in yabi sunanka.

Bari masu gaskiya su kewaye ni, * domin ka kyauta mani, ya Maɗaukaki.

Zabura ta 143

Ka ji adduata, Yahweh, * ya Allah, ka ji roƙona don jinƙai.

Ka amsa mani da amincinka, * ka amsa mani da adalcinka.

    Amma kada ka kai bawanka a gaban sharia, * domin babu wani mai rai da zai barata a gabanka.

        Domin magabci ya faki raina, * ya goga rayuwata zuwa Ƙalƙashin Ƙasa.

        Ya sa ni zama cikin lungun duhu, * kamar mutanen Dauwamammen Gida.

        Ruhuna ya narke mani, * zuciyata ta karai.

    Na tuna zamanin dā, * na lissafci dukan ayyukanka, * kan ayyukan hannuwanka na yi nazari.

        Na miƙa hannuwana zuwa wurinka, * daga Ƙalƙashin Ƙasa maƙogwarona na ƙishinruwanka.

            Ka yi hanzarin amsa mani, Yahweh, * ruhuna ya gaza, ya Allah!

        In ka kau da fuskarka daga guna, * zan yi kama da masu gangarawa Ramin.

    Bari in yi kaciɓis da alherinka da asuba, * domin ina dogara gare ka.

    Ka nuna mani hanyar da zan bi, * domin na mai da hankalina gunka.

        Yahweh, ka cece ni daga magabtana,* ya Allahna, a gaskiya ina nutsewa.

    Ka koya mani yin nufinka, * domin kai ne Allahna.

    Da ruhaniyarka ta ƙwarai * ka bi da ni * zuwa Ƙasa madaidaiciya.

Yahweh, saboda sunanka ka ba ni rai, * ta gaskiyarka ka fanso raina daga magabtana.

Ta ƙaunarka ka shafe abokan gabata, * ka hallaka dukan masu tsorata ni, * domin ni bawanka ne.

Zabura ta 144

        Yabo ga Allah, Dutsena, * wanda ya koya wa hannuwana dabarun yaƙi, * damatsana logogin faɗa.

Garuna da mafakata, * katangata da matserata,

Shugabana, na dogara gare shi, * wanda ya rusunad da mutane a ƙafafuna.

    Yahweh, menene mutun, har da za ka damu da shi, * ɗan adan, har da za ka kula da shi?

    Mutun kamar tururi ne, * kwanakinsa kamar inuwa ce mai wucewa.

Yahweh, ka naɗe sammanka, ka sakko, * ta taɓa duwatsu, ka sa su yi hayaƙi.

Ka gilma walƙiyoyinka, ka watsa su, * ka ƙera kibanka, ka harba su.

    Ka miƙo hannuwanka daga sama, * ka tsamo ni, ka cece ni

    daga Zuzzurfan Ruwa, * daga hannun baƙi,

    waɗanda bakinsu ke wulla ƙarya, * hanuunsu na dama kuma yana yin shaidar zur.

        Ya Allah, bari in raira maka sabuwar waƙa, * ina kaɗa maka garaya mai tsarkiyoyi goma,

        kai da ka ba sarkinka nasara, * ka fanso bawanka Dauda.

    Ka fanso ni daga takobin Mugun nan, * ka ƙwato ni daga hannun baƙi.

    waɗanda bakinsu ke wulla ƙarya, * hannunsu na dama kuma yana yin shaidar zur.

Bari ya yi wa yayanmu maza albarka kamar icen inabi, * da aka hora tun ƙuruciyarsu

yaya matanmu kuma kamar ginshiƙai, * da aka gina don adon fāda.

    Bari rumbuanmu su cika, * har su yi banzabo.

    Bari tumakinmu su haifi dubban yaya, * dubbai bisa dubbai a makiyayinmu, * shanunmu su yi ɓulɓul.

Kada mu ga wani hari ko gudun hijira, * ko mu ji hayaniya a dandalinmu.

Albarka ga jamaar da ta zama haka, * albarka ga jamaa wadda Yahweh ne Allahnsu.

Zaburta ta 145

Zan ɗaukaka ka, ya Allah Sarkina, * zan albarkaci sunanka, ya Maɗaukaki!

    Zan albarkace ka kowace rana, * in yi waƙa da sunanka har abada abadin.

    Yahweh Akbar, * Mai Girma ne da ya dace da yabo, * domin girmansa ba shi da iyaka.

    Kowace tsara za ta bayyana ayyukanka ga tsara ta gaba, * tana ba da labarin bajintarka.

        Ya Mai Martaba, za su yi magana a kan ɗaukakarka, * ni kuwa zan wallafa waƙoƙin alajibanka.

        Ya Mai Ƙarfi, za su furta ayyukanka masu bantsoro, * ni kuwa zan lissafci muujjizanka.

        Za su furta jumlar alheranka, ya Rabbi, * suna raira yabon adalcinka.

            Yahweh Arahamani Arahimi ne, * mai jinkirin hushi, mai yalwar alheri.

            Yahweh mai alherin ne ga kowa, * rahamominsa suna kan dukan ayyukansa.

                 Yahweh, dukan ayyukanka za su yabe ka,* masu bautarka kuma za su yi maka godiya.

                 Za su yi shela ta ɗaukakar mulkinka, * suna maganar ikonka.

                 Suna sanar wa yan adan jarumtakarka, * da ɗaukaka ta girman mulkinka.

                 Mulkinka madauwammin mulki ne, * sarautarka ta dukan zamanai ce.

            Yahweh amintacce ne a cikin maganarsa, * mai alheri ne kuma a cikin dukan ayyukansa.

            Yahweh yana tallafar dukan masu fāɗuwa, * yana ɗaga dukan waɗanda suka sunkuya.

        Kowa da kowa ya zura maka ido, * domin kana ba su abincinsu a kan kari.

        Kana buɗe hannunka, * ka ƙosad da kowane mai rai da alherinka.

        Yahweh mai adalci ne a dukan hanyoyinsa, * mai ƙauna ne kuma a dukan ayyukansa.

    Yahweh na kusa da dukan masu nemansa, * masu nemansa da gaskiya.

    Yana biyan bukatun masu tsoronsa, * ta jin kukansu yana cetonsu.

    Yahweh na kiyaye dukan masu ƙaunarsa, * amma zai hallaka dukan miyagu.

Bakina zai furta yabon Yahweh, * duk nama da jini zai yabi sunansa mai tsarki, * har abada abadin.

Zabura ta 146

Halelu-Yah!

Raina, ka yabi Yahweh! * Bari in yabi Yahweh muddin ina raye, * in yi wa Allahna waƙa lokacin da nike rayuwa.

    Kada ku dogara ga mahukunta, * ga ɗan adan da baya iya yin ceto.

    Da lumfashinsa ya fita, sai ya koma turɓayarsa, * a ranan nan shirye-shiryensa sun ƙare.

            Albarka ga wanda Allahn Yakubu shi ne taimakonsa, * da ke sa zuciya ga Maɗaukakin Yahweh Allahnsa,

                 wanda ya yi sammai da ƙassai, * teku da duk abin da ke cikinsu,

                 wanda ke yin aminci ga zaluntattu, * da kāre hakkin cutattu, * yana ba da abinci ga mayunwata.

            Yahweh yana yantad da ɗaurarru, * Yahweh yana buɗe idanun makafi, * Yahweh yana miƙad da karkatattu.

    Yahweh yana ƙaunar masu adalci, * Yahweh yana kare baƙi.

    Yana ƙarfafa marayu da gwauraye, * amma yana ƙarya ikon miyagu.

Yahweh zai yi mulki har abada, * Allahnki, ya Sihiyona, sarkin dukan zamanu ne.

Halelu-Yah!



Zabura ta 147:1-11

Halelu-Yah!

Waƙar yabon Allahnmu tana da kyau, * muna jin daɗin yabon Maɗaukaki.

Yahweh ne mai sake ginin Birnin Ƙudus, * yana tattara korarrun Israila.

    Yakan warkad da masu karayayyar zuciya, * yana ɗaure masu raunukansu.

        Yakan ba kowane tauraro lamba, * yana raɗa wa kowanensu suna.

            Ubangijinmu mai girma ne da mafificin iko, * babu mai iya kwatanta gwanintarsa.

                 Yahweh yakan tallafa wa masu tawaliu, * yana ƙasƙanta miyagu har Ƙalƙashin Ƙasa.

            Ku yi waƙar godiya ga Yahweh, * ku ƙada garaya ga Allahnmu.

        Yana rufe sama da gizagizai, * yana yin ruwan sama don ƙasa, * yana sa ciyawa ta tsira a kan duwatsu.

    Yana ba shanu abincinsu, * da abin da hankaki za su kwasa.

Baya jin daɗin ƙarfin dawaki, * kaurin cinyar mutun baya burge shi.

Amma Yahweh na jin daɗin masu tsoronsa, * da masu dogara ga ƙarfinsa.

Zabura ta 147:12-20

Ka yabi Yahweh, ya Birnin Ƙudus, * ki yabi Allahnki, ya Sihiyona!

Domin ya ƙarfafa dogaran ƙofofinki, * ya sa wa yayanki albarka a cikinki.

Yana wanzad da salama har iyakokinki, * yana wadata ki da alkama mafi kyau.

    Yana aiko da kalmarsa duniya, * aradunsa tana tafiya da gaggawa zuwa duwatsu.

    Yana barbaɗa dusar ƙanƙara kamar ulu, * yana watsa jaura kamar toka.

    Yana zubo ƙanƙararsa kamar gari. * Wa zai jure wa tsananin sanyinsa?

    Yana aika maganarsa ta narkad da su, * yana sa iskarsa ta hura sai ruwa ya yi gudu.

Yana bayyana saƙonsa ga Yakubu, * kaidodinsa da hukuntansa ga Israila.

Bai yi naam haka da sauran alummai ba, * bai taɓa koya masu hukuntansa ba.

Halelu-Yah!


Zabura ta 148

Halelu-Yah!

Ku yabi Yahweh daga sammai, * ku yabe shi daga can bisa!

    Ka yabe shi, dukan malaikunsa, * ku yabe shi, dukan mayaƙansa!

        Ku yabe shi, rana da wata, * ku yabe shi, dukan taurarin asubar fari!

            Ku yabe shi, sammai mafi tsayi, * da ruwayen da ke bisa sammai!

        Bari su yabi sunan Yahweh, * shi ne ya umurta, aka halicce su.

    Ya kafa su tuntuni har abada, * ya ba da kaidar da ba za ta shuɗe ba.

Ku yabi Yahweh daga Ƙalƙashin Ƙasa, * ku dodannin ruwa da dukan zurfafa!

    Walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da hayaƙi, * iskar hadarin da ke bin maganarsa,

        duwatsu da dukan tuddai, * itatuwa masu yaya da na alul duka,

            naman daji da dukan bisashe, * masu rarrafe da tsuntsaye masu fukafukai,

        sarakunan duniya da dukan alummai, * shugabanni da dukan kabilan duniya,

    samari da yan mata, * tsaffi da yara,

bari su yabi sunan Yahweh, * domin sunansa kaɗai ne mai ɗaukaka.

Ko da yake ɗaukakarsa tana gaban sama da ƙasa, * ya ɗaga ƙahon jamaarsa.

Bari dukan masu bautarsa su yabe shi, * musamman yayan Israila, yan gaban goshinsa.



Zabura ta 149

Halelu-Yah!

Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh, * ku yabe shi a taron masu bautarsa.

    Bari Israila ya yi murna da Mahallicinsa, * yayan Sihiyona su yi farinciki da Sarkinsu.

Su yabi sunansa da rawa, * su yabe shi da ganga da garaya.

    Domin Yahweh yana jin daɗin jamaarsa, * yana naɗa rawanin nasara ga gajiyayyu.

                 Bari masu bauta masa su yi murna da Maɗaukaki, * su yi farinciki da shi lokacin kwanciyarsu.

    Bari su ɗaukaka Allah da maƙogwaronsu, * suna riƙe takubba masu kaifi a hannwansu,

don su zartad da ramuwa a kan alummai, * da sakayya a kan kabilu,

    don su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, * shugabanninsu da mari,

don su aikata rubutaccen hukunci. * Wannan ce shaidar yabo ga dukan masu bauta masa!

Halelu-Yah!



Zabura ta 150

Halelu-Yah!

Ku yabi Allah a tsattsarkan wurinsa, * ku yabe shi a mafakarsa ta sama!

    Ku yabe shi don ikonsa, * ku yabe shi yadda ya dace da girmansa!

        Ku yabe shi da busar kakaki, * ku yabe shi da garaya da molo!

        Ku yabe shi da tambari game da rawa, * ku yabe shi da tsarkiya da sarewa!

    Ku yabe shi da kuge mai ƙara, * ku yabe shi da kuge mai amo!

Bari duk mai lumfashi * ya yabi Yahweh!

Halelu-Yah!